Ta Hannun Yohanna
5 Bayan wannan, sai Yesu ya haura Urushalima don ya halarci wani bikin Yahudawa. 2 A Ƙofar Tumaki da ke Urushalima, akwai wani tafki da a Ibrananci ake kira Betzata, tafkin na da rumfuna biyar. 3 A cikin rumfunan, akwai mutane da yawa marasa lafiya, da makafi, da guragu, da kuma waɗanda hannayensu da ƙafafunsu sun shanye, suna kwance. 4* —— 5 Amma akwai wani mutum a wurin da ya yi shekaru talatin da takwas yana rashin lafiya. 6 Da Yesu ya ga mutumin yana kwance a wurin, kuma ya san cewa mutumin ya daɗe yana rashin lafiya, sai ya ce masa: “Kana so ka warke?” 7 Mutumin ya amsa masa ya ce: “Maigirma, ba ni da wanda zai sa ni cikin tafkin saꞌad da ruwan ya motsa, kuma idan na yi ƙoƙarin shiga, sai wani ya riga ni.” 8 Sai Yesu ya ce masa: “Ka tashi! Ka ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.” 9 Nan da nan mutumin ya warke kuma ya ɗauki tabarmarsa ya soma tafiya.
Hakan ya faru ne a Ranar Assabaci. 10 Sai Yahudawa suka soma gaya wa mutumin da aka warkar cewa: “Yau Ranar Assabaci ne, kuma bai kamata ka ɗauki tabarma ba.” 11 Amma ya amsa musu ya ce: “Mutumin da ya warkar da ni ne ya ce, ‘Ka ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.’” 12 Sai suka tambaye shi suka ce: “Wane ne mutumin da ya ce maka, ‘Ka ɗauki tabarmarka ka yi tafiya’?” 13 Amma mutumin da aka warkar bai san wanda ya warkar da shi ba, domin Yesu ya shiga cikin taron jamaꞌa da ke wurin.
14 Bayan haka, sai Yesu ya sami mutumin a cikin haikali kuma ya ce masa: “Ga shi, ka warke. Kada ka sake yin zunubi domin kada wani abin da ya fi wannan muni ya same ka.” 15 Sai mutumin ya tafi kuma ya gaya wa Yahudawan cewa Yesu ne ya warkar da shi. 16 Saboda haka, Yahudawan suka tayar ma Yesu da rigima,* domin yana yin abubuwan nan ne a Ranar Assabaci. 17 Amma Yesu ya amsa musu ya ce: “Ubana yana kan yin aiki har yanzu, kuma ni ma ina kan yin aiki.” 18 Hakan ne ya sa Yahudawan sun ƙara neman su kashe shi, domin ban da taka dokar Assabaci, yana kiran Allah Ubansa, ta hakan yana mai da kansa daidai da Allah.
19 Don haka, Yesu ya amsa ya ce musu: “A gaskiya ina gaya muku, Ɗan ba zai taɓa yin ko abu ɗaya yadda ya ga dama ba, amma sai abin da ya ga Uban yake yi. Domin duk abubuwan da Uban yake yi, abubuwan ne Ɗan yake yi. 20 Domin Uban yana ƙaunar Ɗan kuma yana nuna masa dukan abubuwan da yake yi, zai kuma nuna masa ayyukan da suka fi waɗannan domin ku yi mamaki. 21 Kamar yadda Uban yake ta da matattu kuma yake sa su rayu, haka ma Ɗan yake ba da rai ga duk wanda ya ga dama. 22 Gama Uban ba ya yi wa kowa shariꞌa, amma ya ba wa Ɗan ikon yin dukan shariꞌa, 23 domin dukan mutane su daraja Ɗan kamar yadda suke daraja Uban. Duk wanda bai daraja Ɗan ba, ba ya daraja Uban wanda ya aiko shi. 24 A gaskiya ina gaya muku, duk wanda ya ji kalmomina kuma ya gaskata da Wanda ya aiko ni yana da rai na har abada, kuma ba za a yi masa shariꞌa ba, amma ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai.
25 “A gaskiya ina gaya muku, lokaci yana zuwa, ya ma riga ya zo, da matattu za su ji muryar Ɗan Allah, kuma waɗanda suka saurara za su rayu. 26 Kamar yadda Uban yake da rai a cikinsa,* haka ma ya sa Ɗan ya kasance da rai a cikinsa. 27 Kuma ya ba shi ikon yin shariꞌa, domin shi ne Ɗan mutum. 28 Kada ku yi mamakin wannan, domin lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura* za su ji muryarsa 29 kuma su fito, waɗanda suka yi abubuwa masu kyau za su tashi kuma su rayu, amma waɗanda suka yi abubuwa marasa kyau za su tashi kuma a yi musu shariꞌa. 30 Ba zan iya yin ko abu ɗaya yadda na ga dama ba. Yadda Uban ya gaya mini ne nake yin shariꞌa, ina yin shariꞌar adalci domin ba nufin kaina nake yi ba, amma nufin wanda ya aiko ni ne.
31 “Idan ni kaɗai ne nake ba da shaida a kaina, shaidata ba gaskiya ba ce. 32 Akwai wani da ke ba da shaida game da ni, kuma na san cewa shaidar da yake bayarwa game da ni gaskiya ce. 33 Kun aiki mutane zuwa wurin Yohanna kuma ya gaya muku gaskiya. 34 Ko da yake ba na bukatar shaida daga wurin mutum, amma na faɗi abubuwan nan ne domin ku iya tsira. 35 Mutumin nan fitila ne mai ci da kuma haske, kuma kun yarda ku yi farin ciki a cikin haskensa. 36 Amma ina da shaida da ta fi abin da Yohanna ya faɗa, domin ayyukan da nake yi su ne Ubana ya ba ni in yi, kuma ayyukan suna ba da shaida cewa Uban ne ya aiko ni. 37 Uban kuma wanda ya aiko ni, shi da kansa ya ba da shaida game da ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ba kuma ba ku taɓa ganin yadda yake ba, 38 kuma kalmarsa ba ta cikinku domin ba ku ba da gaskiya ga wanda ya aiko ba.
39 “Kuna bincika Nassosi domin kuna ganin za ku sami rai na har abada ta wurinsu, kuma su ne suke ba da shaida game da ni. 40 Duk da haka, ba kwa so ku zo wurina domin ku sami rai. 41 Ba na karɓan ɗaukaka daga wurin mutane, 42 amma na san cewa ba kwa ƙaunar Allah a zuciyarku. 43 Na zo a cikin sunan Ubana, amma ba ku karɓe ni ba. Idan wani ya zo cikin sunansa, za ku karɓe shi. 44 Ta yaya za ku ba da gaskiya, tun da yake kuna karɓan ɗaukaka daga juna kuma ba kwa neman ɗaukaka da ke fitowa daga wurin Allah makaɗaici? 45 Kada ku yi tsammanin zan kai ƙarar ku wurin Uba; akwai mai kai ƙarar ku, wato Musa, wanda kuke bege a kansa. 46 Da a ce kun ba da gaskiya ga Musa, da kun ba da gaskiya gare ni, domin ya rubuta game da ni. 47 Amma idan ba ku ba da gaskiya ga abubuwan da ya rubuta ba, ta yaya za ku ba da gaskiya ga abubuwan da na faɗa?”