Ta Hannun Matiyu
18 A lokacin, almajiran Yesu suka zo wurinsa suka tambaye shi cewa: “Wane ne ya fi girma a Mulkin sama?” 2 Sai ya kira wani ƙaramin yaro, kuma ya sa shi ya tsaya a tsakiyarsu, 3 ya ce: “A gaskiya ina gaya muku, idan ba ku canja kun zama kamar ƙananan yara ba, ba za ku taɓa shiga cikin Mulkin sama ba. 4 Saboda haka, duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar ƙaramin yaron nan, shi ne mafi girma a Mulkin sama; 5 kuma duk wanda ya marabci ƙaramin yaro kamar wannan saboda sunana, ya marabce ni ma. 6 Amma duk wanda ya sa ɗaya daga cikin ƙananan nan da suka ba da gaskiya gare ni tuntuɓe, zai fi wa mutumin a rataya a wuyarsa babban dutsen niƙa da jaki yake juyawa kuma a jefa shi a cikin teku don ya nitse.
7 “Kaiton duniya, saboda abubuwan da ke sa mutane tuntuɓe! A gaskiya, dole ne a samu abubuwan da za su sa mutane tuntuɓe, amma kaiton mutumin da ya sa wasu tuntuɓe! 8 Idan hannunka ko ƙafarka yana sa ka tuntuɓe, ka yanke shi ka yar. Zai fi maka ka samu rai na har abada da hannu ɗaya ko ƙafa ɗaya, da a jefa ka da hannaye biyu da ƙafafu biyu cikin wuta na har abada. 9 Ƙari ga haka, idan idonka yana sa ka tuntuɓe, ka cire shi ka yar. Zai fi maka ka samu rai na har abada, da ido ɗaya, maimakon a jefa ka cikin wutar Gehenna* da idanu biyu. 10 Ku kula, kada ku rena ko ɗaya daga cikin ƙananan nan. Domin ina gaya muku cewa, a kullum malaꞌikunsu a sama suna gaban Ubana wanda yake sama. 11* ——
12 “Me kuke tsammani? Idan mutum yana da tumaki ɗari, sai ɗaya a cikinsu ya ɓata, ba zai bar sauran casaꞌin da tara a kan tuddai kuma ya je ya nemi ɗayan da ya ɓata ba? 13 A gaskiya ina gaya muku, zai yi farin ciki sosai idan ya samu ɗayan da ya ɓata, fiye da casaꞌin da tara da ba su ɓata ba. 14 Haka nan ma, Ubana* wanda yake cikin sama ba ya so ko ɗaya daga cikin ƙananan nan ya hallaka.
15 “Ƙari ga haka, idan ɗanꞌuwanka ya yi zunubi, ka je ka gaya masa laifinsa* tsakanin ku biyun kawai. Idan ya saurare ka, ka maido da ɗanꞌuwanka hanyar da ta dace ke nan. 16 Amma idan bai saurare ka ba, sai ka sake zuwa wurinsa tare da mutum ɗaya ko biyu. Domin ta wurin shaidar* mutum biyu ko uku za a iya tabbatar da kowace magana. 17 Idan bai saurare su ba, ka gaya wa ikilisiya. Idan ya ƙi ya saurari ikilisiyar ma, ka mai da shi kamar wanda bai san Allah ba,* da kuma mai karɓan haraji.
18 “A gaskiya ina gaya muku, duk abubuwan da kuka ɗaure a duniya, an riga an ɗaure su a sama. Kuma duk abubuwan da kuka kunce a duniya, an riga an kunce su a sama. 19 Har ila ina gaya muku, idan mutane biyu daga cikinku suka yarda su roƙi abu mai muhimmanci, Ubana da ke cikin sama zai ba su abin da suka roƙa. 20 Domin duk inda mutane biyu ko uku suka taru cikin sunana, ina tare da su.”
21 Sai Bitrus ya zo ya sami Yesu, ya ce: “Ubangiji, sau nawa ne ya kamata ɗanꞌuwana ya yi mini laifi kuma in yafe masa? Har sau bakwai ne?” 22 Yesu ya ce masa: “Ina gaya maka cewa, ba sau bakwai kawai ba, amma har sau sabaꞌin da bakwai.
23 “Shi ya sa za a iya kwatanta Mulkin sama da wani sarki da yake so bayinsa su biya bashin da yake bin su. 24 Saꞌad da ya soma karɓan bashinsa, sai aka kawo masa wani da ya ci bashin talenti dubu goma.* 25 Amma da yake ba zai iya biyan bashin ba, maigidan ya ce a sayar da shi, da matarsa, da yaransa, da duk abin da yake da shi don ya biya bashin. 26 Sai bawan ya durƙusa a gabansa, ya ce, ‘Ka yi haƙuri da ni, zan biya ka duk bashin da kake bi na.’ 27 Sai maigidan ya ji tausayin bawan, ya ce a bar shi, kuma ya yafe masa bashin. 28 Da bawan ya fita, sai ya ga wani bawan da yake bin bashin dinari* ɗari, sai ya shaƙe masa wuya ya ce, ‘Ka biya ni duk abin da nake bin ka.’ 29 Sai bawan ya durƙusa a gabansa yana roƙon sa yana cewa, ‘Ka yi haƙuri da ni, zan biya ka.’ 30 Amma ya ƙi jin roƙonsa, kuma ya sa aka sa shi a kurkuku, har sai ya biya dukan bashin da ya ci. 31 Da sauran bayin suka ga abin da ya faru, hakan ya dame su sosai. Sai suka je suka gaya wa maigidansu duk abin da ya faru. 32 Sai maigidansa ya kira shi kuma ya ce masa: ‘Kai mugun bawa, na yafe maka duk bashin da nake bin ka saꞌad da ka roƙe ni. 33 Bai kamata ka ji tausayin abokin aikinka kamar yadda na ji tausayin ka ba?’ 34 Don haka, maigidan ya yi fushi sosai, sai ya ce wa masu tsaron kurkukun su saka shi a cikin kurkuku, har sai ya biya bashin da ya ci. 35 Haka nan ma, Ubana wanda yake cikin sama zai yi wa kowannenku da ya ƙi ya yafe wa ɗanꞌuwansa da zuciya ɗaya.”