Litinin, 28 ga Yuli
Ruhun Allah da yake cikinku ya fi ruhun da yake cikin mutanen da suke na duniya.—1 Yoh. 4:4.
Idan kana jin tsoro, ka yi tunani a kan abin da Jehobah zai yi a nan gaba bayan an hallaka Shaiɗan. A wani gwaji da aka yi a taron yanki na 2014, wani mahaifi ya bayyana wa iyalinsa yadda kalaman da ke 2 Timoti 3:1-5 za su kasance idan ana annabci ne game da Aljanna. Ya ce: ‘A sabuwar duniya, za a yi farin ciki sosai. Gama mutane za su zama masu son juna, masu son ibada, masu sanin kasawarsu, masu tawaliꞌu, masu yabon Allah, masu biyayya ga iyayensu, masu godiya, masu tsarki, masu ƙaunar iyalinsu sosai, masu gafartawa, masu yin maganganu masu kyau game da waɗansu. Masu kame kansu, masu tausayi, masu son nagarta, masu riƙon amana, masu hankali, masu sauƙin kai, masu son Allah fiye da jin daɗi, kuma suna da dangantaka mai kyau da Allah. Masu bauta wa Allah da gaske. Ka manne wa irin mutanen nan.’ Kana tattaunawa da iyalinka ko ꞌyanꞌuwa game da yadda rayuwa za ta kasance a sabuwar duniya? w24.01 6 sakin layi na 13-14
Talata, 29 ga Yuli
Ina jin daɗinka ƙwarai.—Luk. 3:22.
Sanin cewa Jehobah ya amince da bayinsa yana da ban ƙarfafa! Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yahweh yakan ji daɗin mutanensa.” (Zab. 149:4) Amma a wasu lokuta, Kirista zai iya yin sanyin gwiwa kuma ya soma shakkar ko Jehobah ya amince da shi. Akwai bayin Allah masu aminci da yawa a Littafi Mai Tsarki da su ma sun yi fama da irin wannan tunani. (1 Sam. 1:6-10; Ayu. 29:2, 4; Zab. 51:11) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ꞌyan Adam ajizai za su iya samun amincewar Allah. Ta yaya? Ta wurin ba da gaskiya ga Yesu Kristi da kuma yin baftisma. (Yoh. 3:16) Ta yin hakan, za mu nuna wa mutane cewa mun tuba daga zunubanmu kuma mun yi alkawarin yin nufin Jehobah. (A. M. 2:38; 3:19) Jehobah zai yi farin ciki sosai idan muka ɗau matakan nan don mu zama abokansa. Idan muka ci-gaba da cika alkawarin da muka yi cewa za mu yi nufin Jehobah, Jehobah zai amince da mu kuma zai ɗauke mu a matsayin abokansa.—Zab. 25:14. w24.03 26 sakin layi na 1-2
Laraba, 30 ga Yuli
Ba za mu iya yin shiru a kan abin da muka ji, muka kuma gani ba.—A. M. 4:20.
Za mu iya yin koyi da almajiran Yesu ta wajen ci-gaba da yin waꞌazi ko da hukuma ta ce mu daina yin hakan. Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana mu iya yin aikin da ya ba mu. Don haka mu roƙi Jehobah ya ba mu ƙarfin zuciya da hikima, kuma ya taimake mu mu iya jimre matsalolinmu. Yawancinmu muna fama da matsaloli dabam-dabam. Ko rashin lafiya, ko rasuwar wani da muke ƙauna, ko wata matsala a iyalinmu, ko tsanantawa da dai sauran su. Annoba da tashe-tashen hankula sun sa jimre wa matsalolin nan ya ƙara yin wuya. Idan kana cikin matsala, ka faɗa wa Jehobah duk abin da ke zuciyarka. Ka bayyana masa abin da ke faruwa da kai kamar yadda za ka gaya wa amininka. Tabbas, Jehobah zai taimake ka, “zai lura da kai.” (Zab. 37:3, 5) Idan muka nace da yin adduꞌa, zai taimaka mana mu “yi haƙuri a cikin azaba.” (Rom. 12:12) Jehobah ya san matsalolin da bayinsa suke fuskanta. “Yakan kuma ji kukansu ya cece su.”—Zab. 145:18, 19. w23.05 5-6 sakin layi na 12-15