Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Oktoba pp. 18-23
  • Yadda Za Ka Inganta Adduꞌarka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za Ka Inganta Adduꞌarka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KADA KA BAR KOME YA HANA KA YIN ADDUꞌA
  • YADDA ZA MU ƘARA INGANTA YADDA MUKE ADDUꞌA
  • KA YI TUNANI A KAN ADDUꞌOꞌIN DA KE LITTAFI MAI TSARKI
  • KA CI-GABA DA KUSANTAR JEHOBAH TA WURIN YIN ADDUꞌA
  • Mu Riƙa Yin Adduꞌa a Madadin Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ka Kusaci Allah Cikin Addu’a
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Ka Kyautata Addu’o’inka Ta Wurin Nazarin Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ka Rika Yin Addu’a don Ka Kusaci Allah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Oktoba pp. 18-23

TALIFIN NAZARI NA 42

WAƘA TA 44 Adduꞌar Wanda Ke Cikin Wahala

Yadda Za Ka Inganta Adduꞌarka

“ Na yi kira da dukan zuciyata, amsa mini, ya Yahweh!”—ZAB. 119:145.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abin da za mu iya koya daga adduꞌoꞌin da bayin Jehobah suka yi da ke Littafi Mai Tsarki.

1-2. (a) Mene ne zai iya hana mu gaya wa Jehobah dukan abubuwan da ke zuciyarmu? (b) Ta yaya muka san cewa Jehobah yana sauraron adduꞌoꞌinmu da kyau?

SHIN, a wasu lokuta idan kana adduꞌa kana maimaita abu ɗaya, kuma ba ka gaya wa Jehobah ainihin yadda kake ji? Hakan abu ne da zai iya faruwa da kowannenmu. Da yake muna da ayyuka da yawa, mai yiwuwa za mu riƙa yin adduꞌa cikin hanzari maimakon mu ɗau lokaci muna yin sa. Ban da haka ma, idan muna ganin ba mu cancanci mu yi adduꞌa ga Jehobah ba, yin adduꞌa zai iya yi mana wuya.

2 Littafi Mai Tsarki ya koya mana cewa, ba kalmomi masu kayatarwa da muka yi amfani da su a adduꞌoꞌinmu ne suka fi muhimmanci ga Jehobah ba. Abin da yake so shi ne, mu yi adduꞌa da dukan zuciyarmu. Yana jin “kukan marasa ƙarfi.” (Zab. 10:17) Yana sauraron mu da kyau domin ya damu da mu.—Zab. 139:​1-3.

3. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Me ya sa bai kamata mu ji tsoron gaya wa Jehobah ainihin yadda muke ji ba? Ta yaya za mu inganta yadda muke yin adduꞌa? Ta yaya yin tunani a kan adduꞌoꞌin da bayin Jehobah suka yi da ke Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu inganta yadda muke adduꞌa? Kuma me za mu iya yi, idan muna cikin damuwa sosai har ba mu san abin da za mu gaya wa Jehobah ba? Bari mu ga amsoshin tambayoyin nan.

KADA KA BAR KOME YA HANA KA YIN ADDUꞌA

4. Me zai taimaka mana mu gaya wa Jehobah dukan abin da yake zuciyarmu? (Zabura 119:145)

4 Idan muka fahimci cewa Jehobah abokinmu ne kuma yana son mu yi nasara, hakan zai sa mu gaya masa duk abin da ke daminmu. Marubucin Zabura ta 119 ya fahimci hakan. Ya yi fama da matsaloli a rayuwarsa. Alal misali, wasu mutane sun yi ƙarya a kansa. (Zab. 119:​23, 69, 78) Kuma a wasu lokuta ya yi sanyin gwiwa don kurakuran da ya yi. (Zab. 119:5) Duk da haka, bai ji tsoron gaya wa Jehobah ainihin yadda yake ji ba.—Karanta Zabura 119:145.

5. Me ya sa zai dace kada mu bar kome ya hana mu yin adduꞌa? Ka ba da misali.

5 Jehobah yana son kowa ya riƙa yin adduꞌa har da waɗanda suka yi zunubi mai tsanani. (Isha. 55:​6, 7) Saboda haka, kada mu bar kome ya hana mu yin adduꞌa ga Jehobah. Alal misali, matuƙin jirgin sama ya san cewa zai iya neman taimako daga wurin maꞌaikatan jirgin saman da suke tashar jirgin. Shin, idan ya yi wani kuskure ko kuma ya ɓata hanya, zai ji kunyar kiran su don su taimaka masa? Aꞌa! Haka ma, idan a wasu lokuta ba mu san abin da za mu yi ba, ko kuma mun yi zunubi, zai dace mu nemi taimakon Jehobah da tabbaci cewa zai taimaka mana.—Zab. 119:​25, 176.

YADDA ZA MU ƘARA INGANTA YADDA MUKE ADDUꞌA

6-7. Ta yaya yin tunani game da halayen Jehobah zai taimaka mana mu ƙara inganta yadda muke adduꞌa? Ka ba da misali. (Ka kuma duba ƙarin bayani.)

6 Idan muna adduꞌa kuma muka gaya wa Jehobah ainihin yadda muke ji a zuciyarmu, hakan zai sa mu kusace shi. To, me zai taimaka mana mu riƙa yin adduꞌa haka?

7 Ka yi tunani game da halayen Jehobah.a Idan muna tunani a kan halayen Jehobah, hakan zai sa ya yi mana sauƙi mu gaya masa ainihin yadda muke ji a zuciyarmu. (Zab. 145:​8, 9, 18) Ka yi laꞌakari da labarin Kristine, wadda mahaifinta azzalumi ne. Ta ce: “Yin adduꞌa ga Jehobah, da ɗaukan sa a matsayin Uba mai ƙauna ya yi mini wuya. Ina ganin kamar kurakuraina za su sa ya yi watsi da ni.” Me ya taimaka mata? Ta ce: “Na yi tunani sosai a kan yadda Jehobah yake nuna ƙauna marar canjawa, hakan ya tabbatar mini cewa yana ƙauna ta. Na san cewa ba zai taɓa bari na ba. Ko da na yi kuskure, zai ci-gaba da ƙauna ta kuma zai taimaka mini. Hakan ya sa ya yi mini sauƙi in riƙa gaya masa abubuwan da suke sa ni farin ciki, da kuma waɗanda suke sa ni baƙin ciki.”

8-9. Ta yaya za mu amfana idan muka yi tunani a kan abin da muke so mu yi adduꞌa a kai? Ka ba da misali.

8 Ka yi tunani a kan abin da kake so ka yi adduꞌa a kai. Kafin ka yi adduꞌa, zai dace ka yi wa kanka wasu tambayoyi. Alal misali: ‘Waɗanne matsaloli ne nake fuskanta a yanzu haka? Akwai wanda ya kamata in gafarta masa? Akwai abin da ya faru a rayuwata kwanan nan da nake bukatar Jehobah ya taimaka min?’ (2 Sar. 19:​15-19) Ƙari ga haka, ka tuna da abin da Yesu ya koya mana game da adduꞌa. Kuma ka yi tunani a kan abin da za ka roƙi Jehobah game da Sunansa, da Mulkinsa, da kuma Nufinsa.—Mat. 6:​9, 10.

9 Saꞌad da wata ꞌyarꞌuwa mai suna Aliska ta ji cewa maigidanta yana da kansar ƙwaƙwalwa, yin adduꞌa ya yi mata wuya. Ta ce: “Na damu sosai, har ma idan ina adduꞌa ba na sanin abin da zan faɗa.” Me ya taimaka mata? Ta daɗa da cewa: “Kafin in yi adduꞌa, nakan ɗan ɗau lokaci in yi tunani a kan abin da nake son in faɗa. Hakan ya taimaka mini in riƙa yin adduꞌa a kan abubuwa da dama, ba game da ni da maigidana kawai ba. Yin hakan yana kwantar mini da hankali, kuma yana taimaka mini in tattara hankalina wuri ɗaya kafin in yi adduꞌa.”

10. Me ya sa zai dace mu riƙa yin adduꞌa na dogon lokaci? (Ka kuma duba hotunan.)

10 Kada ka riƙa yin adduꞌa da gaggawa. Gaskiyar ita ce, ko da gajeriyar adduꞌa ce muke yi, za mu iya kusantar Jehobah. Amma idan muka ɗau dogon lokaci muna adduꞌa, za mu fi bayyana masa ainihin yadda muke ji.b Maigidan ꞌyarꞌuwa Aliska da aka ambata ɗazu, mai suna Elijah ya ce: “Ina adduꞌa ga Jehobah kowace rana, amma ina ji kamar na fi kusantar Jehobah idan na ɗau dogon lokaci ina adduꞌa. Jehobah, Allah ne mai haƙuri. Kuma na san zai jira in kammala adduꞌata ko da za ɗau dogon lokaci. Don haka, ba na hanzari saꞌad da nake adduꞌa.” Ga abin da za ka iya yi: Ka nemi lokaci da kuma wuri da zai ba ka dama ka yi adduꞌa na dogon lokaci ba tare da wani abu ya ɗauke hankalinka ba. Sai ka yi adduꞌar da babban murya, kuma ka riƙa yin hakan a kai a kai.

Hotuna: Na 1. Wani ɗanꞌuwa yana tunani a kan abin da ya karanta daga Littafi Mai Tsarki da asuba. Littafin na buɗe a kan tebur, ga kuma shayi a gefe. Na 2. Bayan gari ya waye, yana zaune a wurin har ila kuma ya ɗau lokaci yana adduꞌa.

Ka nemi lokaci da kuma wurin da zai ba ka dama ka yi adduꞌa ga Jehobah ba tare da wani abu ya ɗauke hankalinka ba (Ka duba sakin layi na 10)


KA YI TUNANI A KAN ADDUꞌOꞌIN DA KE LITTAFI MAI TSARKI

11. Ta yaya za mu amfana idan muka bincika adduꞌoꞌin da ke Littafi Mai Tsarki? (Ka kuma duba akwatin nan “Kana Ji Kamar Yadda Suka Ji?”)

11 Za mu amfana sosai idan muka yi laꞌakari da adduꞌoꞌi da kuma waƙoƙin yabo da ke Littafi Mai Tsarki. Yayin da muke tunani a kan yadda bayin Allah suka bayyana masa abin da ke zukatansu, hakan zai sa mu ma mu yi koyi da su. Ƙari ga haka, za mu iya samun sabbin kalmomin yabo da za mu iya yin amfani da su saꞌad da muke adduꞌa. Kuma za mu iya samun adduꞌar da ta yi daidai da yanayin da muke ciki.

Kana Ji Kamar Yadda Suka Ji?

Bayin Jehobah sun gaya masa ainihin yadda suke ji a yanayoyi dabam-dabam. Shin, ka taɓa ji kamar yadda suka ji?

  • A lokacin da Yakubu yake cikin damuwa sosai, ya yi adduꞌa ga Jehobah. Amma ba game da matsalarsa kawai ba. Ya yi godiya kuma ya nuna cewa ya dogara ga Jehobah.—Far. 32:​9-12.

  • Saꞌad da Sarki Sulemanu ya ga kamar ba zai iya aikin da Jehobah ya ba shi ba da yake shi matashi ne, ya roƙi Jehobah ya taimaka masa.—1 Sar. 3:​7-9.

  • Bayan Dauda ya yi zina da Bath-sheba, ya roƙi Jehobah ya taimaka masa ya kasance da “zuciya marar ƙazanta.”—Zab. 51:​9-12.

  • Saꞌad da Maryamu ta sami damar yin aiki na musamman, ta yabi Jehobah.—Luk. 1:​46-49.

Abubuwan da za ka iya yin nazari a kai: Ka bincika adduꞌar da wani bawan Allah ya yi, kuma ka tambayi kanka, ‘Mene ne ya roƙi Jehobah?’ ‘Ta yaya ya yi hakan?’ ‘Kuma yaya Jehobah ya amsa adduꞌar?’ Saꞌan nan ka yi amfani da darasin da ka koya.

12. Waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi wa kanmu idan muka ga adduꞌar da wani ya yi a Littafi Mai Tsarki?

12 Idan ka ga wata adduꞌa a Littafi Mai Tsarki, ka tambayi kanka: ‘Wa ya yi adduꞌar kuma a wane yanayin ne ya yi hakan? Ina ji kamar yadda wanda ya yi adduꞌar nan ya ji? Wane darasi ne na koya daga adduꞌar?’ Mai yiwuwa za ka bukaci ka ƙara yin bincike don samun amsoshin tambayoyin nan. Idan ka samu, babu shakka, za ka ga cewa kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Bari mu ga adduꞌoꞌi huɗu da aka ambata a Littafi Mai Tsarki.

13. Wane darasi ne za mu iya koya daga adduꞌar da Hannatu ta yi? (1 Samaꞌila 1:​10, 11) (Ka kuma duba hoton.)

13 Karanta 1 Samaꞌila 1:​10, 11. A lokacin da Hannatu ta yi wannan adduꞌar, tana fama da manyan matsaloli guda biyu. Na ɗaya, bata haifuwa. Na biyu, kishiyarta tana sa ta baƙin ciki kowane lokaci. (1 Sam. 1:​4-7) Idan kai ma kana fama da matsalar da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa, me za ka iya koya daga adduꞌar da Hannatu ta yi? Ta ɗauki lokaci ta gaya wa Jehobah komen da ke damunta. Bayan hakan, sai hankalinta ya kwanta. (1 Sam. 1:​12, 18) Mu ma za mu samu sauƙi idan muka danƙa wa Jehobah dukan damuwarmu ta wurin gaya masa matsalolin da muke fama da su.—Zab. 55:22.

Hotuna: Na 1. Hannatu ta juya baya tana baƙin ciki yayin da mijinta Elkana yake wasa da yaransa biyu. Na 2. Feninna ta riƙe jaririnta tana murmushi. Na 3. Hannatu tana kuka saꞌad da take adduꞌa da dukan zuciyarta. Na 4. Babban Firist Eli yana zaune ya naɗe hannu yana kallon Hannatu.

Saꞌad da Hannatu take fama da rashin haihuwa, kuma kishiyarta tana sa ta baƙin ciki kullum, Hannatu ta gaya wa Jehobah kome da ke damunta (Ka duba sakin layi na 13)


14. (a) Mene ne kuma muka koya daga labarin Hannatu? (b) Ta yaya karanta Kalmar Allah da yin tunani a kan abin da muka karanta za su taimaka mana mu inganta yadda muke adduꞌa? (Ka duba ƙarin bayani.)

14 ꞌYan shekaru bayan Hannatu ta haifi Samaꞌila, ta kawo shi wurin Babban Firist Eli. (1 Sam. 1:​24-28) Ta yi adduꞌa, ta gaya wa Jehobah cewa tana godiya domin ta ga cewa yana kāre da kuma kula da bayinsa masu aminci.c (1 Sam. 2:​1, 8, 9) Ko da yake matsalolinta ba su ƙare kwata-kwata ba, Hannatu ta mai da hankali a kan albarkun da ta samu daga wurin Jehobah. Mene ne hakan ya koya mana? Za mu iya jimre matsalolin da muke fama da su idan mun mai da hankali a kan yadda Jehobah yake taimaka mana.

15. Idan aka yi mana rashin adalci, mene ne za mu iya koya daga adduꞌar da Irmiya ya yi? (Irmiya 12:1)

15 Karanta Irmiya 12:1. Akwai lokacin da annabi Irmiya ya damu sosai saꞌad da yake ganin kamar mugayen mutane suna jin daɗin rayuwarsu. Kuma sau da yawa ya yi sanyin gwiwa don yadda ꞌyanꞌuwansa Israꞌilawa suke yi masa baꞌa. (Irm. 20:​7, 8) Babu shakka, mun fahimci yadda ya ji. Domin mu ma ana yi mana baꞌa, kuma muna ganin yadda wasu mugayen mutanen suke jin daɗin rayuwarsu. Ko da yake Irmiya ya gaya wa Jehobah cewa abubuwan da yake gani suna sa shi damuwa, bai taɓa ce Jehobah marar adalci ne ba. Kuma da ya ga yadda Jehobah ya hukunta bayinsa da suka yi tawaye, hakan ya ƙara tabbatar masa cewa Jehobah Allah ne mai adalci. (Irm. 32:19) Mu ma za mu iya gaya wa Jehobah abin da ke damunmu, da tabbaci cewa nan ba da daɗewa ba, zai kawo ƙarshen duk wani rashin adalcin da muke fuskanta.

16. Mene ne za mu iya koya da adduꞌar da wani Balawi ya yi? (Zabura 42:​1-4) (Ka kuma duba hotunan.)

16 Karanta Zabura 42:​1-4. Wani Balawi ne ya rubuta waƙar nan. Kuma ya yi hakan ne a lokacin da bai sami damar bauta wa Jehobah a haikali tare da sauran Israꞌilawa ba. Abubuwan da ya rubuta sun nuna yadda yake ji. Za mu iya jin yadda ya ji idan yanayinmu ya sa ba za mu iya barin gidanmu ba, ko kuma idan aka jefa mu cikin kurkuku. A wasu lokuta za mu iya ji kamar abubuwa suna tafiya daidai, a wasu lokuta kuma sai mu soma baƙin ciki. Amma ko da yaya ne muke ji, zai dace mu roƙi Jehobah ya taimaka mana. Hakan zai sa mu yi tunani da kyau, kuma mu kasance da raꞌayin da ya dace game da yanayin da muke ciki. Alal misali, Balawin ya gano cewa yanayin da yake ciki zai iya sa ya sami wata damar yabon Jehobah. (Zab. 42:5) Ƙari ga haka, ya yi tunani a kan yadda Jehobah yake kāre shi. (Zab. 42:8) Yin adduꞌa ga Jehobah da dukan zuciyarmu zai taimaka mana mu fahimci yanayin da muke ciki, mu sami kwanciyar hankali kuma mu iya jimrewa.

Hotuna: Na 1. Wani Balawi yana adduꞌa saꞌad da yake daji. Na 2. Wani ɗanꞌuwa yana zaune ya gadon asibiti yana adduꞌa, kuma akwai Littafi Mai Tsarkinsa a kan cinyarsa.

Balawin da ya rubuta Zabura ta 42 ya gaya wa Jehobah kome da ke zuciyarsa. Idan mun gaya wa Jehobah ainihin yadda muke ji saꞌad da muke adduꞌa, hakan zai taimaka mana mu kasance da raꞌayin da ya dace game da yanayin da muke ciki (Ka duba sakin layi na 16)


17. (a) Me za mu iya koya daga adduꞌar da annabi Yona ya yi? (Yona 2:​1, 2) (b) Idan muna fama da wata matsala, ta yaya za mu amfana daga wasu furuci da ke littafin Zabura? (Ka duba ƙarin bayani.)

17 Karanta Yona 2:​1, 2. Annabi Yona ya yi wannan adduꞌar ne a cikin cikin babban kifi. Ko da yake bai yi abin da Jehobah ya gaya masa ya yi ba, ya kasance da tabbaci cewa Jehobah zai ji adduꞌarsa. Saꞌad da yake yin adduꞌa, Yona ya yi amfani da furuci da yawa da ke littafin Zabura.d Babu shakka ya san littafin Zabura sosai. Yin tunani a kan abin da ke littafin ya sa ya kasance da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka masa. Haka ma, idan mun haddace wasu nassosi da ke Littafi Mai Tsarki, za mu iya tuna da su saꞌad da muke adduꞌa, kuma hakan zai ƙarfafa mu idan muna fama da wata matsala.

KA CI-GABA DA KUSANTAR JEHOBAH TA WURIN YIN ADDUꞌA

18-19. Idan a wasu lokuta ba mu san abin da za mu gaya wa Jehobah a adduꞌa ba, ta yaya abin da ke Romawa 8:​26, 27, zai ƙarfafa mu? Ka ba da misali.

18 Karanta Romawa 8:​26, 27. A wasu lokuta, za mu iya damuwa sosai, har mu gagara bayyana wa Jehobah yadda muke ji. A irin wannan lokacin, ruhun Allah zai yi roƙo a madadin mu. Mene ne hakan yake nufi? Jehobah ya yi amfani da ruhu mai tsarki wajen sa marubutan Littafi Mai Tsarki su rubuta adduꞌoꞌi da yawa. Idan mun gagara gaya wa Jehobah yadda muke ji, Jehobah zai iya ɗaukan wasu adduꞌoꞌin da aka yi a matsayin abin da muke so mu roƙa. Kuma ya biya mana bukatarmu.

19 Abin da ya taimaka wa wata ꞌyarꞌuwa a ƙasar Rasha mai suna Yelena ke nan. An kama ta don tana adduꞌa da kuma karanta Littafi Mai Tsarki. Yelena ta damu sosai har yin adduꞌa ya yi mata wuya. Ta ce: “Na tuna cewa idan tsananin damuwa ya sa ban san abin da zan yi adduꞌa a kai ba, Jehobah zai ɗauka adduꞌoꞌin bayinsa a dā a matsayin abin da nake so in roƙa. Hakan ya ƙarfafa ni sosai a lokacin da nake fama da mawuyacin yanayi.”

20. Ta yaya za mu tattara hankalinmu wuri ɗaya idan muna cikin damuwa kuma muna so mu yi adduꞌa?

20 Idan muna cikin damuwa, zai iya yi mana wuya mu tattara hankalinmu wuri ɗaya saꞌad da muke yin adduꞌa. Wani abin da zai iya taimaka mana shi ne, karanta wasu surori a littafin Zabura da babban murya. Wani abu kuma shi ne rubuta yadda muke ji, kamar yadda Sarki Dauda ya yi. (Ka duba Zab. 18, 34, 142 da rubutun da ke saman kowannensu.) Gaskiyar ita ce, akwai abubuwa dabam-dabam da za mu iya yi da za su taimaka mana mu shirya zukatanmu kafin mu yi adduꞌa. (Zab. 141:2) Kowa ne zai zaɓi wanda ya fi dacewa da shi.

21. Me ya sa za mu iya yin adduꞌa da dukan zuciyarmu?

21 Abin ƙarfafa ne sanin cewa Jehobah yana fahimtar yadda muke ji tun kafin mu roƙe shi wani abu. (Zab. 139:4) Duk da haka, yana so mu gaya masa yadda muke ji kuma mu nuna cewa mun dogara gare shi. Saboda haka, kada ka bar wani abu ya hana ka yin adduꞌa ga Ubanmu na sama. Saꞌad da kake adduꞌa, za ka iya yin koyi da adduꞌoꞌin da ke Littafi Mai Tsarki. Ka yi adduꞌa da dukan zuciyarka. Ka gaya wa Jehobah abubuwan da suke sa ka farin ciki da waɗanda suke sa ka damuwa. Da yake shi amininka ne, ba zai taɓa barin ka ba!

MECE CE AMSARKA?

  • Me zai taimaka maka ka gaya wa Jehobah ainihin yadda kake ji saꞌad da kake adduꞌa?

  • Waɗanne abubuwa ne za ka iya yi don ka inganta yadda kake adduꞌa?

  • Ta yaya za mu amfana idan muka bincika adduꞌoꞌin da ke Littafi Mai Tsarki?

WAƘA TA 45 Abubuwan da Nake Tunani a Kai

a Ka duba “Halayen Jehobah” da aka ambata a Littafin Bincike don Shaidun Jehobah a ƙarƙashin jigon nan “Jehobah Allah.”

b A yawancin lokuta, adduꞌoꞌin da ake yi a ikilisiya a madadin ꞌyanꞌuwa gajeru ne.

c Saꞌad da take yin adduꞌa, Hannatu ta yi amfani da furucin da suka yi kama da abin da Musa ya rubuta. Babu shakka, takan yi tunani a kan abin da ke Nassosi. (M. Sha. 4:35; 8:18; 32:​4, 39; 1 Sam. 2:​2, 6, 7) Ɗarurruwan shekaru bayan hakan, mahaifiyar Yesu Maryamu ta yi amfani da irin kalmomin da Hannatu ta yi amfani da su wajen yabon Jehobah.—Luk. 1:​46-55.

d An jera Nassosin nan Zabura 69:1; 16:10; 30:3; 142:​2, 3; 143:​4, 5; 18:6; da 3:​8, yadda suke a adduꞌar da Yona ya yi a littafin Yona 2:​3-9.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba