Ta Hannun Yohanna
2 A rana ta uku, an yi bikin aure a Kana da ke Galili, kuma mamar Yesu tana wurin. 2 An gayyaci Yesu da almajiransa ma zuwa bikin.
3 Da ruwan inabi ya ƙare, sai mamar Yesu ta gaya masa cewa: “Ruwan inabinsu ya ƙare.” 4 Amma Yesu ya ce mata: “Ina ruwanmu da wannan batun? Lokacina bai yi ba tukuna.” 5 Sai mamarsa ta gaya wa masu hidimar cewa: “Ku yi duk abin da ya gaya muku ku yi.” 6 Akwai randuna shida da aka yi da duwatsu a wurin, bisa ga alꞌadar tsabtacewa na Yahudawa. Kowace randa tana iya ɗaukan litan ruwa wajen arbaꞌin da huɗu ko kuma sittin da shida. 7 Sai Yesu ya ce musu: “Ku cika randunan da ruwa.” Sai suka cika randunan har baki. 8 Sai ya ce musu: “Ku ɗiba daga ciki kuma ku kai wa uban bikin.” Sai suka ɗiba. 9 Saꞌad da uban bikin ya sha ruwan da aka juya zuwa ruwan inabi, kuma bai san daga ina ne aka samo shi ba, (ko da yake masu hidimar da suka ɗebo ruwan sun sani), sai uban bikin ya kira angon 10 kuma ya ce masa: “Ai kowa yakan fara ba da ruwan inabi mai kyau tukuna, kuma idan mutane sun bugu, sai ya fito da ruwan inabi marar kyau. Amma kai ka ajiye ruwan inabi mai kyau sai yanzu.” 11 Yesu ya yi wannan a Kana da ke Galili. Kuma wannan ne abin ban mamaki na farko da ya yi. Ya sa mutane sun ga ɗaukakarsa, kuma almajiransa sun ba da gaskiya gare shi.
12 Bayan haka, sai shi da mamarsa, da ꞌyanꞌuwansa, da almajiransa suka gangara zuwa Kafarnahum, amma ba su daɗe a wurin ba.
13 Saꞌad da Bikin Ƙetarewa na Yahudawa ya yi kusa, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima. 14 Saꞌad da ya shiga haikalin, ya ga masu sayar da shanu, da tumaki, da kurciyoyi, da kuma masu canja kuɗi suna zaune a kujerunsu. 15 Bayan da ya yi bulala da igiya, sai ya kori dukan masu tumaki, da masu shanu daga haikalin. Sai ya tutture teburan masu canja kuɗi, kuma ya zubar da dukan kuɗaɗensu. 16 Sai ya ce wa masu sayar da kurciyoyin: “Ku fitar da waɗannan abubuwa daga nan. Ku daina mayar da gidan Ubana kasuwa!” 17 Sai almajiransa suka tuna abin da aka rubuta cewa: “Ƙaunar da nake yi wa gidanka, tana ƙuna na kamar wuta.”
18 Da suka ga haka, sai Yahudawa suka amsa suka ce masa: “Wace alama ce za ka nuna mana, tun da yake kana yin abubuwan nan?” 19 Sai Yesu ya ce musu: “Ku rusa wannan haikalin, kuma a cikin kwana uku zan gina shi.” 20 Sai Yahudawan suka ce masa: “An yi shekaru arbaꞌin da shida kafin a gama gina haikalin nan, shi ne za ka gina a cikin kwana uku?” 21 Amma yana nufin jikinsa ne saꞌad da ya ce haikali. 22 Saꞌad da aka ta da Yesu daga mutuwa ne almajiransa suka tuna cewa ya saba faɗan hakan. Sai suka gaskata da nassosi da kuma abin da Yesu ya gaya musu.
23 Saꞌad da Yesu yake Urushalima domin Bikin Ƙetarewa, mutane da yawa sun ba da gaskiya ga sunansa, domin alamun ban mamaki da suka ga yana yi. 24 Amma Yesu bai yarda da su ba domin ya san dukansu, 25 kuma ba ya bukatar wani ya ba shi shaida game da mutum, domin ya san abin da ke cikin zuciyar mutum.