28 GA YULI–3 GA AGUSTA
KARIN MAGANA 24
Waƙa ta 38 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. Ka Shirya Kanka don Ka Iya Magance Matsaloli a Nan Gaba
(minti 10)
Ku ci gaba da samun ƙarin ilimi da hikima (K. Ma 24:5; it-2-E 610 sakin layi na 8)
Saꞌad da kake sanyin gwiwa, ka tabbata kana adduꞌa da karanta Littafi Mai Tsarki da kuma halartan taro a kowane lokaci (K. Ma 24:10; w09 12/15 18 sakin layi na 12-13)
Idan muna da bangaskiya sosai kuma muna ƙaunar Jehobah, hakan zai sa mu shawo kan matsaloli (K. Ma 24:16; w20.12 15)
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
K. Ma 24:27—Me muka koya daga wannan karin maganar? (w09 10/15 12)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) K. Ma 24:1-20 (th darasi na 11)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 2) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Kun gama hira, da kake so ka soma yi masa waꞌazi, sai wani abu ya sa mutumin ya tafi. (lmd darasi na 2 batu na 4)
5. Fara Magana da Mutane
(minti 3) WAꞌAZI GIDA-GIDA. (lmd darasi na 3 batu na 4)
6. Fara Magana da Mutane
(minti 3) WAꞌAZI A INDA JAMAꞌA SUKE. Ka gaya wa mutumin yadda muke nazari da mutane, sai ka ba mutumin katin nazarin Littafi Mai Tsarki. (lmd darasi na 4 batu na 3)
7. Jawabi
(minti 3) lmd ƙarin bayani na 1 batu na 11—Jigo: Allah Yana Magana da Mu. (th darasi na 6)
Waƙa ta 99
8. Ku Taimaka wa Juna a Lokacin Wahala
(minti 15) Tattaunawa.
Annoba da balaꞌi da taꞌaddanci da yaƙi da kuma tsanantawa za su iya faruwa ba zato ba tsammani. Idan hakan ya faru, ꞌyanꞌuwa sukan haɗa kai su taimaka da kuma ƙarfafa juna. Ko da abubuwan nan ba su faru da mu ba, muna baƙin ciki idan hakan ya faru da ꞌyanꞌuwanmu, kuma muna iya ƙoƙarinmu don mu taimaka musu.—1Ko 12:25, 26.
Karanta 1 Sarakuna 13:6 da Yakub 5:16b. Sai ka tambayi masu sauraro:
Me ya sa yin adduꞌa a madadin ꞌyanꞌuwa yana taimakawa?
Karanta Markus 12:42-44 da 2 Korintiyawa 8:1-4. Sai ka tambayi masu sauraro:
Ko da ba mu da abu da yawa da za mu ba ꞌyanꞌuwa da suke da bukata, me ya sa ya kamata mu bayar ko da kaɗan ne?
Ku kalli BIDIYON An Ƙarfafa ’Yan’uwa Lokacin da Aka Hana Aikinmu. Sai ka tambayi masu sauraro:
Waɗanne sadaukarwa ne ꞌyanꞌuwanmu suka yi don su taimaka wa ꞌyanꞌuwa da suke zama a wuraren da aka hana aikinmu a Gabashin Turai?
A lokacin da aka hana aikinmu, ta yaya ꞌyanꞌuwa suka bi umurni game da yin taro da kuma ƙarfafa juna?—Ibr 10:24, 25
9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) lfb darasi na 4-5