Ta Hannun Matiyu
14 A lokacin, Hirudus* wanda shi ne ke mulkin yankin, ya ji labari game da Yesu 2 kuma ya ce wa bayinsa: “Wannan Yohanna Mai Baftisma ne. An ta da shi daga mutuwa, shi ya sa ake yin ayyukan ban mamakin nan ta wurinsa.” 3 Dā ma Hirudus ya kama Yohanna ya ɗaure shi kuma ya saka shi a kurkuku saboda Hirudiya, matar ɗanꞌuwansa Filibus. 4 Domin Yohanna ya sha gaya masa cewa: “Bai dace ka aure ta ba.” 5 Ko da yake ya so ya kashe Yohanna, amma ya ji tsoron jamaꞌa, domin sun ɗauki Yohanna a matsayin annabi. 6 Amma da ake bikin ranar haifuwar Hirudus, ꞌyar Hirudiya ta yi rawa a bikin kuma hakan ya sa Hirudus farin ciki sosai 7 har ya yi alkawari da rantsuwa cewa zai ba ta duk abin da take so. 8 Sai ta bi shawarar da mamarta ta ba ta, kuma ta ce: “Ka ba ni kan Yohanna Mai Baftisma a kan faranti.” 9 Ko da yake ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwar da ya yi a gaban waɗanda suke cin abinci da shi, ya ba da umurni cewa a ba ta. 10 Sai Hirudus ya tura mutane kurkuku su yanko kan Yohanna. 11 Sai aka kawo kan a faranti aka ba wa yarinyar, ita kuwa ta kai wa mamarta. 12 Daga baya, almajiran Yohanna suka zo suka ɗauki gawarsa suka binne; sai suka je suka gaya wa Yesu. 13 Da Yesu ya ji haka, sai ya shiga jirgin ruwa, ya haye zuwa wani wurin da ba kowa don ya kasance shi kaɗai. Amma da mutane suka ji haka, sai suka fito daga garuruwa suka bi shi da ƙafa.
14 Da ya isa bakin tekun, sai ya ga jamaꞌa da yawa kuma ya ji tausayin su, sai ya warkar da marasa lafiya a cikinsu. 15 Amma da yamma ta yi, sai almajiransa suka zo, suka ce masa: “Ba kowa a wurin nan fa, kuma yamma ta riga ta yi; ka sallami mutanen nan don su je ƙauyuka, su saya wa kansu abinci.” 16 Amma Yesu ya ce musu: “Ba sai sun tafi ba; ku ba su abin da za su ci.” 17 Sai suka ce masa: “Ba mu da kome a nan, sai burodi biyar da kifi biyu.” 18 Sai ya gaya musu cewa: “Ku kawo mini su a nan.” 19 Sai ya gaya wa jamaꞌar su zauna a kan ciyawa. Sai ya ɗauki burodi guda biyar ɗin, da kifi biyun, ya kalli sama kuma ya yi godiya. Sai ya rarraba burodin, ya ba wa almajiransa, almajiran kuwa suka ba wa jamaꞌar. 20 Sai dukansu suka ci suka ƙoshi, kuma suka tattara duk abin da ya rage har ya cika kwanduna goma sha biyu. 21 Waɗanda suka ci abincin sun kai wajen maza dubu biyar, ban da mata da yara. 22 Ba tare da ɓata lokaci ba, sai ya sa almajiransa su shiga jirgin ruwa, su haye zuwa ɗayan gefen tekun don su jira shi, shi kuwa ya tsaya domin ya sallami jamaꞌar.
23 Bayan da ya sallame su, sai ya haura kan tudu shi kaɗai don ya yi adduꞌa. Har dare ya yi yana can shi kaɗai. 24 A lokacin kuwa, jirgin ya riga ya yi nisa sosai* daga gaɓar tekun, raƙuman ruwa suna buga jirgin, kuma iska mai ƙarfi tana busowa tana mai da jirgin baya. 25 Da asuba,* sai ga Yesu yana takawa a kan tekun zuwa wurin almajiransa. 26 Da almajiran suka gan shi yana tafiya a kan tekun, sai tsoro ya kama su, kuma suka ce: “Fatalwa ce!” Kuma suka soma ihu saboda tsoro. 27 Nan da nan, sai Yesu ya yi musu magana ya ce: “Ku kwantar da hankalinku! Ni ne; kada ku ji tsoro.” 28 Sai Bitrus ya amsa ya ce: “Ubangiji, in kai ne, ka umurce ni in zo wurinka a kan tekun.” 29 Yesu ya amsa masa ya ce: “Ka zo!” Sai Bitrus ya fita daga jirgin ruwan kuma ya soma takawa a kan tekun zuwa wurin Yesu. 30 Amma da ya ga iskar ta yi ƙarfi, sai ya ji tsoro. Kuma da ya fara nitsewa sai ya yi ihu ya ce: “Ubangiji, ka cece ni!” 31 Nan da nan, Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi kuma ya ce masa: “Ya kai mai ƙarancin bangaskiya, me ya sa ka yi shakka?” 32 Bayan da suka shiga cikin jirgin ruwan, sai iskar ta daina hurawa. 33 Sai waɗanda suke cikin jirgin ruwan suka durƙusa a gabansa suka ce: “A gaskiya, kai Ɗan Allah ne.” 34 Sai suka ƙetare tekun kuma suka isa Ganisaret.
35 Da mutane suka gane shi, sai suka yaɗa labarinsa a ƙasashen da ke kewaye da wurin, kuma mutane suka kawo masa dukan waɗanda suke rashin lafiya. 36 Suka roƙe shi ya bar su su taɓa bakin mayafinsa kawai, kuma dukan waɗanda suka taɓa kuwa sun warke.