Ta Hannun Yohanna
7 Bayan wannan, Yesu ya yi ta zagayawa a cikin Galili. Ba ya so ya yi hakan a cikin Yahudiya domin Yahudawa suna neman su kashe shi. 2 Amma Bikin Bukkoki* na Yahudawa ya yi kusa. 3 Sai ꞌyanꞌuwansa suka ce masa: “Ka bar nan ka je cikin Yahudiya, domin almajiranka ma su ga ayyukan da kake yi. 4 Ai, duk wanda yake so a san shi ba ya yin abubuwa a ɓoye. Idan kana yin abubuwan nan, ka nuna kanka ga duniya.” 5 Gaskiyar ita ce, ꞌyanꞌuwansa ba su ba da gaskiya a gare shi ba. 6 Sai Yesu ya ce musu: “Lokacina bai yi ba tukuna, amma ku dai koyaushe lokacinku ne. 7 Duniya ba ta da dalili ta tsane ku, amma ta tsane ni, domin na ba da shaida cewa ayyukanta na mugunta ne. 8 Ku je bikin, amma ni ba zan je wannan bikin a yanzu ba, domin lokacina bai gama yi ba.” 9 Bayan da ya gaya musu abubuwan nan, sai ya ci-gaba da zama a Galili.
10 Bayan da ꞌyanꞌuwansa suka tafi bikin, sai shi ma ya tafi bikin, amma a ɓoye ba a fili ba. 11 Sai Yahudawan suka soma neman sa a wurin bikin, suna cewa: “Ina wancan mutumin yake?” 12 Kuma jamaꞌa suna ta magana a tsakaninsu a ɓoye game da shi. Wasu suna cewa: “Shi mutumin kirki ne.” Wasu kuma suna cewa: “Aꞌa. Yana yaudarar mutane.” 13 Amma babu wanda ya yi magana game da shi a fili, domin suna tsoron Yahudawan.
14 Saꞌad da aka yi wajen kwana huɗu ana bikin, sai Yesu ya shiga haikali kuma ya soma koyarwa. 15 Sai Yahudawa suka yi mamaki sosai suna cewa: “Yaya aka yi mutumin nan yake da ilimin Nassosi haka, duk da cewa bai yi karatu a makarantu ba?”* 16 Sai Yesu ya amsa musu ya ce: “Abin da nake koyarwa ba nawa ba ne, amma na wanda ya aiko ni ne. 17 Idan wani yana so ya yi nufin Allah, zai san ko koyarwar daga wurin Allah ne, ko kuma abin da nake faɗa nawa ne. 18 Duk wanda yake faɗan abubuwa na kansa, yana neman ɗaukakar kansa. Amma duk wanda yake ƙoƙarin sa a ɗaukaka wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, kuma babu rashin adalci a cikinsa. 19 Musa ya ba ku Doka, ko ba haka ba? Amma babu ko ɗayanku da yake bin Dokar. Me ya sa kuke neman ku kashe ni?” 20 Sai jamaꞌar suka amsa suka ce: “Kana da aljani. Wane ne yake neman ya kashe ka?” 21 Sai Yesu ya amsa musu ya ce: “Abu ɗaya kawai na yi, amma dukanku kuna mamaki. 22 Saboda wannan ne Musa ya ba ku umurnin yin kaciya, ko da yake ba daga wurin Musa ba ne, amma daga wurin kakanninku ne, kuma kuna yi wa mutum kaciya a Ranar Assabaci. 23 Idan an yi wa mutum kaciya a Ranar Assabaci, don kada a taka Dokar Musa, to me ya sa kuke fushi da ni sosai domin na warkar da mutum a Ranar Assabaci? 24 Ku daina yin shariꞌa bisa ga abin da ido ke gani, amma ku yi shariꞌa bisa ga abin da yake daidai.”
25 Sai wasu mazaunan Urushalima suka soma cewa: “Ba wannan mutumin ne shugabanni suke neman su kashe ba? 26 Ga shi nan kuwa a fili yana koyarwa, amma ba su ce masa kome ba. Ko dai shugabannin sun amince cewa shi ne Kristi? 27 Amma mu mun san inda mutumin nan ya fito. Ai idan Kristi ya zo, babu wanda zai san daga ina ne ya fito.” 28 Saꞌad da Yesu yake koyarwa a haikali, sai ya ɗaga murya ya ce: “Kun san ni kuma kun san inda na fito, kuma ba ni ne na aiko kaina ba, amma Wanda ya aiko ni yana wanzuwa, kuma ba ku san shi ba. 29 Na san shi domin ni wakilinsa ne, kuma shi ne ya aiko ni.” 30 Sai suka soma ƙoƙarin kama shi, amma babu wanda ya iya taɓa shi, domin lokacinsa bai yi ba tukuna. 31 Duk da haka, mutane da yawa sun ba da gaskiya gare shi, kuma suna cewa: “Idan Kristi ya zo, zai yi abubuwan ban mamaki fiye da waɗanda mutumin nan ya yi ne?”
32 Da Farisiyawa suka ji mutane suna faɗin abubuwan nan a tsakaninsu, sai manyan firistoci da Farisiyawan suka aika jamiꞌan tsaro su kama shi. 33 Sai Yesu ya ce: “Zan kasance da ku na ɗan lokaci kafin in koma wurin Wanda ya aiko ni. 34 Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba, kuma inda nake ba za ku iya zuwa ba.” 35 Sai Yahudawan suka soma cewa a tsakaninsu: “Ina mutumin nan yake so ya je da ba za mu iya samun shi ba? Ko dai za shi wurin Yahudawa da suke zama a tsakanin mutanen Girka, kuma ya koyar da mutanen Girkan ne? 36 Mene ne yake nufi saꞌad da ya ce, ‘Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba, kuma inda nake ba za ku iya zuwa ba’?”
37 A ranar ƙarshe, wato babbar rana ta bikin, sai Yesu ya tashi tsaye, kuma ya ta da murya ya ce: “Idan wani yana jin ƙishin ruwa, bari ya zo wurina ya sha. 38 Duk wanda ya ba da gaskiya gare ni, kamar yadda nassi ya faɗa cewa: ‘Rafuffukan ruwa masu ba da rai za su ɓullo daga cikinsa.’” 39 Amma Yesu yana magana ne game da ruhu, wanda masu ba da gaskiya gare shi sun kusan su samu. Domin a lokacin, ba a ba da ruhun ba tukuna, gama ba a ɗaukaka Yesu ba tukuna. 40 Da wasu daga cikin jamaꞌa suka ji hakan, sai suka soma cewa: “A gaskiya wannan ne Annabin.” 41 Wasu na cewa: “Wannan ne Kristin.” Amma wasu kuma na cewa: “Kristi zai zo daga Galili ne? 42 Ba nassi ya ce Kristi zai fito daga zuriyar Dauda da kuma Baitalami, ƙauyen da Dauda ya fito ba?” 43 Sai mutanen suka soma gardama a tsakaninsu game da Yesu. 44 Ko da yake wasu daga cikinsu sun so su kama shi, babu wanda ya iya taɓa shi.
45 Sai jamiꞌan tsaron suka koma wurin manyan firistoci da Farisiyawan. Kuma manyan firistocin da Farisiyawan suka tambayi jamiꞌan tsaron cewa: “Me ya sa ba ku kawo shi nan ba?” 46 Sai jamiꞌan tsaron suka ce: “Babu mutumin da ya taɓa magana kamar sa.” 47 Sai Farisiyawan suka ce: “Ku ma mutumin ya ruɗe ku ne? 48 Akwai ɗaya daga cikin shugabanni ko kuma Farisiyawa da ya ba da gaskiya gare shi ne? 49 Wannan taron jamaꞌa da ba su san Doka* ba, laꞌanannu ne.” 50 Sai Nikodimus, wanda ɗaya ne daga cikinsu, kuma ya taɓa zuwa wurin Yesu, ya ce musu: 51 “A Dokarmu, ba a yi wa mutum shariꞌa sai bayan an ji daga wurinsa, kuma an san abin da ya yi, ko ba haka ba?” 52 Sai suka amsa masa suka ce: “Kai ma daga Galili ne? Ka bincika ka gani, ai babu annabin da zai fito daga Galili.”*