Ta Hannun Luka
16 Saꞌan nan ya ce wa almajiransa: “Akwai wani mai arziki da ke da bawa mai kula da kayansa. An zargi bawan da yin banza da kayan maigidansa. 2 Sai maigidan ya kira bawan ya ce masa, ‘Mene ne nake ji haka game da kai? Ka ba da lissafin aikinka, domin ba za ka iya kula da gidana kuma ba.’ 3 Sai bawan ya ce wa kansa, ‘Mene ne zan yi yanzu da maigidana zai kore ni daga aiki? Ga shi ba ni da ƙarfin yin noma, kuma ina jin kunyar yin bara.* 4 Yawwa! Na san abin da zan yi, don idan aka kore ni daga aiki, mutane za su karɓe ni a gidansu.’ 5 Sai ya kira dukan mutane da maigidansa yake bin su bashi kuma ya ce wa na farkon, ‘Nawa maigidana yake bin ka?’ 6 Sai ya amsa masa ya ce, ‘Jarka* ɗari na mān zaitun.’ Sai bawan ya ce wa mutumin, ‘Ga takardar yarjejeniya da kuka rubuta, ka zauna kuma ka mai da shi hamsin da wuri.’ 7 Bayan haka, sai ya ce ma wani, ‘Kai kuma fa, nawa maigidana yake bin ka?’ Sai mutumin ya ce, ‘Manyan buhuna* ɗari na alkama.’ Sai ya ce wa mutumin, ‘Ga takardar yarjejeniya da kuka rubuta, ka mai da shi tamanin.’ 8 Sai maigidan bawan ya yaba masa domin ya nuna hikima duk da cewa abin da ya yi bai dace ba. Gama ꞌyan zamanin nan sun iya bi da mutanen zamaninsu da hikima fiye da ꞌyaꞌyan haske.
9 “Ƙari ga haka, ina gaya muku: Ku yi amfani da dukiya ta rashin gaskiya* ku samar wa kanku abokai. Domin idan dukiyar ta ƙare, za su karɓe ku zuwa wuraren da mutane za su rayu har abada. 10 Wanda ya isa a amince da shi a ƙaramin abu, za a iya amince da shi a babban abu, kuma mutumin da ke rashin gaskiya a ƙaramin abu, zai yi rashin gaskiya a babban abu. 11 Don haka, idan ba za a iya amince da ku a yadda kuke amfani da dukiya ta rashin gaskiya ba, to, wa zai yarda ya ba ku dukiya ta gaskiya? 12 Kuma idan ba za a iya amince da ku a yadda kuke amfani da dukiyar wani ba, wa zai ba ku naku? 13 Babu bawan da zai iya yi wa shugabanni biyu hidima, sai dai ya so ɗaya ya kuma ƙi ɗayan, ko ya yi wa ɗaya ladabi, ya kuma rena ɗayan. Ba za ku iya zama bayin Allah da kuma Dukiya ba.”
14 A lokacin, Farisiyawa waɗanda masu son kuɗi ne, suna jin dukan abubuwan nan da yake faɗa, sai suka soma yi masa baꞌa. 15 Sai ya ce musu: “Ku ne kuke nuna kanku a gaban mutane cewa ku masu adalci ne, amma Allah ya san zukatanku. Abin da ake gani yana da muhimmanci a gaban mutane, ƙazanta ne a gaban Allah.
16 “Doka* da abubuwan da annabawa suka rubuta suna nan kafin Yohanna ya zo. Tun daga lokacin, an soma shelar Mulkin Allah a matsayin labari mai daɗi, kuma kowane irin mutum yana yin iya ƙoƙarinsa ya shiga. 17 Hakika, zai fi sauƙi sama da ƙasa su shuɗe a kan layi ɗaya na Doka ya kasa cika.
18 “Duk wanda ya kashe aurensa* kuma ya auri wata, ya yi zina. Kuma duk wanda ya auri matar da mijinta ya kashe aurensu,* ya yi zina.
19 “An yi wani mutum mai arziki da ke saka kaya masu tsada,* kuma yana jin daɗin rayuwa kowace rana. 20 Akwai kuma wani maroƙi mai suna Liꞌazaru da akan ajiye a ƙofar gidan mai arzikin, kuma miki ya cika jikinsa 21 yana marmarin ya ci daga burbuɗi da ke faɗowa daga teburin mai arzikin. Hakika, har karnuka ma sukan zo su lashe mikin da ke jikinsa. 22 Da shigewar lokaci, maroƙin ya mutu, kuma malaꞌiku suka ɗauke shi, suka kai shi kusa da* Ibrahim.
“Ƙari ga haka, mai arzikin ma ya mutu kuma aka binne shi. 23 Daga cikin kabarin, ya ɗaga idanunsa saꞌad da yake cikin azaba, kuma daga nesa ya ga Ibrahim da Liꞌazaru kusa da* shi. 24 Sai ya kira ya ce, ‘Baba Ibrahim, ka ji tausayi na, ka aiki Liꞌazaru ya sa yatsarsa a cikin ruwa, ya ɗiga a harshena in ɗan ji sanyi. Ina shan wahala sosai a cikin wannan wuta mai ci sosai.’ 25 Amma Ibrahim ya ce masa, ‘Ɗana, ka tuna fa cewa a lokacin da kake da rai, ka ji daɗin abubuwa masu kyau da yawa, Liꞌazaru kuma ya sha wuya sosai. Amma yanzu yana jin daɗi kuma kai kana shan wahala. 26 Ban da haka ma, akwai ƙaton rami tsakanin mu da kai, don waɗanda suke so su ƙetare daga wurinmu zuwa wurinka ba za su iya ba, kuma waɗanda suke so su ƙetare daga wurinka zuwa wurinmu ba za su iya ba.’ 27 Sai ya ce masa, ‘Idan haka ne, ina roƙonka baba, ka aike shi ya je gidan babana, 28 domin ina da ꞌyanꞌuwa maza guda biyar, ina so ya yi musu gargaɗi sosai don kada su ma su zo wannan wurin azaba.’ 29 Amma Ibrahim ya ce masa, ‘Suna da rubuce-rubucen Musa da na annabawa, su yi abin da suka faɗa.’ 30 Sai ya ce, ‘Aꞌa baba Ibrahim, ba za su yi hakan ba, amma idan wani daga cikin matattu ya je wajensu, za su tuba.’ 31 Amma Ibrahim ya ce masa, ‘Idan ba su bi abin da Musa da annabawa suka rubuta ba, ko da wani ya tashi daga mutuwa, ba zai iya sa su tuba ba.’”