Ta Hannun Matiyu
21 Saꞌad da suka yi kusa da Urushalima kuma suka kai Baitꞌfaji da ke Tudun Zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu, 2 ya ce musu: “Ku shiga cikin ƙauyen nan da kuke gani, da zarar kun shiga, za ku ga wata jaka da aka ɗaure ta tare da ɗanta. Ku kunce su ku kawo mini. 3 Idan wani ya yi muku magana, ku gaya masa cewa, ‘Ubangiji ne yake bukatar su.’ Da jin haka, zai bari ku tafi da su nan da nan.”
4 Hakan ya faru don a cika abin da annabi ya faɗa, cewa: 5 “Ku gaya wa ꞌyar Sihiyona cewa: ‘Ga sarkinki yana zuwa wurinki, shi marar zafin rai ne, yana tafiya a kan jaki, e, a kan ɗan jaki.’”
6 Sai almajiran suka je kuma suka yi daidai abin da Yesu ya gaya musu. 7 Sun kawo jakar tare da ɗanta suka shimfiɗa mayafinsu a kansu, sai Yesu ya zauna a kansu. 8 Yawancin mutanen sun shimfiɗa mayafinsu a kan hanya, wasu kuma suna ta yanka rassan itatuwa suna ta shimfiɗa a kan hanya. 9 Ƙari ga haka, jamaꞌar da ke gabansa da waɗanda suke bin sa suna ta ihu suna cewa: “Ya Allah, muna roƙo, ka ceci Ɗan Dauda! Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Jehobah!* Muna roƙon ka, ka cece shi, Kai da kake cikin sama!”
10 Da ya shiga cikin Urushalima, sai mutanen birnin gabaki-ɗaya suka ruɗe. Suna ta tambaya cewa: “Wane ne wannan?” 11 Sai jamaꞌar suka yi ta cewa: “Wannan shi ne annabi Yesu, da ya fito daga Nazaret na Galili!”
12 Yesu ya shiga cikin haikali, sai ya kori waɗanda suke saya da sayarwa, kuma ya tutture teburan masu canja kuɗi da kujerun masu sayar da kurciyoyi. 13 Kuma ya ce musu: “A rubuce yake cewa, ‘Za a ce da gidana, gidan adduꞌa,’ amma kun mai da shi wurin ɓuyan ɓarayi.” 14 Ban da haka, makafi da guragu sun zo wurinsa a haikalin, kuma ya warkar da su.
15 Saꞌad da manyan firistoci da marubuta suka ga ayyukan ban mamaki da ya yi, da kuma yaran da suke ihu a cikin haikalin suna cewa, “Ya Allah, muna roƙo, ka ceci Ɗan Dauda!” sai suka yi fushi sosai. 16 Sai suka ce masa: “Ka ji abin da waɗannan suke cewa?” Yesu ya ce musu: “E. Ashe ba ku taɓa karantawa ba, cewa, ‘Ka sa bakin yara da jarirai su yabe ka’?” 17 Sai ya bar su a birnin ya tafi Betani ya kwana a wurin.
18 Da yake komawa birnin da sassafe, sai yunwa ta kama shi. 19 Da ya ga wani itacen ɓaure a gefen hanya, sai ya je wurin, amma bai sami kome ba sai ganye, sai ya ce wa itacen: “Kada ka ƙara yin ꞌyaꞌya har abada.” Nan da nan itacen ɓauren ya bushe. 20 Da almajiransa suka ga hakan, sai suka yi mamaki sosai kuma suka ce: “Ya aka yi itacen ɓauren ya bushe nan take?” 21 Sai Yesu ya amsa musu, ya ce: “A gaskiya ina gaya muku, idan kuna da bangaskiya kuma ba ku yi shakka ba, za ku iya yin abin da na yi wa itacen ɓauren nan. Ƙari ga haka, ko da kun ce ma wannan tudun, ‘Ka tashi ka faɗi a cikin teku,’ hakan zai faru. 22 Kuma idan kuna da bangaskiya, duk abin da kuka roƙi Allah a cikin adduꞌa, za ku samu.”
23 Da ya shiga cikin haikalin, sai manyan firistoci da dattawan Yahudawan suka zo suka same shi yana koyarwa, kuma suka ce masa: “Da wane iko kake yin abubuwan nan? Kuma wane ne ya ba ka wannan ikon?” 24 Sai Yesu ya amsa musu ya ce: “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Idan kun ba ni amsa, ni ma zan gaya muku da wane iko nake yin abubuwan nan. 25 Daga ina ne Yohanna ya sami izinin yin baftismar da ya yi? Daga sama ne ko daga wurin mutane?” Sai suka soma magana a tsakaninsu suna cewa: “Idan muka ce masa, ‘Daga sama ne,’ zai ce mana, ‘To me ya sa ba ku yarda da shi ba?’ 26 Amma idan muka ce, ‘Daga wurin mutane ne,’ muna tsoron abin da jamaꞌar za su yi mana, domin dukansu sun ɗauki Yohanna a matsayin annabi.” 27 Sai suka amsa wa Yesu suka ce: “Ba mu sani ba.” Shi kuma ya ce musu: “Ni ma ba zan gaya muku da wane iko nake yin abubuwan nan ba.
28 “Mene ne raꞌayinku game da wannan? Wani mutum yana da yara biyu. Ya je ya sami na farkon ya ce masa, ‘Ɗana, ka je gonar inabi ka yi aiki yau.’ 29 Ɗan ya amsa masa ya ce, ‘Ba zan je ba,’ amma daga baya ya yi da-na-sani kuma ya je. 30 Da ya je wurin ɗansa na biyu, sai ya gaya masa abin da ya gaya wa ɗansa na farko. Sai ɗan ya ce, ‘Zan je baba,’ amma kuma bai je ba. 31 Wanne ne a cikin yaran ya yi abin da babansu yake so?” Sai suka ce: “Na farkon.” Sai Yesu ya ce musu: “A gaskiya ina gaya muku, masu karɓan haraji da karuwai za su riga ku shiga Mulkin Allah. 32 Yohanna ya zo don ya nuna muku hanyar adalci, amma ba ku yarda da shi ba. Amma masu karɓan haraji da karuwai sun yarda da shi, kuma duk da cewa kun ga hakan, ba ku tuba kuma kun yarda da shi ba.
33 “Ga wani misali kuma: Akwai wani mutum mai gona, da ya shuka inabi a gonar. Ya kewaye gonar da katanga, kuma ya tona wurin matse ꞌyaꞌyan inabi a ciki. Ƙari ga haka, ya gina hasumiyar tsaro a ciki. Sai ya sa wasu manoma su kula da shi, shi kuma ya yi tafiya zuwa wata ƙasa. 34 Da lokacin girbi ya yi, sai ya aiki bayinsa zuwa wurin manoman don su karɓa masa amfanin gonar. 35 Sai manoman suka kama bayin, suka yi wa ɗaya dūka, suka kashe ɗaya, kuma suka jefi ɗaya. 36 Sai ya sake aikan wasu bayi fiye da na farkon, amma manoman sun yi musu abin da suka yi wa bayi na farkon. 37 A ƙarshe, sai ya aika ɗansa, yana cewa, ‘Za su daraja ɗana.’ 38 Da manoman suka gan shi, sai suka ce wa juna, ‘Wannan shi ne zai gāji gonar. Ku zo mu kashe shi don gādonsa ya zama namu!’ 39 Sai suka kama shi, suka jefa shi bayan gonar inabin kuma suka kashe shi. 40 Don haka, idan mai gonar ya zo, mene ne zai yi wa manoman?” 41 Sai suka ce masa: “Da yake su mugaye ne, zai hallaka su, kuma zai ba da gonar inabin ga wasu manoma dabam, waɗanda za su ba shi amfanin gonar a lokacin girbi.”
42 Yesu ya gaya musu cewa: “Ba ku taɓa karanta a cikin Nassosi ba cewa, ‘Dutsen da magina suka ƙi, shi ne ya zama dutse* mafi amfani a ginin. Wannan daga wurin Jehobah* ne, abin mamaki kuwa a idanunmu’? 43 Shi ya sa nake gaya muku cewa, za a ɗauke Mulkin Allah daga wurinku, a ba wa alꞌummar da take yin abin da Allah yake so.* 44 Duk wanda ya faɗi a kan dutsen, zai hallaka. Kuma duk wanda dutsen ya faɗi a kansa, dutsen zai murƙushe shi.”
45 Da manyan firistocin suka ji misalan da ya bayar, sun san cewa yana magana game da su ne. 46 Ko da yake sun so su kama shi, sun ji tsoron jamaꞌar domin jamaꞌar sun ɗauke shi a matsayin annabi.