Ta Hannun Yohanna
11 Akwai wani mutum mai suna Liꞌazaru da yake rashin lafiya, shi daga ƙauyen Betani ne, ƙauyen su Maryamu da ꞌyarꞌuwarta Marta. 2 Wannan Maryamu ce ta zuba mān ƙamshi a kan Ubangiji kuma ta share ƙafafunsa da gashin kanta, ɗanꞌuwanta Liꞌazaru ne yake rashin lafiya. 3 Sai ꞌyanꞌuwansa mata suka aika saƙo ga Yesu, suna cewa: “Ubangiji, ga shi, wanda kake ƙauna yana rashin lafiya.” 4 Da Yesu ya ji hakan, sai ya ce: “Ba mutuwa ba ce ƙarshen wannan rashin lafiyar, amma zai sa a ɗaukaka Allah ne, domin a iya girmama Ɗan Allah ta hakan.”
5 Yesu yana ƙaunar Marta da ꞌyarꞌuwarta da kuma Liꞌazaru. 6 Amma saꞌad da ya ji cewa Liꞌazaru yana rashin lafiya, sai ya ƙara yin kwana biyu a inda yake. 7 Bayan haka, sai ya ce wa almajiransa: “Ku zo mu sake komawa cikin Yahudiya.” 8 Sai almajiransa suka ce masa: “Malam, kwana-kwanan nan Yahudawa suka nemi su jejjefe ka, kuma kana so ka sake komawa wurin?” 9 Yesu ya amsa ya ce: “Ba awa goma sha biyu ne yini guda ba? Idan mutum yana tafiya da rana, ba zai yi tuntuɓe ba, domin yana ganin hasken duniyar nan. 10 Amma idan mutum yana tafiya da dare, yakan yi tuntuɓe, domin babu haske a cikinsa.”
11 Bayan da ya faɗi abubuwan nan, sai ya ƙara cewa: “Liꞌazaru abokinmu yana barci, amma zan je wurin in tashe shi.” 12 Sai almajiransa suka ce masa: “Ubangiji, idan yana barci, ai hakan zai taimaka masa ya warke.” 13 Yesu yana nufin cewa Liꞌazaru ya mutu ne. Amma suna tsammanin yana magana ne game da yin barci kawai. 14 Sai Yesu ya gaya musu kai tsaye cewa: “Liꞌazaru ya mutu. 15 Saboda ku ne nake farin ciki cewa ba na wurin, domin ku iya ba da gaskiya. Amma bari mu je wurinsa.” 16 Sai Toma wanda ake kira ꞌYan Biyu, ya ce wa ꞌyanꞌuwansa almajirai: “Mu ma mu tafi, don mu mutu tare da shi.”
17 Saꞌad da Yesu ya isa, sai ya gano cewa Liꞌazaru ya riga ya yi kwanaki huɗu a kabari. 18 Betani yana kusa da Urushalima, wajen kilomita huɗu* ne daga Urushalima. 19 Yahudawa da yawa sun zo su yi wa Marta da Maryamu taꞌaziyya saboda mutuwar ɗanꞌuwansu. 20 Saꞌad da Marta ta ji cewa Yesu yana zuwa, sai ta fita don ta same shi; amma Maryamu ta ci-gaba da zama a gida. 21 Sai Marta ta ce wa Yesu: “Ubangiji, da a ce kana nan, da ɗanꞌuwana bai mutu ba. 22 Duk da haka ko a yanzu ma, na san cewa duk abin da ka roƙi Allah, Allah zai ba ka.” 23 Yesu ya gaya mata cewa: “Ɗanꞌuwanki zai tashi.” 24 Marta ta ce masa: “Na san zai tashi daga mutuwa a ranar ƙarshe.” 25 Yesu ya ce mata: “Ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda yake ba da gaskiya gare ni, ko da ya mutu, zai sake rayuwa. 26 Kuma duk wanda yake raye, yake kuma ba da gaskiya gare ni, ba zai taɓa mutuwa ba. Kin gaskata da wannan?” 27 Sai ta ce masa: “E, Ubangiji, na gaskata cewa kai ne Kristi, Ɗan Allah, wanda aka ce zai zo cikin duniya.” 28 Saꞌad da ta faɗi hakan, sai ta tafi ta kira ꞌyarꞌuwarta Maryamu, kuma ta gaya mata a ɓoye cewa: “Malam yana nan, kuma yana kiran ki.” 29 Saꞌad da Maryamu ta ji hakan, sai ta tashi nan da nan ta je ta same shi.
30 Yesu bai shigo cikin ƙauyen ba tukuna, amma yana wurin da Marta ta same shi. 31 Saꞌad da Yahudawan da suke tare da Maryamu a gida don su yi mata taꞌaziyya suka ga ta tashi nan take kuma ta fita waje, sai suka bi ta, suna tsammanin za ta je kabarin ne don ta yi kuka a wurin. 32 Da Maryamu ta hangi Yesu, ta je inda yake. Sai ta fāɗi a gabansa kuma ta ce masa: “Ubangiji, da a ce kana nan, da ɗanꞌuwana bai mutu ba.” 33 Saꞌad da Yesu ya ga Maryamu da Yahudawan da suke tare da ita suna kuka, ya yi baƙin ciki kuma ya damu sosai. 34 Sai ya ce: “Ina ne kuka binne shi?” Sai suka ce masa: “Ubangiji, ka zo ka gani.” 35 Sai Yesu ya zub da hawaye. 36 Sai Yahudawan suka soma cewa: “Ayya, ku ga irin ƙaunar da yake yi masa!” 37 Amma wasu daga cikinsu sun ce: “Shin wannan mutumin da ya buɗe idanun makahon can, ba zai iya hana mutumin nan mutuwa ba?
38 Bayan da Yesu ya sake yin baƙin ciki, sai ya zo wurin da kabarin yake. Kabarin kuwa, kogon dutse ne, kuma akwai dutse da aka rufe bakin kogon da shi. 39 Sai Yesu ya ce: “Ku ture dutsen.” Sai Marta, ꞌyarꞌuwar wanda ya mutu ta ce masa: “Ubangiji, yanzu gawarsa za ta yi wari, domin kwanansa huɗu ke nan da mutuwa.” 40 Sai Yesu ya ce mata: “Ba na gaya miki cewa idan kin ba da gaskiya, za ki ga ɗaukakar Allah ba?” 41 Sai suka ture dutsen. Sai Yesu ya ɗaga idanunsa sama ya ce: “Ya Uba, na gode maka da ka saurare ni. 42 A gaskiya na san cewa a kullum kana saurara na. Amma na yi maganar nan ne domin jamaꞌa da suke tsaye a nan su ba da gaskiya cewa kai ne ka aiko ni.” 43 Saꞌad da ya gama faɗin abubuwan nan, sai ya ɗaga murya ya ce: “Liꞌazaru, ka fito!” 44 Sai mutumin da ya mutu ya fito, an nannaɗe ƙafafunsa da hannayensa da yadi, kuma an naɗe fuskarsa da yadi. Sai Yesu ya ce musu: “Ku kunce shi ya tafi.”
45 Saboda haka, Yahudawa da yawa da suka zo wurin Maryamu kuma suka ga abin da Yesu ya yi, sun ba da gaskiya gare shi. 46 Amma sai wasu daga cikinsu suka tafi wurin Farisiyawa kuma suka gaya musu abin da Yesu ya yi. 47 Sai manyan firistoci da kuma Farisiyawa suka tara dukan membobin Sanhedrin* kuma suka ce musu: “Mene ne za mu yi, domin mutumin nan yana yin ayyukan ban mamaki da yawa? 48 Idan muka bar shi ya ci-gaba da yin waɗannan abubuwan, duk za su ba da gaskiya gare shi, kuma Romawa za su zo su ƙwace wurinmu* da kuma ƙasarmu.” 49 Sai ɗaya daga cikinsu, mai suna Kayafas, wanda shi ne shugaban firistoci a shekarar, ya ce musu: “Ku dai ba ku san kome ba, 50 kuma ba ku yi tunanin cewa za ku amfana idan mutum ɗaya ya mutu saboda mutane, maimakon a hallaka alꞌumma duka ba.” 51 Bai faɗi wannan da tunanin kansa ba, amma domin shi ne shugaban firistoci a shekarar, ya yi annabci cewa Yesu zai mutu domin alꞌummar. 52 Kuma ba domin alꞌummar kawai ba, amma domin ya tara ꞌyaꞌyan Allah da suka warwatse a wurare dabam-dabam su zama ɗaya. 53 Daga ranar sun ƙulla cewa za su kashe Yesu.
54 Saboda haka, Yesu ya daina tafiya a fili a wurin da Yahudawa suke, amma ya bar wurin ya tafi wani yanki da ke kusa da daji, wato wani gari da ake kira Ifraimu. Kuma ya zauna a wurin tare da almajiransa. 55 Da Bikin Ƙetarewa na Yahudawa ya yi kusa, mutane da yawa daga ƙauyuka suka haura zuwa Urushalima kafin Bikin Ƙetarewan domin su tsabtace kansu bisa doka. 56 Sai suka yi ta neman Yesu. Kuma yayin da suke tsaye a wurare dabam-dabam a haikalin, suna ta ce wa juna: “Mene ne raꞌayinku? Ba zai zo bikin ba ne?” 57 Amma manyan firistoci da Farisiyawa sun ba da umurni cewa, idan wani ya san inda Yesu yake, ya zo ya faɗa musu domin su kama shi.