Ayyukan Manzanni
27 Saꞌad da aka yanke shawara cewa za mu tashi a jirgin ruwa zuwa Italiya, sai aka miƙa Bulus da sauran fursunonin a hannun wani jamiꞌin soja mai suna Juliyus, wanda yake rukunin sojojin Agustus. 2 Muka shiga jirgin ruwa wanda yake shirin tashi daga Adiramitiyum zuwa tashoshin jiragen ruwa da suke bakin teku a yankin Asiya, sai muka kama tafiya; kuma Aristarkus mutumin Makidoniya daga Tasalonika, yana tare da mu. 3 Washegari sai muka tsaya a Sidon, kuma Juliyus ya yi wa Bulus alheri. Ya bar shi ya je ya ga abokansa kuma su kula da shi.
4 Da muka soma tafiya daga can a jirgin ruwa, sai iska ta soma gāba da mu. Saboda haka, mun bi ta tsibirin Saifrus inda iskar ba ta da ƙarfi. 5 Saꞌad da muka wuce tekun da ke gefen Kilikiya da Famfiliya, sai muka tsaya a tashar jirgin ruwa da ke Mira a Likiya. 6 A wurin, jamiʹin sojan ya sami wani jirgin ruwa daga Alekzandiriya da za shi Italiya, sai ya sa mu a jirgin ruwan. 7 Bayan da muka yi kwanaki da yawa muna tafiya a hankali, sai muka iso Kinidus da kyar. Da yake iska ta hana mu ci-gaba, mun zagaya ta bayan Kirit da ke Salmoni. 8 Sai muka ci-gaba da tafiya a gaɓar tekun da kyar, har muka iso wani wuri da ake kira Amintacciyar Mafaka da ke kusa da birnin Lasiya.
9 Da yake an riga an ɓata lokaci da yawa, tafiya ma a cikin teku na da haɗari sosai, kuma Ranar Neman Gafara ma ta riga ta wuce,* sai Bulus ya ba da wata shawara 10 ga mutanen, ya ce: “Ina ganin wannan tafiyar za ta jawo hasara sosai ga jirgin da kayan da ke cikin jirgin, har ma ga rayukanmu.” 11 Amma jamiꞌin sojan ya saurari abin da matuƙin jirgin da mai jirgin suka faɗa maimakon ya saurari Bulus. 12 Da yake bai dace su zauna a tashar jirgin ruwan a lokacin sanyi ba, sai yawancinsu suka ba da shawara cewa su ci-gaba da tafiya daga wurin su ga ko akwai yadda za su iya isa Finiks don su zauna a wurin a lokacin sanyi. Wannan tashar jirgin ruwa ce da ke Kirit da ke fuskantar arewa maso gabas da kuma kudu maso gabas.
13 Da iska ta fara busowa daga kudu kaɗan-kaɗan, sai suka yi tsammanin cewa bukatarsu ta biya, sun jawo ƙugiya da ke riƙe jirgin ruwan kuma suka soma tafiya ta Kirit kusa da bakin teku. 14 Amma bayan ɗan lokaci, sai wata iska mai ƙarfi da ake kira Yuroakwilo* ta soma busawa. 15 Da iskar ta bugo jirgin har ya kasa fuskantar iskar, sai muka bari kawai iskar ta yi ta tura mu. 16 Sai muka iso wani ƙaramin tsibiri da ake kira Kauda inda iskar ta ragu, duk da haka, da kyar ne muka jawo ƙaramin jirgi* da ke bayan babban jirgin. 17 Bayan da suka jawo ƙaramin jirgin zuwa cikin babban, sai suka yi amfani da igiyoyi suka ɗaura shi ta ƙasa, kuma domin suna tsoro kada su maƙale a yashin Sirtis,* sai suka sauke filafilan jirgin domin iska ta yi ta tura jirgin. 18 Saboda ruwan yana hauka kuma yana jijjiga jirgin ruwan sosai, washegari suka fara rage kayayyakin da suke jirgin ruwan. 19 A rana ta uku, da hannayensu suka jefar da kayan aikin jirgin ruwan a cikin teku.
20 Saꞌad da aka yi kwanaki da yawa ba a ga rana ko taurari ba, kuma iska mai ƙarfi sosai ta ci-gaba da buga jirgin ruwan, sai muka soma tunani cewa ba za mu tsira ba. 21 Bayan mutanen sun daɗe ba su ci abinci ba, Bulus ya tashi tsaye a tsakaninsu kuma ya ce: “Da kun bi shawarata cewa kada mu shiga hanya daga Kirit, da haɗari da hasarar nan ba su same ku ba. 22 Amma duk da haka, ina roƙon ku ku yi ƙarfin zuciya, kada ku ji tsoro, domin babu ko ɗayanku da zai rasa ransa, sai dai jirgin ne kawai za mu rasa. 23 Da dare, Allahn da ni nasa ne kuma ina masa hidima mai tsarki, ya aiko malaꞌikansa ya tsaya kusa da ni 24 kuma ya ce: ‘Kada ka ji tsoro Bulus. Dole ka tsaya a gaban Kaisar. Kuma saboda kai, Allah zai ceci dukan waɗanda suke cikin jirgin tare da kai.’ 25 Saboda haka, ku kasance da ƙarfin zuciya, domin na ba da gaskiya ga Allah cewa kome zai faru daidai yadda aka gaya mini. 26 Amma jirgin zai rugurguje kuma ya jefar da mu a gaɓar wani tsibiri.”
27 A dare na goma sha huɗu, iska ta ci-gaba da kaɗa jirgin ruwan a tekun Adiriya. Da tsakar daren, sai masu tuƙa jirgin ruwan suka soma tsammanin cewa sun fara kusa da gaɓar teku. 28 Sai suka gwada zurfin ruwan suka ga ya kai ƙafa wajen ɗari da ashirin,* bayan da suka ɗan yi gaba suka sake gwadawa, suka ga ya kai ƙafa wajen casaꞌin.* 29 Don tsoron kada jirginmu ya yi karo da duwatsu, sai suka saki ƙugiyoyi guda huɗu daga bayan jirgin kuma suka soma fatan gari ya waye. 30 Amma masu tuƙa jirgin ruwan sun yi ƙoƙari su gudu daga jirgin ruwan, sai suka saki ƙaramin jirgin cikin teku, suka yi kamar za su saki ƙugiyar daga sashen gaba na babban jirgin. 31 Sai Bulus ya ce wa jamiꞌin sojan da sojojin: “In mutanen nan ba su tsaya a cikin jirgin nan ba, ba za ku tsira ba.” 32 Sai sojojin suka yanke igiyoyin da suke riƙe da ƙaramin jirgin suka bar shi ya faɗi.
33 Da gari ya kusan wayewa, sai Bulus ya roƙi dukansu su ɗan ci abinci, yana cewa: “Yau kwana goma sha huɗu ke nan da kuke jira, kuna damuwa kuma ba ku ci kome ba. 34 Saboda haka, don lafiyar jikinku, ina roƙon ku ku ɗan ci abinci, gama babu ɗayanku da zai rasa ko gashin kansa guda.” 35 Bayan ya faɗi hakan, sai ya ɗauki burodi, ya yi godiya ga Allah a gaban dukansu, ya kakkarya shi, kuma ya soma ci. 36 Hakan ya ƙarfafa dukansu kuma suka soma cin abinci. 37 Dukanmu a jirgin, mutane ɗari biyu da sabaꞌin da shida ne. 38 Bayan da suka ci suka ƙoshi, sai suka rage nauyin jirgin ta wajen zubar da alkama da ke cikin jirgin zuwa teku.
39 Da gari ya waye, ba su gane ƙasar da suke ba, sai suka ga wani lungu kuma akwai yashi a wurin, sai suka yanke shawara su kai jirgin zuwa wurin idan za su iya. 40 Sai suka yanke ƙugiyoyin kuma suka bar su su faɗi cikin teku, a daidai lokacin kuma suka kunce abubuwan da ake tuƙa jirgin ruwan da su; sai suka ta da filafilan gaban jirgin daidai yadda iska za ta tura shi gaba, sai suka nufi gaɓar tekun. 41 Da suka isa wurin da ruwa biyu suka haɗu, sai suka shiga cikin yashi. Sun yi ƙoƙarin tuƙa jirgin ruwan da wuri don su isa gaɓar, sai gaban jirgin ya maƙale a cikin yashin ya kasa tafiya, kuma ƙarfin raƙuman ruwan suka soma farfashe bayan jirgin. 42 Da sojojin suka ga hakan, sai suka tsai da shawarar kakkashe dukan fursunonin don kada waninsu ya yi iyo kuma ya gudu. 43 Amma jamiꞌin sojan ya yi niyyar ya ceci Bulus kuma ya hana sojojin aikata abin da suke shirin yi. Sai ya umurci waɗanda suka iya iyo su yi tsalle daga jirgin ruwan zuwa cikin teku kuma su yi iyo zuwa gaɓa tukuna, 44 wasu kuma suka biyo baya, wasu a kan katakai, wasu kuma a kan tarkacen jirgin ruwan. Don haka dukansu sun kai bakin teku da rai.