Ta Hannun Yohanna
1 Tun farko akwai Kalma, Kalman yana tare da Allah, kuma Kalman allah ne.* 2 Shi ne wanda yake tare da Allah tun farko. 3 An yi dukan abubuwa ta wurinsa, kuma babu wani abin da aka yi da ba ta wurinsa ba ne.
Abin da aka yi 4 ta wurinsa shi ne rai, kuma wannan rai shi ne haske ga mutane. 5 Hasken yana haskakawa a cikin duhu, amma duhun bai sha ƙarfinsa ba.
6 Akwai wani mutum da Allah ya aiko a matsayin wakilinsa; sunansa Yohanna. 7 Mutumin nan ya zo a matsayin shaida don ya gaya wa mutane gaskiya game da hasken, domin kowane irin mutane su ba da gaskiya ta wurinsa. 8 Ba shi ba ne hasken, amma an aiko shi ne domin ya ba da shaida game da hasken.
9 Haske na gaske da ke ba wa kowane irin mutum haske ya kusan zuwa duniya. 10 A dā yana cikin duniya, kuma an halicci duniya ta wurinsa ne, amma duniya ba ta san shi ba. 11 Ya zo garinsu, amma mutanensa ba su yarda da shi ba. 12 Duk da haka, dukan waɗanda suka karɓe shi, ya ba su izini su zama ꞌyaꞌyan Allah, domin suna ba da gaskiya ga sunansa. 13 Ba ta wurin jini ko nufin jiki ko kuma nufin mutum ne suka zama ꞌyaꞌyan Allah ba, amma ta wurin nufin Allah ne.
14 Kalman kuwa ya zama mutum kuma ya zauna tare da mu. Mun ga ɗaukakarsa, irin ɗaukakar da ɗa makaɗaici* yake samuwa daga wurin ubansa. Kuma yana cike da alherin Allah da kuma gaskiya. 15 (Yohanna ya ba da shaida game da shi, kuma ya ta da murya ya ce: “Wannan shi ne wanda nake magana game da shi saꞌad da na ce, ‘Wanda yake zuwa a bayana ya sha gabana, domin yana raye kafin ni.’”) 16 Saboda yawan alherinsa, dukanmu muna samun alheri marar ƙarewa. 17 Ta wurin Musa ne aka ba da Doka, amma ta wurin Yesu Kristi ne alheri marar ƙarewa da gaskiya suka zo. 18 Babu wanda ya taɓa ganin Allah, Ɗa makaɗaici wanda yake kama da Allah kuma yake kusa da Uban, shi ne ya bayyana Shi.
19 Wannan ne shaidar da Yohanna ya bayar saꞌad da Yahudawa suka aiki firistoci da Lawiyawa daga Urushalima su tambaye shi cewa: “Wane ne kai?” 20 Sai ya gaya musu gaskiya, bai yi mūsu ba, yana cewa: “Ba ni ba ne Kristi.” 21 Sai suka tambaye shi cewa: “To wane ne kai? Kai Iliya ne?” Sai ya amsa ya ce: “Ba ni ba ne shi.” “Kai annabi ne?” Sai ya amsa musu ya ce: “Aꞌa!” 22 Sai suka ce masa: “Wane ne kai? Ka gaya mana domin mu iya ba da amsa ga waɗanda suka aiko mu. Me za ka ce game da kanka?” 23 Sai ya ce: “Ni ne muryar wani da ke kira a daji yana cewa, ‘Ku sa hanyar Jehobah* ta miƙe,’ kamar yadda annabi Ishaya ya ce.” 24 Farisiyawa ne suka aike mutanen. 25 Sai suka tambaye shi suka ce: “To, me ya sa kake yin baftisma idan kai ba Kristi ba ne ko Iliya ko kuma Annabin?” 26 Sai Yohanna ya amsa musu ya ce: “Ina yin baftisma da ruwa. Amma akwai wani da ke tsakaninku da ba ku san shi ba, 27 wanda yake zuwa a bayana, wanda ko igiyar takalmansa ma ban isa in kunce ba.” 28 Abubuwan nan sun faru a Betani, a ƙetaren Kogin Jodan wurin da Yohanna yake yi wa mutane baftisma.
29 Washegari da ya ga Yesu yana zuwa wurinsa, sai ya ce: “Ku duba, ga Ɗan Ragon Allah wanda ya ɗauke zunubin duniya! 30 Wannan shi ne wanda nake magana game da shi saꞌad da na ce: ‘Wanda yake zuwa a bayana ya sha gabana, domin yana raye kafin ni.’ 31 Ko ni ma a dā ban san shi ba, amma dalilin da ya sa na zo ina yin baftisma da ruwa shi ne domin a bayyana shi ga mutanen Israꞌila.” 32 Yohanna ya kuma ba da shaida yana cewa: “Na ga ruhu yana saukowa daga sama kamar kurciya kuma ya tsaya a kansa. 33 Ko ni ma a dā ban san shi ba, amma Wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa ya ce mini: ‘Duk wanda ka ga ruhun yana saukowa a kansa kuma ya tsaya a kansa, shi ne wanda yake baftisma da ruhu mai tsarki.’ 34 Na ga hakan, kuma na ba da shaida cewa wannan shi ne Ɗan Allah.”
35 Washegari kuma, Yohanna yana tsaye tare da biyu daga cikin almajiransa, 36 sai ya ga Yesu yana wucewa, sai ya ce: “Ku duba, ga Ɗan Ragon Allah!” 37 Saꞌad da almajiransa biyun suka ji ya faɗi hakan, sai suka bi Yesu. 38 Da Yesu ya juya ya ga suna bin shi, sai ya ce musu: “Me kuke nema?” Sai suka ce masa: “Rabbai (wanda idan aka fassara, yana nufin “Malam”), a ina ne kake zama?” 39 Sai ya ce musu: “Ku zo ku gani.” Sai suka je kuma suka ga wurin da yake zama, kuma suka zauna tare da shi a ranar. A lokacin, wajen ƙarfe huɗu na yamma ne.* 40 Ɗaya daga cikin almajirai biyun da suka ji abin da Yohanna ya faɗa kuma suka bi Yesu, shi ne Andarawus, ɗanꞌuwan Siman Bitrus. 41 Ya fara samun ɗanꞌuwansa Siman kuma ya ce masa: “Mun samo Almasihu” (wanda idan aka fassara yana nufin, “Kristi”), 42 sai ya kai shi wurin Yesu. Saꞌad da Yesu ya kalle shi, sai ya ce masa: “Kai ne Siman ɗan Yohanna, za a kira ka Kefas” (wanda aka fassara zuwa “Bitrus”).
43 Washegari, Yesu ya so ya je Galili. Sai ya ga Filibus kuma ya ce masa: “Ka zama mabiyina.” 44 Filibus mutumin Betsaida ne, garin su Andarawus da Bitrus. 45 Filibus ya sami Nataniyel kuma ya ce masa: “Mun sami wanda Musa ya rubuta game da shi a cikin Doka,* kuma annabawa sun rubuta game da shi: Wato Yesu, ɗan Yusufu daga Nazaret.” 46 Amma Nataniyel ya ce masa: “Wani abin kirki zai iya fitowa daga Nazaret ne?” Sai Filibus ya ce masa: “Ka zo ka gani.” 47 Da Yesu ya ga Nataniyel yana zuwa wurinsa, sai ya ce game da shi: “Ku ga mutumin Israꞌila na gaske, wanda babu yaudara a cikinsa.” 48 Sai Nataniyel ya ce masa: “Ta yaya ka san ni?” Sai Yesu ya ce masa: “Kafin Filibus ya kira ka, na gan ka saꞌad da kake ƙarƙashin itacen ɓaure.” 49 Sai Nataniyel ya ce: “Rabbai,* kai ne Ɗan Allah, kai ne Sarkin Israꞌila.” 50 Sai Yesu ya amsa masa ya ce: “Ka gaskata hakan ne domin na gaya maka cewa na gan ka a ƙarƙashin itacen ɓaure? Za ka ga abubuwan da suka fi waɗannan.” 51 Sai Yesu ya ƙara cewa: “A gaskiya ina gaya muku, za ku ga sama ta buɗu kuma malaꞌikun Allah suna hawa da sauka zuwa wurin Ɗan mutum.”