Tambayoyi Daga Masu Karatu
Uku cikin Lingila sun ba da labarin gunaguni don shafa wa Yesu mai mai tsada. Shin manzanni da yawa ne suka yi gunaguni, ko kuma dai Yahuza ne kawai?
Mun sami labarin wannan abin da ya auku a Lingila ta Matiyu, Markus, da kuma Yahaya. Kamar dai Yahuza ne ya fara gunagunin, kuma aƙalla wasu manzannin suka yarda da abin da ya ce. Wannan abin da ya auku ya ba da dalilin da ya sa za mu yi godiya da muke da labarai kashi huɗu na Lingila. Abin da kowane marubuci ya rubuta daidai ne, amma ba su faɗi abu iri ɗaya ba. Ta wajen gwada wasu labarai, za mu ga cikakken yadda abin ya faru dalla-dalla.
Labarin da yake Matiyu 26:6-13 ya faɗi wurin da abin ya faru—a gidan Saminu kuturu, a Betanya—amma bai faɗi sunar matar da ta tsiyaye wa Yesu man turare a kā ba. Matiyu ya lura: “Amma da almajiran suka ga haka, sai suka ji haushi” (tafiyar tsutsa tamu ce), suka yi gunaguni suna cewa da an sayar da man an ba da kuɗin wa gajiyayyu.
Labarin Markus ya ƙunshi yawancin waɗannan abubuwan. Amma ya ƙara da cewa sai ta fasa ulun. Yana ɗauke da man ƙanshi na “nardi tsantsa,” kamar irin wanda ake kawowa daga Indiya. Game da gunagunin, Markus ya ba da rahoton cewa “waɗansu kuwa da suka ji haushi,” kuma “suka hasala da ita.” (Markus 14:3-9, tafiyar tsutsa tamu ce.) Saboda haka labarai biyun sun nuna cewa fiye da manzo ɗaya ne ya yi gunagunin. Amma yaya ya soma?
Yahaya, wanda ya shaidi abin da idonsa, ya ƙara fayyacewa. Ya faɗi sunar matar—Maryamu, ’yar’uwar Marta da Li’azaru. Yahaya kuma ya ƙara waɗannan bayani, wanda za mu ɗauka ƙarin bayani ne maimakon saɓani: “Ta shafa a ƙafafun Yesu, sa’an nan ta shafe su da gashinta.” (Tafiyar tsutsa tamu ce.) In aka tattaro labaran, za mu ga cewa Maryamu ta zuba man, wanda Yahaya ya tabbatar cewa “nardi tsantsa” ne, a kan Yesu da kuma ƙafafunsa. Yahaya ya shaƙu da Yesu ƙwarai kuma ba shi da wuya ya yi fushi idan aka yi wa Yesu rashin kunya. Mun karanta: “Yahuza Iskariyoti, ɗaya daga cikin almajiransa, wato wanda zai bashe shi, ya ce, ‘Me ya hana a sayar da man nan a kan dinari ɗari uku, a ba gajiyayyu kuɗin?’ ”—Yahaya 12:2-8.
Babu shakka, Yahuza “ɗaya daga cikin almajiransa” ne, amma za ka ga fushin Yahaya cewa wanda yake da irin wannan matsayin yana shirin ya bashe Yesu. Mai fassara Dokta C. Howard Matheny ya lura game da Yahaya 12:4: “Furcin nan ‘ya kusa ya’ [ko, “zai”] da kuma ‘yana bashe’ [ko, “zai bashe”] duka suna nuna abin da yake faruwa ne. Wannan ya nuna cewa bashe Yesu da Yahuza ya yi ba abin da ya faru farat ɗaya ba ne amma abin da ya yi tunaninsa ne kuma ya shirya cikin kwanaki da yawa.” Yahaya ya ƙara fayyace dalilin gunagunin Yahuza “ba wai don yana kula da gajiyayyu ba, a’a, sai dai don shi ɓarawo ne, da ya ke kuma jakar kuɗinsu na hannunsa yakan riƙa taɓa abin da ke ciki.”
Saboda haka, ya tabbata cewa Yahuza ɓarawon ne ya fara gunaguni domin zai sami kuɗi da yawa ya sata idan aka sayar da man mai tsadan gaske aka zuba kuɗin a cikin jakar kuɗi da take hannunsa. Da Yahuza ya yi gunaguni, wasu manzannin wataƙila sun yi gunaguni su ma domin suna ganin shawararsa tana da kyau. Saboda haka, Yahuza, ne ainihin wanda ya fara gunagunin.