Ayyukan Manzanni
14 Ana nan, sai Bulus da Barnabas suka shiga majamiꞌar Yahudawa a Ikoniya kuma suka yi magana har Yahudawa da mutanen Girka da yawa suka ba da gaskiya. 2 Amma Yahudawa waɗanda suka ƙi ba da gaskiya sun zuga mutanen alꞌummai kuma sun ɓata tsakaninsu da ꞌyanꞌuwa masu bi. 3 Sai Bulus da Barnabas suka ɗauki lokaci suna magana da ƙarfin hali ta wurin ikon Jehobah,* wanda ya ba da shaida ga kalmar alherinsa domin ya yi alamu da ayyukan ban mamaki ta wurinsu. 4 Amma mutanen garin suka rabu kashi biyu; waɗansu suna goyon bayan Yahudawa, waɗansu kuma suna goyon bayan manzannin. 5 Saꞌad da mutanen alꞌummai da Yahudawa tare da shugabanninsu suka yi ƙoƙari su wulaƙanta su kuma su jejjefe su, 6 an gaya musu, sai suka gudu zuwa biranen Likoniya, wato Listira da Darbe da kuma ƙauyukan da suke kewaye da su. 7 A wurin, sun ci-gaba da yin shelar labari mai daɗi.
8 A Listira akwai wani mutum da ke zaune wanda gurgu ne. Haka yake tun aka haife shi kuma bai taɓa tafiya ba. 9 Mutumin nan yana saurarar abin da Bulus yake faɗa. Sai Bulus ya zuba masa ido kuma ya lura cewa mutumin ya ba da gaskiya cewa zai warke, 10 da babbar murya ya ce: “Ka tashi tsaye.” Sai mutumin ya yi tsalle kuma ya soma tafiya. 11 Da jamaꞌa suka ga abin da Bulus ya yi, sai suka yi ihu da yaren Likoniya suna cewa: “Ga shi, alloli sun sauko mana a kamannin mutane!” 12 Sai suka fara kiran Barnabas Zeyus, Bulus kuma sun kira shi Hamis, domin shi ne yake kan gaba a yin magana. 13 Sai firist na Zeyus, wanda haikalinsa yana ƙofar birnin, ya kawo bijimai da furanni zuwa ƙofofin birnin kuma shi da jamaꞌar sun so su miƙa hadayu.
14 Amma, da manzo Barnabas da Bulus suka ji haka, sai suka yayyage rigunansu kuma suka shiga cikin jamaꞌar da gudu suka yi ihu suna cewa: 15 “Me ya sa kuke yin abubuwan nan? Mu ma mutane ne masu kasawa kamar ku. Muna yi muku shelar labari mai daɗi domin ku bar abubuwan nan marasa amfani, ku komo ga Allah mai rai, wanda ya yi sama, da ƙasa, da teku, da kuma dukan abubuwan da ke cikinsu. 16 A zamanin dā, ya bar dukan alꞌummai su riƙa yin abin da suka ga dama, 17 ko da yake ya ba da shaida game da kansa ta wurin alherin da yake yi, yana ba ku ruwan sama kuma yana sa gonakinku su ba da amfani a kan lokaci. Yana ba ku abinci ku ci ku ƙoshi kuma yana cika zukatanku da farin ciki.” 18 Duk da cewa sun faɗi abubuwan nan, da kyar suka hana jamaꞌar miƙa musu hadaya.
19 Amma Yahudawa daga Antakiya da Ikoniya suka zo, suka zuga jamaꞌar, sai jamaꞌar suka jejjefi Bulus da duwatsu kuma suka ja shi zuwa bayan gari, suna tsammanin ya mutu. 20 Da almajiran suka kewaye shi, sai ya tashi ya shiga cikin garin. Washegari, shi da Barnabas suka tafi Darbe. 21 Bayan sun yi shelar labari mai daɗi a garin, kuma suka mai da mutane da yawa almajiran Yesu, sai suka koma Listira, da Ikoniya, da kuma Antakiya. 22 Sun ƙarfafa almajiran Yesu a biranen, kuma sun gaya musu su ci-gaba da tsayawa da ƙarfi a cikin bangaskiya, suna cewa: “Dole ne mu sha azaba sosai kafin mu shiga Mulkin Allah.” 23 Ƙari ga haka, sun naɗa dattawa a kowace ikilisiya, suna adduꞌa da azumi kuma sun miƙa su ga Jehobah* wanda a gare shi ne suka ba da gaskiya.
24 Sai suka bi ta Bisidiya kuma suka isa Famfiliya, 25 bayan da suka yi shelar kalmar a Ferga, sai suka gangara zuwa Attaliya. 26 Daga nan kuma suka shiga jirgin ruwa suka koma Antakiya inda tun dā aka yi musu adduꞌa cewa alherin Allah ya kiyaye su cikin aikin nan da suka gama yanzu.
27 Da suka iso kuma suka tara dukan ikilisiyar, sai suka ba su labarin abubuwa da yawa da Allah ya yi ta wurinsu. Da yadda ya buɗe wa mutanen alꞌummai hanyar samun bangaskiya. 28 Sai sun ɗan daɗe tare da almajiran.