Ta Hannun Markus
5 Sai suka ƙetare zuwa ɗayan gefen tekun a yankin mutanen Garasa. 2 Kuma nan da nan bayan Yesu ya sauka daga jirgin ruwan, sai wani mutum da ke da ruhu mai ƙazanta ya fito daga wurin da ake binne mutane,* ya zo ya same shi. 3 Wannan mutumin yana zama a wurin da ake binne mutane. A lokacin, ba mai iya ɗaure shi da kyau, ko ma da sarƙa ne. 4 An sha ɗaure hannayensa da ƙafafunsa da sarƙa, amma yakan tsintsinke su; kuma ba wanda yake da ƙarfin riƙe shi. 5 A kullum kuwa dare da rana, yana ihu a inda ake binne mutane, yana tsattsage jikinsa da duwatsu. 6 Amma da ya hangi Yesu daga nesa, sai ya yi gudu ya je ya durƙusa a gabansa. 7 Sai ya yi ihu ya ce: “Ina ruwanka da ni, Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ka rantse da Allah cewa ba za ka azabtar da ni ba.” 8 Domin Yesu yana ta ce masa: “Ka fita daga jikinsa, kai ruhu mai ƙazanta.” 9 Amma Yesu ya tambaye shi ya ce: “Mene ne sunanka?” Sai ya amsa ya ce: “Sunana Runduna ne, domin muna da yawa.” 10 Sai ya yi ta roƙon Yesu kada ya kori ruhohin daga yankin.
11 A lokacin, akwai garken aladu da suke cin abinci a kan tudu. 12 Sai ruhohin suka roƙe shi cewa: “Ka tura mu cikin aladun nan, domin mu shiga cikinsu.” 13 Kuma ya ba su izinin. Sai ruhohin suka fito, suka shiga jikin aladun, kuma garken aladun suka gangara suka faɗi cikin teku. Su wajen dubu biyu ne, da suka nitse a cikin tekun. 14 Amma masu kiwon aladun suka gudu, suka kuma ba da labarin a cikin gari da kuma ƙauyuka. Sai mutane suka fito don su ga abin da ya faru. 15 Da suka zo wurin Yesu kuma suka ga mutumin da a dā yake da rundunar aljanu yana zaune sanye da riga, kuma yana cikin hankalinsa, sai tsoro ya kama su. 16 Waɗanda abin ya faru a idanunsu sun ba su labarin yadda abin ya faru da mutumin da ke da aljanun da kuma aladun. 17 Sai suka soma roƙon Yesu ya bar yankinsu.
18 Da yake shiga cikin jirgin, sai mutumin da aka fitar da aljanu daga jikinsa ya roƙi Yesu ya bar shi ya bi shi. 19 Amma Yesu bai yarda ba. Sai ya ce masa: “Ka tafi gida wurin ꞌyanꞌuwanka, ka ba su labarin dukan abubuwan da Jehobah* ya yi maka, da jinƙai da ya yi maka.” 20 Sai mutumin ya tafi yankin Dikafolis* ya soma yaɗa dukan abubuwan da Yesu ya yi masa, kuma dukan mutanen suka yi mamaki.
21 Da Yesu ya sake ƙetare zuwa ɗayan gefen tekun, sai jamaꞌa suka taru wurinsa, shi kuma yana bakin tekun. 22 Sai ɗaya daga cikin shugabannin majamiꞌa, mai suna Yayirus, da ganin Yesu, sai ya faɗi a gabansa. 23 Ya yi ta roƙan Yesu, yana cewa: “ꞌYata ƙarama tana rashin lafiya sosai.* Ina roƙonka, ka zo ka taɓa ta domin ta warke kuma ta rayu.” 24 Sai Yesu ya bi shi kuma taron jamaꞌa suka bi Yesu suna ta matsa shi.
25 Akwai wata mata da ta yi shekaru goma sha biyu tana fama da yoyon jini. 26 Ta sha wahala sosai* a hannun likitoci da yawa kuma ta kashe dukan kuɗinta. Maimakon ta samu sauƙi, rashin lafiyar sai daɗa muni yake yi. 27 Da ta ji labarin Yesu, sai ta zo ta bayansa a cikin jamaꞌar, kuma ta taɓa mayafinsa 28 domin ta yi ta faɗa a zuciyarta cewa: “Idan na taɓa mayafinsa kawai, zan warke.” 29 Nan da nan ta daina yoyon jinin, kuma ta ji a jikinta cewa ta warke daga rashin lafiya mai tsananin.
30 Nan da nan Yesu ya gane cewa iko ya fita daga jikinsa, sai ya juya a cikin jamaꞌar kuma ya ce: “Wane ne ya taɓa mayafina?” 31 Almajiransa suka ce masa: “Kana ganin taron jamaꞌa suna matsa ka, kuma ka ce ‘Wane ne ya taɓa ni?’” 32 Amma yana ta jujjuyawa don ya ga wanda ya taɓa shi. 33 Matar ta soma rawar jiki saboda tsoro, don ta san abin da ya faru da ita. Sai ta zo ta faɗi a gabansa kuma ta gaya masa gaskiyar abin da ya faru. 34 Ya ce mata: “ꞌYata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, kuma ki rabu da rashin lafiya mai tsananin.”
35 Yayin da Yesu yake kan magana, sai wasu mutane daga gidan shugaban majamiꞌar suka zo suka ce: “ꞌYarka ta rasu! Me amfanin damun Malamin kuma?” 36 Amma Yesu ya ji abin da suka ce kuma ya gaya wa shugaban majamiꞌar cewa: “Kada ka ji tsoro,* kai dai ka ba da gaskiya.” 37 Bai bar kowa ya bi shi ba, sai dai Bitrus, da Yaƙub, da kuma Yohanna ɗanꞌuwan Yaƙub.
38 Saꞌad da suka shiga gidan shugaban majamiꞌar, sai ya ga ana hayaniya kuma mutane suna kuka da makoki. 39 Da ya shiga gidan, sai ya ce musu: “Me ya sa kuke kuka, da hayaniya haka? Yarinyar ba ta mutu ba, amma tana barci ne.” 40 Da suka ji hakan, sai suka soma yi masa dariyar reni. Bayan da ya fitar da jamaꞌar waje, sai shi da baban yarinyar da mamarta, da kuma waɗanda suke tare da shi suka je inda yarinyar take. 41 Sai ya riƙe hannun yarinyar, kuma ya ce mata: “Talita kumi,” idan aka fassara furucin, yana nufin: “Ƙaramar yarinya, ina ce miki, ki tashi!” 42 Nan da nan yarinyar ta tashi kuma ta soma tafiya. (Shekarunta goma sha biyu ne.) Kuma suka yi farin ciki da mamaki sosai. 43 Amma ya ja musu kunne sosai cewa kada su gaya wa kowa abin da ya faru kuma ya ce a ba ta abinci ta ci.