Ta Hannun Markus
9 Ƙari ga haka, ya ce musu: “A gaskiya ina gaya muku, akwai wasu da suke tsaye a nan da ba za su taɓa mutuwa ba har sai sun ga Mulkin Allah ya zo da iko.” 2 Bayan kwana shida, Yesu ya ɗauki Bitrus da Yaƙub da Yohanna, ya kai su wani tudu mai tsawo inda suka kasance su kaɗai. Kuma kamannin Yesu ya canja a gabansu. 3 Sai mayafinsa ya soma ƙyalli, kuma ya yi fari fat, yadda babu wani mai wanke riguna a duniya da zai iya sa su yi fari kamar haka. 4 Ƙari ga haka, Iliya da Musa sun fito, kuma suna magana da Yesu. 5 Sai Bitrus ya ce wa Yesu: “Malam,* yana da kyau da muka zo nan. Bari mu kafa tentuna* uku a nan, ɗaya domin ka, ɗaya na Musa, ɗaya kuma na Iliya.” 6 Ya ma rasa abin da zai faɗa, domin tsoro ya kama su sosai. 7 Sai gajimare ya haɗu kuma ya rufe su, sai wata murya daga cikin gajimaren ta ce: “Wannan shi ne Ɗana, wanda nake ƙauna. Ku saurare shi.” 8 Sai nan da nan suka dudduba amma ba su ga kowa ba, sai Yesu shi kaɗai.
9 Da suke saukowa daga kan tudun, sai Yesu ya ja musu kunne kada su gaya wa kowa abin da suka gani har sai Ɗan mutum ya tashi daga mutuwa. 10 Sun riƙe maganar a zuciya,* amma suna ta tattauna a tsakaninsu abin da tashi daga mutuwar yake nufi. 11 Kuma suka fara masa tambaya cewa: “To, don me marubuta suka ce Iliya ne zai fara zuwa?” 12 Sai ya amsa musu ya ce: “Iliya ya riga ya zo, kuma ya mai da abubuwa yadda suke a dā. Amma me ya sa aka rubuta cewa Ɗan mutum zai sha wahala sosai, kuma za a rena shi? 13 Ina gaya muku cewa Iliya ya riga ya zo, har suka yi masa abin da suka ga dama, kamar yadda aka rubuta game da shi.”
14 Da suka zo suka sami sauran almajiran, sai suka ga cewa jamaꞌa sun kewaye su kuma akwai marubuta da ke gardama da su. 15 Amma saꞌad da dukan jamaꞌar suka gan shi, sai suka yi mamaki sosai, kuma suka yi gudu don su je su gaishe shi. 16 Sai ya tambaye su: “A kan me kuke gardama da su?” 17 Sai wani daga cikin jamaꞌar ya ce: “Malam, na kawo maka ɗana, domin yana da ruhu mai ƙazanta da ke hana shi yin magana. 18 A duk lokacin da ruhun ya tashi, yakan jefar da shi a ƙasa, yakan sa shi ya yi ta fitar da kumfa a bakinsa, ya yi ta cizon haƙoransa, har ya rasa ƙarfinsa. Na gaya wa almajiranka su fitar da ruhun, amma sun kasa yin haka.” 19 Sai Yesu ya ce musu: “Ku mutanen zamanin nan marasa bangaskiya, har yaushe zan ci-gaba da kasancewa tare da ku? Har yaushe zan ci-gaba da yin haƙuri da ku? Ku kawo mini shi.” 20 Sai suka kawo masa yaron, da ruhun ya ga Yesu, sai nan da nan ya jefa yaron ƙasa, sai yaron ya soma farfaɗiya. Bayan da yaron ya faɗi a ƙasa, sai ya soma birgima, kuma kumfa yana fita daga bakinsa. 21 Sai Yesu ya tambayi baban yaron: “Tun yaushe ne abin nan ya soma faruwa da shi?” Sai ya ce: “Tun yana ƙarami, 22 kuma yakan jefa shi cikin wuta da kuma ruwa don ya kashe shi. Amma idan za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu kuma ka taimaka mana.” 23 Yesu ya ce masa: “Me ya sa ka ce, ‘Idan za ka iya’? Ai, kowane abu mai yiwuwa ne ga wanda ya ba da gaskiya.” 24 Nan da nan baban yaron ya ta da murya ya ce: “Ina da bangaskiya! Ka taimaka mini a inda nake bukatar bangaskiya!”
25 Da Yesu ya ga cewa jamaꞌar suna gudu zuwa wurinsu, sai ya tsawata wa ruhun mai ƙazanta, yana cewa: “Kai ruhu da ke hana yaron nan jin magana da yin magana, na umurce ka ka fita daga jikinsa kuma kada ka sake shiga!” 26 Bayan ruhun ya sa yaron ya yi kuka, kuma ya yi ta farfaɗiya, sai ya fita. Yaron kuwa ya kwanta kamar gawa, har yawancin mutanen suna cewa: “Ya mutu!” 27 Amma Yesu ya riƙe yaron a hannu kuma ya ɗaga shi, sai yaron ya tashi. 28 Da Yesu ya shiga cikin gida, sai almajiransa suka tambaye shi shi kaɗai, cewa: “Me ya sa ba mu iya fitar da shi ba?” 29 Sai Yesu ya ce musu: “Irin wannan ruhun ba ya fita sai da adduꞌa.”
30 Sai suka bar wurin kuma suka bi ta Galili, amma Yesu ba ya son kowa ya san inda suke. 31 Domin yana koyar da almajiransa kuma yana gaya musu cewa: “Za a ci amanar Ɗan mutum kuma a ba da shi ga mutane, za su ma kashe shi, amma duk da cewa sun kashe shi, bayan kwana uku zai tashi.” 32 Ba su gane abin da yake nufi ba, kuma suna tsoron yi masa tambaya.
33 Sai suka shiga cikin Kafarnahum. Saꞌad da yake cikin gida, sai ya yi musu tambaya cewa: “A kan mene ne kuke gardama a hanya?” 34 Sai suka yi shuru, domin a kan hanya suna gardama da junansu a kan wane ne ya fi girma. 35 Sai ya zauna kuma ya kira almajiransa goma sha biyu, ya ce musu: “Duk wanda yake so ya zama na farko a tsakaninku, dole ya zama na ƙarshe a tsakaninku duka, kuma ya yi wa dukanku hidima.” 36 Sai ya ɗauki wani ƙaramin yaro, ya sa shi ya tsaya a tsakiyarsu; kuma ya sa hannu a kafaɗarsa, ya ce musu: 37 “Duk wanda ya marabci ƙaramin yaro kamar wannan saboda sunana, ya marabce ni; wanda ya marabce ni kuma, ba ni kawai ya marabta ba, amma ya marabci Wanda ya aiko ni ma.”
38 Yohanna ya ce masa: “Malam, mun ga wani yana fitar da aljanu da sunanka, kuma mun yi ƙoƙari mu hana shi domin ba ya bin mu.” 39 Amma Yesu ya ce: “Kada ku yi ƙoƙarin hana shi, babu wanda zai yi ayyukan ban mamaki da sunana, ya kuma yi baƙar magana a kaina nan da nan. 40 Ai duk wanda ba ya gāba da mu, yana tare da mu. 41 Kuma duk wanda ya ba ku kofi ɗaya na ruwa saboda ku na Kristi ne, a gaskiya ina gaya muku, ba zai taɓa rasa ladansa ba. 42 Amma duk wanda ya sa ɗaya daga cikin ƙananan nan da suka ba da gaskiya tuntuɓe, zai fi wa mutumin a rataya a wuyarsa babban dutsen niƙa da jaki yake juyawa kuma a jefa shi a cikin teku.
43 “Idan hannunka yana sa ka tuntuɓe, ka yanke shi ka yar. Zai fi maka ka samu rai na har abada da hannu ɗaya, maimakon ka shiga cikin Gehenna* da hannu biyu, wato cikin wutar da ba za a iya kashe ta ba. 44* —— 45 Kuma idan ƙafanka yana sa ka tuntuɓe, ka yanke shi ka yar. Zai fi maka ka samu rai na har abada da ƙafa ɗaya, maimakon ka shiga cikin Gehenna* da ƙafafu biyu. 46* —— 47 Idan idonka yana sa ka tuntuɓe, ka cire shi ka yar. Zai fi maka ka shiga Mulkin Allah da ido ɗaya, maimakon a jefa ka cikin Gehenna* da idanu biyu, 48 inda tsutsotsi ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashewa ba.
49 “Za a yafa ma kowa wuta kamar yadda ake yafa gishiri a abinci. 50 Gishiri yana da kyau, amma idan gishiri ya rasa ɗanɗanonsa, yaya za a maido da ɗanɗanon? Sai ku kasance da gishiri a cikinku, kuma ku yi zaman lafiya da juna.”