Ta Hannun Matiyu
13 A ranar, Yesu ya bar gidan ya je ya zauna a bakin teku. 2 Sai jamaꞌa da yawa suka taru wajensa, har sai da ya shiga cikin jirgin ruwa ya zauna, kuma dukan taron jamaꞌar sun tsaya a bakin tekun. 3 Sai ya koya musu abubuwa da yawa ta wajen yin amfani da misalai, yana cewa: “Wani mutum ya fita don ya je ya yi shuki. 4 Yayin da yake shukin, wasu iri sun faɗi a kan hanya, kuma tsuntsaye sun zo sun cinye su. 5 Waɗansu kuma suka faɗi a wuri mai duwatsu, inda babu ƙasa sosai, kuma suka tsira da sauri saboda ƙasar ba zurfi. 6 Amma da rana ta fito, sai ta ƙone su, kuma suka bushe domin ba su da jijiya. 7 Wasu kuma suka faɗi a cikin ƙayoyi kuma ƙayoyin suka yi girma suka kashe su. 8 Wasu kuma suka faɗi a ƙasa mai kyau, kuma suka soma ba da amfani, wannan ya ba da amfani sau ɗari, wancan kuma sau sittin, wani kuma sau talatin. 9 Bari mai kunne ya kasa kunne ya ji.”
10 Sai almajiran Yesu suka zo suka ce masa: “Me ya sa kake yi musu magana ta wurin misalai?” 11 Sai ya amsa musu ya ce: “Ku dai an yarda muku ku gane asirai masu tsarki na Mulkin sama, amma su ba a yarda su fahimta ba. 12 Domin duk wanda yake da abu, za a ƙara masa har ya yi yawa sosai. Amma duk wanda bai da abu, za a ɗauke har ɗan abin da yake da shi. 13 Shi ya sa nake yi musu magana ta wurin misalai; domin suna dubawa, amma ba sa ganin wani abu, suna kasa kunne, amma ba sa jin kome, kuma ba sa fahimtar abin da suke ji. 14 Ƙari ga haka, annabcin Ishaya yana cika a kansu. Ya ce: ‘Hakika, za ku ji, amma ba za ku taɓa fahimta ba. Hakika, za ku duba, amma ba za ku taɓa ganin wani abu ba. 15 Domin zuciyar mutanen nan ta yi tauri, suna ji da kunnuwansu amma ba sa yin abubuwan da suka ji. Sun kuma rufe idanunsu don kada su taɓa gani da idanunsu, kada kuma su ji da kunnuwansu domin kada su fahimta har su juyo in kuma warkar da su.’
16 “Amma ku riƙa farin ciki, domin idanunku suna gani, kunnuwanku kuma suna ji. 17 A gaskiya ina gaya muku, annabawa da masu adalci da yawa sun so su ga abubuwan da kuke gani, amma ba su gani ba. Sun so su ji abubuwan da kuke ji, amma ba su ji ba.
18 “To, ga abin da misalin mai shukin nan yake nufi. 19 Irin da ya faɗi a kan hanya shi ne misalin mutumin da ya ji saƙon Mulkin kuma bai fahimce shi ba, saꞌan nan mugun nan ya zo ya ƙwace abin da aka shuka a cikin zuciyarsa. 20 Irin da ya faɗi a wurin da akwai duwatsu kuwa, shi ne misalin mutum wanda da zarar ya ji kalmar Allah, sai ya karɓe ta da farin ciki nan take. 21 Amma da yake kalmar ba ta yi jijiya a zuciyarsa ba, bai daɗe ba, kuma saꞌad da ya yi fama da azaba ko tsanantawa saboda kalmar, sai nan take ya yi tuntuɓe. 22 Irin da ya faɗi a cikin ƙayoyi, shi ne misalin mutumin da yake jin kalmar, amma yawan damuwa na wannan zamanin da kuma yadda son arziki yake ruɗin mutane sun kashe kalmar, don haka, ta kasa ba da amfani. 23 Irin da ya faɗi a ƙasa mai kyau, shi ne misalin mutumin da ya ji kalmar Allah kuma ya fahimce ta, sai ya ba da amfani. Wannan ya ba da amfani sau ɗari, wancan kuma sau sittin, wani kuma sau talatin.”
24 Ya sake ba su wani misali cewa: “Za a iya kwatanta Mulkin sama da wani mutum da ya shuka iri mai kyau a gonarsa. 25 Da mutane suke barci, sai abokin gābansa ya zo ya shuka ciyayi a cikin alkamar kuma ya tafi. 26 Saꞌad da alkamar suka tsiro, kuma suka ba da amfani, ciyayin ma sun fito. 27 Sai bayin mutumin suka zo suka ce masa, ‘Maigida, ba iri mai kyau ne ka shuka a gonarka ba? To, ta yaya ciyayi suka fito a wurin?’ 28 Sai ya ce musu, ‘Abokin gābana ne ya yi wannan.’ Sai bayinsa suka ce masa, ‘Kana so ne mu je mu ciccire ciyayin?’ 29 Amma ya ce, ‘Aꞌa, kada garin cire ciyayin ku cire tare da alkamar. 30 Bari dukansu su yi girma tare har lokacin girbi. A lokacin, zan gaya wa masu girbin cewa: Ku fara ciccire ciyayin ku tara, ku ɗaɗɗaure su don a ƙona; amma ku tara alkamar ku zuba a rumbuna.’”
31 Sai ya sake ba su wani misali yana cewa: “Mulkin sama yana kama da ƙwayar mastad* da wani mutum ya ɗauko ya shuka a gonarsa. 32 Ƙwayar ce ta fi ƙanƙanta a cikin sauran iri, amma idan ta yi girma, sai ta fi dukan sauran abubuwan da aka shuka, ta zama babban itace, har ma tsuntsayen sama sukan zo su soma yin gidajensu a kan rassansa.”
33 Ya sake ba su wani misali ya ce: “Mulkin sama yana kama da yisti wanda wata mace ta ɗauka ta kwaɓa da mudu uku na garin fulawa, har sai da dukan garin da aka kwaɓa ya kumbura.”
34 Yesu ya gaya wa taron jamaꞌar dukan abubuwan nan ta wurin misalai. Hakika, ba ya gaya musu kome sai tare da misali, 35 domin a cika abin da aka faɗa ta wurin bakin annabi da ya ce: “Zan yi magana da misalai. Zan sanar da abin da yake a ɓoye tun farkon duniya.”*
36 Bayan da Yesu ya sallami taron jamaꞌar, sai ya shiga cikin gida. Almajiransa suka zo suka same shi suka ce: “Ka bayyana mana abin da misalin ciyayi a gona yake nufi.” 37 Sai ya amsa musu ya ce: “Ɗan mutum ne ya shuka iri mai kyau. 38 Gonar ita ce duniya. Iri masu kyau kuma su ne ꞌyaꞌyan Mulkin, amma ciyayin su ne ꞌyaꞌyan mugun nan. 39 Ibilis ne abokin gāba da ya shuka ciyayin. Lokacin girbin shi ne ƙarshen zamanin* nan kuma malaꞌiku ne masu girbin. 40 Kamar yadda aka tara ciyayin kuma aka ƙone su da wuta, haka zai zama a ƙarshen zamanin* nan. 41 Ɗan mutum zai aiko da malaꞌikunsa kuma za su tattara dukan abubuwan da ke jawo tuntuɓe da dukan mutanen da ke aikata zunubi, su cire su daga Mulkinsa. 42 Kuma za su jefa su a cikin wuta mai ci sosai. A wurin ne za su yi ta kuka da cizon haƙora. 43 A lokacin, masu adalci za su haskaka kamar rana a Mulkin Ubansu. Bari mai kunne ya kasa kunne ya ji.
44 “Mulkin sama yana kama da dukiya da aka ɓoye a cikin gona, wadda wani mutum ya samu ya sake ɓoye ta; kuma saboda farin ciki ya je ya sayar da dukan abubuwan da yake da su ya sayi gonar.
45 “Ƙari ga haka, Mulkin sama yana kama da ɗan kasuwa da yake tafiye-tafiye yana neman luꞌuluꞌai* masu kyau. 46 Da ya sami wani luꞌuluꞌu mai daraja sosai, ya koma kuma nan da nan ya sayar da dukan abubuwan da yake da su ya sayi luꞌuluꞌun.
47 “Har ila, Mulkin sama yana kama da ragar kamun kifi da aka jefa cikin teku kuma ta kamo kifaye iri-iri. 48 Da ta cika, sai suka jawo ta zuwa bakin teku, kuma suka zauna suka ware masu kyau suka zuba a kwanduna, amma suka zubar da marasa kyau. 49 Haka zai zama a ƙarshen zamani.* Malaꞌiku za su zo su ware mugaye daga masu adalci, 50 kuma za su jefa su a cikin wuta mai ci sosai. A wurin ne za su yi ta kuka da cizon haƙora.
51 “Kun gane abin da dukan abubuwan nan suke nufi?” Suka ce masa: “E.” 52 Sai ya ce musu: “Saboda haka, duk malamin da aka koya masa game da Mulkin sama, yana kama da wani mutum wanda maigida ne da ya fitar da abubuwa masu daraja sababbi da tsofaffi daga ajiyarsa.”
53 Da Yesu ya gama ba da waɗannan misalan, sai ya bar wurin. 54 Bayan da ya shigo yankin da ya yi girma, sai ya soma koyar da mutane a majamiꞌunsu. Mutanen sun yi mamaki sosai kuma suka ce: “Daga ina ne wannan mutumin ya sami hikimar nan, da ikon yin waɗannan ayyukan ban mamaki? 55 Wannan ba shi ne ɗan kafintan nan ba? Sunan mamarsa ba Maryamu ba ne? Ba ꞌyanꞌuwansa ne su Yaƙub, da Yusufu, da Siman, da kuma Yahuda ba? 56 Ba dukan ꞌyanꞌuwansa mata suna tare da mu ba? To, daga ina ne ya samo dukan abubuwan nan?” 57 Saboda haka, suka ƙi yarda da shi. Amma Yesu ya ce musu: “Ai, annabi ba ya rasa daraja, sai dai a yankinsa da kuma cikin gidansa.” 58 Kuma bai yi ayyuka da yawa masu ban mamaki a wurin ba, saboda rashin bangaskiyarsu.