Ta Hannun Luka
14 Wata Ranar Assabaci, Yesu ya je ya ci abinci a gidan wani shugaban Farisiyawa, kuma suka zuba masa ido. 2 Sai ga wani mutum mai ciwon kumburi ya zo gabansa. 3 Sai Yesu ya tambayi waɗanda suka san Doka* sosai da Farisiyawa cewa: “Ya dace ne a warkar da mutum a Ranar Assabaci, ko bai dace ba?” 4 Amma sun yi shuru. Sai Yesu ya riƙe mutumin, ya warkar da shi, kuma ya sallame shi. 5 Sai ya ce musu: “Wane ne a cikinku, wanda idan ɗansa, ko bijiminsa ya faɗi a cikin rijiya a Ranar Assabaci, ba zai cire shi ba?” 6 Sai suka kasa ba shi amsa.
7 Saꞌad da ya ga waɗanda aka gayyata suna zaɓan wurin zama mafi daraja, sai ya ba su wani misali yana cewa: 8 “Idan wani ya gayyace ka zuwa bikin aure, kada ka zauna a wurin zama mafi kyau. Domin mai yiwuwa an gayyaci wani da ya fi ka daraja. 9 In ba haka ba, mutumin da ya gayyaci ku biyun zai zo ya ce maka, ‘Bari mutumin nan ya zauna a wurin da ka zauna.’ Hakan zai sa ka tashi da kunya, ka koma wurin zama marar daraja. 10 Amma idan an gayyace ka, ka je ka zauna a wurin zama marar daraja, domin idan mutumin da ya gayyace ka ya zo, zai ce maka, ‘Abokina, ka zo ka zauna a wurin zama mafi daraja.’ Hakan zai mutunta ka a gaban sauran mutanen da aka gayyace su. 11 Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi, amma duk wanda ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.”
12 Sai ya ce wa mutumin da ya gayyace shi: “Saꞌad da kake so ka gayyaci mutane su zo su ci abincin rana ko abincin yamma da kai, kada ka kira abokanka, ko ꞌyanꞌuwanka, ko danginka, ko kuma maƙwabtanka masu arziki. Don wata rana, su ma za su gayyace ka, ta hakan za su biya ka abin da ka yi musu. 13 Amma idan ka shirya biki, ka gayyaci talakawa, da guragu, da makafi, da kuma wasu naƙassasu. 14 Hakan zai sa ka farin ciki, domin ba su da wani abin da za su biya ka da shi. Gama za a biya ka a lokacin da za a ta da masu adalci daga mutuwa.”
15 Da jin waɗannan abubuwan, sai ɗaya daga cikin mutanen da aka gayyata ya ce: “Mai farin ciki ne wanda yake cin abinci a Mulkin Allah.”
16 Yesu ya ce wa mutumin: “Akwai wani mutum da yake shirya babban biki da za a yi da yamma, kuma ya gayyaci mutane da yawa. 17 Da lokacin bikin ya yi, sai ya aiki bawansa ya je ya gaya ma waɗanda aka gayyata cewa, ‘Ku zo, domin an gama shirya kome.’ 18 Sai dukansu suka fara ba da hujjoji. Na farkon ya ce masa, ‘Na sayi gona, ina bukatar in je in dube ta, ka yi haƙuri, ba zan iya zuwa ba.’ 19 Wani kuma ya ce masa, ‘Na sayi shanun noma guda goma, ina so in je in bincika su da kyau, ka yi haƙuri, ba zan iya zuwa ba.’ 20 Har ila, wani ya ce masa, ‘Kwana-kwanan nan ne na yi aure, don haka ba zan iya zuwa ba.’ 21 Sai bawan ya koma, ya gaya wa maigidansa dukan abubuwan da suka faɗa. Sai maigidan ya yi fushi, kuma ya ce wa bawansa, ‘Maza ka bi tituna da kuma lungu-lungu na birnin, ka kawo talakawa, da guragu, da makafi, da kuma wasu naƙassasu.’ 22 Saꞌad da bawan ya dawo, sai ya ce, ‘Maigida, na yi abin da ka ce in yi, amma har yanzu gidan bai cika ba.’ 23 Sai maigidan ya ce ma bawan, ‘Ka bi manya da ƙananan hanyoyi, ka lallashi mutane su zo, don gidana ya cika. 24 Ina gaya muku, babu ko ɗaya daga cikin mutanen nan da aka fara gayyata da zai ɗanɗana abincin yamma da na shirya.’”
25 Wata rana, mutane da yawa suna tafiya tare da Yesu, sai ya juya ya ce musu: 26 “Duk wanda ya zo wurina kuma bai ƙi babansa, da mamarsa, da matarsa, da yaransa, da ꞌyanꞌuwansa maza da mata, har ma da ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba. 27 Ƙari ga haka, duk wanda bai ɗauki gungumen azabarsa* kuma ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba. 28 Alal misali, wane ne a cikinku da yake so ya gina gidan sama,* da ba zai fara zaunawa ya yi lissafin nawa ne zai kashe, don ya san ko yana da isasshen kuɗin da zai gama aikin ba? 29 In ba haka ba, zai fara amma ya kasa kammala ginin, kuma dukan mutane da suka ga ginin, za su soma yi masa dariyar reni, 30 suna cewa: ‘Mutumin nan ya fara gini, amma ya kasa kammalawa.’ 31 Ko kuma wane sarki ne zai fita ya yi yaƙi da wani sarki, ba tare da ya zauna ya yi shawara ko zai iya amfani da sojoji dubu goma, ya yaƙi abokin gābansa da ke da sojoji dubu ashirin ba? 32 Idan ya ga cewa ba zai iya yin haka ba, tun abokin gābansa yana nesa, zai aika wakilansa su same shi, don su yi sulhu.* 33 Haka ma, ku san cewa idan wani daga cikinku bai bar dukan dukiyarsa ba, ba zai iya zama almajirina ba.
34 “Ba shakka, gishiri yana da kyau. Amma idan gishiri ya rasa ɗanɗanonsa, da mene ne za a maido da ɗanɗanon? 35 Ba shi da wani amfani a gona ko a taki. Sai dai a zubar da shi kawai. Bari mai kunne ya kasa kunne ya ji.”