Ta Hannun Markus
8 A kwanakin, jamaꞌa sun sake taruwa amma ba su da abin da za su ci. Sai Yesu ya kira almajiransa kuma ya ce musu: 2 “Ina jin tausayin jamaꞌar nan, domin sun riga sun yi kwana uku tare da ni kuma ba su da abin da za su ci. 3 Idan na sallame su su tafi gidajensu da yunwa,* za su iya suma a hanya, domin wasunsu sun fito ne daga nesa.” 4 Amma almajiransa sun amsa masa sun ce: “A ina ne mutum zai samu isasshen burodi da zai ciyar da jamaꞌar nan a wannan wurin da babu kowa?” 5 Sai Yesu ya ce musu: “Burodi guda nawa ne kuke da su?” Suka ce masa: “Burodi guda bakwai.” 6 Sai ya gaya wa jamaꞌar su zauna a ƙasa, kuma ya ɗauki burodi bakwai ɗin, ya yi godiya, ya kakkarya, sai ya soma ba wa almajiransa, su kuma suka rarraba wa jamaꞌar. 7 Kuma suna da ƙananan kifaye kaɗan, sai Yesu ya yi godiya a kan kifayen kuma ya gaya ma almajiransa su rarraba su. 8 Sai dukansu suka ci, suka ƙoshi. Almajiran kuwa suka tattara abincin da ya rage, kuma ya cika manyan kwanduna bakwai. 9 Waɗanda suka ci abincin sun kai maza wajen dubu huɗu. Sai Yesu ya sallame su.
10 Nan da nan sai ya shiga cikin jirgin ruwa tare da almajiransa kuma suka shiga yankin Dalmanuta. 11 Sai Farisiyawa suka zo wurinsa, suka soma gardama da shi domin su gwada shi, sun ce ya nuna musu alama daga sama. 12 Sai Yesu ya yi baƙin ciki sosai kuma ya ce: “Me ya sa mutanen zamanin nan suke so a nuna musu alama? A gaskiya ina gaya muku cewa, ba za a nuna wa mutanen zamanin nan alama ba.” 13 Sai ya bar su, ya sake shiga jirgin ruwa, ya haye zuwa ɗayan gefen tekun.
14 Amma almajiransa sun manta su ɗauki burodi, kuma ba su da kome a cikin jirgin ruwan, sai burodi guda ɗaya kawai. 15 Sai Yesu ya ja musu kunne sosai, ya ce: “Ku buɗe idanunku; kuma ku yi hankali da yistin Farisiyawa da kuma yistin Hirudus.” 16 Sai suka soma magana da juna domin ba su da burodi. 17 Da Yesu ya ji haka, ya ce musu: “Me ya sa kuke gardama da juna don ba ku da burodi? Har yanzu ba ku gane ba? Har ila ba kwa fahimta? 18 ‘Kuna da idanu, ba ku gani ba? Kuna da kunnuwa, ba ku ji ba?’ Ba ku tuna 19 lokacin da na rarraba burodi biyar ga maza dubu biyar ba, kwanduna cike da abincin da ya rage nawa ne kuka tara?” Suka ce masa: “Kwanduna goma sha biyu.” 20 “Saꞌad da na rarraba burodi bakwai ga maza dubu huɗu, kwanduna cike da abincin da ya rage nawa ne kuka tara?” Sai suka ce masa: “Kwanduna bakwai.” 21 Sai ya ce musu: “Har yanzu ba ku gane abin da nake nufi ba?”
22 Sai suka tsaya a Betsaida. Kuma mutane suka kawo masa wani mutum da makaho ne, sai suka roƙe shi ya taɓa mutumin. 23 Sai ya riƙe makahon a hannu, ya jawo shi zuwa bayan ƙauyen. Bayan ya tofa miyau a idanun makahon, sai Yesu ya sa hannu a kan mutumin kuma ya tambaye shi: “Ka ga wani abu?” 24 Sai mutumin ya ɗaga kai ya ce: “Ina ganin mutane, amma suna kamar itatuwa da suke yawo.” 25 Sai ya sake taɓa idanun mutumin, kuma mutumin ya soma gani da kyau. Idanunsa sun buɗu kuma yana iya bambanta abubuwa. 26 Sai Yesu ya sallami mutumin zuwa gida, yana cewa: “Kada ka shiga cikin ƙauyen.”
27 Sai Yesu da almajiransa suka tafi ƙauyukan Kaisariya Filibi. Da suke kan hanya, sai ya soma tambayar almajiransa, yana cewa: “Mutane suna cewa ni wane ne?” 28 Sai suka ce masa: “Wasu sun ce Yohanna Mai Baftisma ne, wasu kuma sun ce Iliya. Har ila, wasu sun ce ɗaya daga cikin annabawa ne.” 29 Sai ya yi musu tambaya cewa: “Ku kuma fa, a ganinku, ni wane ne?” Sai Bitrus ya amsa ya ce masa: “Kai ne Kristi.” 30 Sai Yesu ya ja musu kunne sosai kada su gaya wa kowa wane ne shi. 31 Ƙari ga haka, ya soma gaya musu cewa, Ɗan mutum zai sha wahala sosai kuma dattawa, da manyan firistoci, da marubuta za su ƙi yarda da shi kuma a kashe shi, amma a rana ta uku za a ta da shi. 32 Ya yi maganar nan a fili kuma dukansu sun ji. Sai Bitrus ya ja shi gefe ya soma tsawata masa. 33 Da jin haka, Yesu ya juya ya kalli almajiransa, ya soma tsawata wa Bitrus, yana cewa: “Ka rabu da ni Shaiɗan! domin kana tunani kamar mutum ne ba kamar Allah ba.”
34 Sai Yesu ya kira jamaꞌar tare da almajiransa kuma ya ce musu: “Duk wanda yake so ya bi ni, sai ya ƙi kansa, kuma ya ɗauki gungumen azabarsa* ya ci-gaba da bi na. 35 Domin duk wanda yake so ya ceci ransa zai rasa shi. Amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni da kuma labari mai daɗi, zai ceci ransa. 36 A gaskiya, mece ce ribar mutum in ya sami dukan duniyar nan amma ya rasa ransa? 37 Kuma, mene ne mutum zai bayar a maimakon ransa? 38 Duk wanda ya ji kunya saboda ni da maganata a zamanin nan da ke cike da zunubi da kuma rashin aminci, Ɗan mutum ma zai ji kunyar sa saꞌad da ya zo a cikin ɗaukakar Ubansa tare da malaꞌiku masu tsarki.”