Ta Hannun Luka
17 Sai ya ce wa almajiransa: “Dole ne a samu abubuwan da za su sa mutane tuntuɓe. Amma kaiton mutumin da ya sa wasu tuntuɓe! 2 Zai fi wa mutumin a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, kuma a jefa shi a cikin teku, a kan ya sa ɗaya daga cikin ƙananan nan tuntuɓe. 3 Ku lura da kanku. Idan ɗanꞌuwanka ya yi maka laifi, ka tsawata masa. Kuma idan ya tuba, ka gafarta masa. 4 Ko da ya yi maka laifi sau bakwai a rana, kuma ya dawo wurinka sau bakwai yana ce maka, ‘Na tuba,’ dole ne ka gafarta masa.”
5 Sai manzannin suka ce ma Ubangiji: “Ka ƙara mana bangaskiya.” 6 Sai Ubangiji ya ce musu: “Ko da bangaskiyarku ƙarama ce kamar ƙwayar mastad,* za ku iya ce wa wannan itacen,* ‘Ka tuge kanka daga nan kuma ka shuka kanka a cikin teku!’ kuma zai yi muku biyayya.
7 “Wane ne a cikinku da idan bawansa ya dawo daga yin huɗa a gona, ko kuma daga kiwo, zai ce masa, ‘Ka zo nan, ka zauna ka ci abinci’? 8 A maimakon haka, zai ce masa: ‘Ka canja kaya, ka shirya mini abincin yamma, ka yi mini hidima har sai na ci na sha, bayan haka sai kai ma ka ci ka sha.’ 9 Zai gode wa bawan don ya yi hidimar da ya kamata ya yi ne? Aꞌa. 10 Hakan nan ma, Idan kun yi dukan aikin da aka ba ku, ku ce: ‘Mu bayi ne kawai da ba mu cancanci yabo ba. Abin da muka yi, abu ne da ya kamata mu yi.’”
11 Yayin da yake hanya za shi Urushalima, ya bi ta iyaka da ke tsakanin Samariya da Galili. 12 Yayin da yake shiga wani ƙauye, sai kutare goma suka same shi, kuma sun tsaya daga nesa. 13 Sai suka ɗaga muryoyinsu suna cewa: “Yesu, Malam, ka ji tausayin mu!” 14 Da ya gan su, sai ya ce musu: “Ku je ku nuna kanku ga firistoci.” Yayin da suke tafiya, sai suka warke. 15 Saꞌad da ɗayansu ya ga cewa ya warke, sai ya dawo, yana yabon Allah da babbar murya. 16 Sai ya zo ya durƙusa a gaban Yesu da fuskarsa a ƙasa, yana gode masa. Ƙari ga haka, shi mutumin Samariya ne. 17 Sai Yesu ya amsa ya ce: “Ba mutane goma ne aka warkar ba? To, ina sauran taran? 18 Me ya sa wannan mutum wanda ya fito daga wata ƙasa, shi ne kaɗai ya dawo ya yi godiya ga Allah?” 19 Sai ya ce wa mutumin: “Ka tashi, ka kama hanya; bangaskiyarka ta warkar da kai.”
20 Saꞌad da Farisiyawa suka tambaye shi lokacin da Mulkin Allah zai zo, sai ya amsa ya ce musu: “Saꞌad da Mulkin Allah ya zo, ba kowa ba ne zai sani; 21 mutane ba za su ce, ‘Ga shi nan!’ ko kuma su ce, ‘Ga shi can!’ ba. Domin Mulkin Allah yana tsakaninku.”
22 Sai ya ce wa almajiransa: “Lokaci yana zuwa da za ku yi marmarin ganin ɗaya daga cikin ranakun Ɗan mutum, amma ba za ku gani ba. 23 Kuma mutane za su ce, ‘Ga shi, yana can!’ ko kuma, ‘Ga shi, yana nan!’ Kada ku fita, ko kuma ku bi bayansu. 24 Kamar yadda walƙiya take haskakawa daga wannan gefe na sama, zuwa wancan gefen, haka Ɗan mutum zai kasance a ranarsa. 25 Amma, dole ne ya sha wahala iri-iri tukuna kuma mutanen zamanin nan su ƙi shi. 26 Ƙari ga haka, kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka ne zai faru a kwanakin Ɗan mutum: 27 suna ci, suna sha, maza suna aure, kuma ana aurar da mata, har zuwa ranar da Nuhu ya shiga cikin jirgin, kuma Ambaliyar ta zo ta hallaka dukansu. 28 Kamar yadda ya faru a kwanakin Lutu ma: suna ci, suna sha, suna saya, suna sayarwa, suna shuki, kuma suna gine-gine. 29 Amma a ranar da Lutu ya fita daga Sodom, sai aka zubo wuta da duwatsun wuta daga sama, kuma dukansu suka hallaka. 30 Haka ma zai zama a ranar da Ɗan mutum zai bayyana.
31 “A ranar, kada wanda yake saman gida amma kayansa suna cikin gida ya sauko don ya kwashe su. Haka ma, wanda yake gona, kada ya dawo don ya kwashi abubuwan da ya bari a gida. 32 Ku tuna da matar Lutu. 33 Duk wanda yake so ya ceci ransa, zai rasa shi. Amma duk wanda ya rasa ransa, zai sake samun rai. 34 Ina gaya muku, a daren, mutane biyu za su kwanta a kan gado; za a ɗauki ɗaya a bar ɗayan. 35 Mata biyu za su kasance suna niƙa a dutse ɗaya, za a ɗauki ɗaya a bar ɗayan.” 36* —— 37 Sai suka amsa suka ce masa: “A ina ne, Ubangiji?” Sai ya ce musu: “A duk inda gawa take, a wurin ne gaggafa* suke taruwa.”