Ta Hannun Markus
11 Saꞌad da suka yi kusa da Urushalima, kuma suka kai Baitꞌfaji da Betani da ke Tudun Zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu, 2 ya ce musu: “Ku shiga cikin ƙauyen nan da kuke gani, da zarar kun shiga, za ku ga wani ɗan jaki da aka ɗaure wanda ba a taɓa hawan sa ba. Ku kunce shi ku kawo shi nan. 3 Idan wani ya ce muku, ‘Don me kuke haka?’ ku ce masa, ‘Ubangiji ne yake bukatar sa, zai kuma mayar da shi nan da nan.’” 4 Sai almajiran suka tafi, suka samu ɗan jakin ɗaure a ƙofar gida, a bakin hanya, kuma suka kunce shi. 5 Sai wasu daga cikin mutanen da suke tsaye a wurin suka ce musu: “Me ya sa kuke kunce ɗan jakin?” 6 Sai almajiran suka gaya wa mutanen daidai abin da Yesu ya gaya musu, kuma mutanen suka bar su su tafi.
7 Sai suka kawo wa Yesu ɗan jakin, suka shimfiɗa mayafinsu a kan jakin, Yesu kuma ya zauna a kai. 8 Ƙari ga haka, mutane da yawa sun shimfiɗa mayafinsu a kan hanya. Wasu kuma sun yanka ganyayen itatuwa daga gonaki. 9 Kuma waɗanda suke gabansa, da waɗanda suke bin sa a baya suna ta ihu, suna cewa: “Ya Allah, muna roƙo, ka cece shi! Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Jehobah!* 10 Albarka ta tabbata ga Mulkin nan mai zuwa na babanmu Dauda! Muna roƙon ka, ka cece shi, kai da kake cikin sama!” 11 Saꞌad da ya kai Urushalima, sai ya shiga cikin haikali, ya dudduba kome. Amma da yake lokaci ya riga ya ƙure, sai ya fita ya koma Betani tare da almajiransa goma sha biyu.
12 Washegari da suke barin Betani, yunwa ta kama shi. 13 Sai ya ga wani itacen ɓaure cike da ganye daga nesa, sai ya je wurin ya duba ko zai samu ꞌyaꞌyan itacen. Amma saꞌad da ya zo wurin, bai samu kome ba sai ganye, domin ba lokacin ꞌyaꞌyan ɓaure ba ne. 14 Sai ya ce wa itacen: “Kada kowa ya ƙara cin ꞌyaꞌyanka har abada.” Kuma almajiransa suna jin abin da yake faɗa.
15 Da suka kai Urushalima, Yesu ya shiga cikin haikali, sai ya soma koran waɗanda suke saya da sayarwa, kuma ya tutture teburan masu canja kuɗi, da kujerun masu sayar da kurciyoyi, 16 ya kuma hana kowa ya ɗauki wani abu ya wuce ta filin haikalin. 17 Sai ya soma koyar da su yana cewa: “Ba a rubuce yake cewa: ‘Za a ce da gidana, gidan adduꞌa don dukan alꞌummai ba’? Amma kun mai da shi wurin ɓuyan ɓarayi.” 18 Saꞌad da manyan firistoci da marubuta suka ji abin da ya faru, sai suka soma neman yadda za su kashe shi; suna jin tsoron sa domin dukan jamaꞌar sun yi mamakin yadda yake koyarwa.
19 Da yamma ta kusa, sai suka fita daga cikin birnin. 20 Amma saꞌad da suke wucewa da safe, sai suka ga cewa itacen ɓauren ya bushe gabaki-ɗaya daga jijiyarsa. 21 Sai Bitrus ya tuna, kuma ya ce masa: “Malam,* duba! itacen ɓaure da ka laꞌanta ya riga ya bushe.” 22 Sai Yesu ya amsa musu ya ce: “Ku ba da gaskiya ga Allah. 23 A gaskiya ina gaya muku, duk wanda ya ce wa tudun nan, ‘Ka tashi ka faɗi a cikin teku,’ kuma bai yi shakka a cikin zuciyarsa ba, amma ya ba da gaskiya cewa abin da ya faɗa zai faru, hakan zai faru. 24 Shi ya sa ina gaya muku cewa, duk abubuwan da kuka yi adduꞌa kuma kuka roƙa, ku ba da gaskiya cewa kun samu, kuma za a ba ku su. 25 Saꞌad da kuka tsaya kuna adduꞌa, ku gafarta duk laifin da wani ya yi muku, domin Ubanku wanda yake cikin sama shi ma ya gafarta muku zunubanku.” 26* ——
27 Sai suka sake koma Urushalima. Kuma yayin da yake tafiya cikin haikali, sai manyan firistoci da marubuta da dattawa suka zo 28 kuma suka ce masa: “Da wane iko ne kake yin abubuwan nan? Ko kuma wane ne ya ba ka ikon yin abubuwan nan?” 29 Sai Yesu ya ce musu: “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Idan kun ba ni amsa, zan gaya muku da wane iko nake yin abubuwan nan. 30 Ku faɗa mini, daga sama ne Yohanna ya samu izinin yin baftisma, ko kuma daga wurin mutane ne?” 31 Sai suka soma yin magana a tsakaninsu suna cewa: “Idan muka ce masa, ‘Daga sama ne,’ zai ce mana, ‘To me ya sa ba ku yarda da shi ba?’ 32 Amma kada mu kuskura mu ce, ‘Daga wurin mutane ne.’” Suna tsoron jamaꞌa, domin dukan jamaꞌar sun ɗauki Yohanna a matsayin annabi. 33 Sai suka amsa wa Yesu, suka ce: “Ba mu sani ba.” Shi kuma ya ce musu: “Ni ma ba zan gaya muku da wane iko nake yin abubuwan nan ba.”