Ta Hannun Luka
24 Amma da sassafe a ranar farko ta mako, matan sun zo kabarin kuma sun kawo kayan ƙamshi da suka shirya. 2 Sun lura cewa an riga an ture dutsen da ya rufe kabarin, 3 kuma da suka shiga, ba su ga gawar Ubangiji Yesu ba. 4 Yayin da suke kan mamaki, sai ga maza biyu suna tsaye kusa da su kuma rigunansu na walƙiya. 5 Sai tsoro ya kama matan kuma suka sunkuyar da kansu ƙasa. Sai maza biyun suka ce musu: “Me ya sa kuke neman mai rai a cikin matattu? 6 Ba ya nan, amma an riga an ta da shi. Ku tuna da abin da ya gaya muku saꞌad da yake Galili, 7 cewa za a ba da Ɗan mutum ga masu zunubi, za su kashe shi a kan gungume, amma a rana ta uku zai tashi.” 8 Sai suka tuna da abin da ya gaya musu. 9 Da suka dawo daga kabarin, sai suka gaya ma almajiransa goma sha ɗaya da sauran mutane waɗannan abubuwa. 10 Matan su ne Maryamu Magdalin, da Jowanna, da Maryamu mamar Yaƙub. Ban da haka, sauran mata da ke tare da su ma suna gaya wa manzannin abubuwan nan. 11 Amma a wurin manzannin, matan suna zancen banza ne kawai, kuma ba su yarda da abin da suka faɗa ba.
12 Amma Bitrus ya gudu ya je kabarin, da ya sunkuya ya leƙa ciki, sai ya ga yadin lilin ne kawai. Sai ya koma yana ta tunanin abin da ya faru.
13 A ranar, biyu daga cikin almajiransa suna tafiya zuwa wani ƙauye da ake kira Imawus, wanda yake wajen kilomita goma sha ɗaya* daga Urushalima, 14 suna tattaunawa da juna a kan duk abubuwan da suka faru.
15 Da suke taɗi da kuma tattauna abubuwan nan, sai Yesu da kansa ya zo ya same su, kuma ya soma tafiya tare da su. 16 Amma ba su gane shi ba. 17 Sai ya ce musu: “Wane batu ne kuke tattaunawa da zafi haka yayin da kuke tafiya?” Sai suka tsaya, kuma ransu a ɓace. 18 Sai ɗaya daga cikinsu mai suna Kiliyobas ya amsa ya ce masa: “Kai baƙo ne kuma kana zama kai kaɗai a Urushalima da ba ka san* abubuwan da suka faru kwana-kwanan nan ba?” 19 Sai ya tambaye su cewa: “Waɗanne abubuwa?” Sai suka ce masa: “Abubuwa game da Yesu mutumin Nazaret, wanda ya nuna cewa shi annabi ne mai iko a furuci da ayyuka a gaban Allah da kuma dukan mutane. 20 Da yadda manyan firistoci da shugabanninmu suka ba da shi don a yanke masa hukuncin kisa, kuma suka rataye shi a kan gungume. 21 Dā ma muna sa rai cewa mutumin nan shi ne wanda zai ꞌyantar da Israꞌila. Ban da haka ma, yau ne kwana uku da abubuwan nan suka faru. 22 Ƙari ga haka, wasu mata a cikinmu sun ba mu mamaki domin sun je kabarinsa da sassafe. 23 Da ba su ga gawarsa ba, sai suka dawo suka gaya mana cewa sun ga abubuwan ban mamaki da kuma malaꞌiku da suka gaya musu cewa yana da rai. 24 Sai wasu da suke tare da mu suka je kabarin, kuma sun ga abubuwa daidai yadda matan suka faɗa, amma ba su gan shi ba.”
25 Sai ya ce musu: “Ya ku marasa wayo da waɗanda ba sa saurin gaskata da abubuwan da annabawa suka faɗa! 26 Ba dole ne Kristi ya sha wahala haka kuma ya shiga cikin ɗaukakarsa ba?” 27 Sai ya bayyana musu dukan abubuwan da Nassosi suka faɗa game da shi, somawa da abubuwan da Musa da dukan annabawa suka faɗa.
28 A ƙarshe, sai suka yi kusa da ƙauyen da za su, sai shi ya yi kamar zai ci-gaba da tafiya. 29 Amma suka roƙe shi ya sauka a ƙauyen, suna cewa: “Ka zauna da mu domin yamma ta yi kuma rana ta kusan faɗuwa.” Da ya ji haka, sai ya bi su cikin gida ya zauna tare da su. 30 Da yake cin abinci tare da su, sai ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya, sai ya soma ba su. 31 Da suka ga haka, sai idanunsu suka buɗe kuma suka gane cewa shi ne, amma sai ya ɓace musu. 32 Sai suka ce wa juna: “Ba abubuwan da yake gaya mana saꞌad da muke kan hanya da yadda yake bayyana mana nassosi sun ratsa zuciyarmu ba?” 33 A wannan lokacin, sai suka tashi suka koma Urushalima kuma suka sami manzanni goma sha ɗaya da waɗanda suke tare da su, 34 kuma manzannin da mutanen suka ce: “Babu shakka an ta da Ubangiji har ma ya bayyana ga Siman!” 35 Saꞌan nan su biyun kuma suka ba da labarin abin da ya faru a hanya da kuma yadda suka gane shi saꞌad da ya kakkarya burodi.
36 Yayin da suke faɗin abubuwan nan sai shi da kansa ya zo ya tsaya a tsakaninsu, kuma ya ce musu: “Salama a gare ku.” 37 Amma domin suna tsoro kuma suna rawar jiki, sai suka yi tsammanin cewa sun ga fatalwa. 38 Sai ya ce musu: “Me ya sa kuka damu, kuma me ya sa kuke shakka a zuciyarku? 39 Ku duba hannayena da ƙafafuna ku gani, ai ni ne da kaina. Ku taɓa ni ku gani domin fatalwa ba ta da nama da ƙashi yadda kuke gani nake da su.” 40 Yayin da ya faɗi hakan, sai ya nuna musu hannayensa da ƙafafunsa. 41 Amma yayin da suke kan shakka domin yawan farin ciki da mamaki, sai ya ce musu: “Kuna da abinci a nan ne?” 42 Sai suka ba shi gasasshen kifi, 43 sai ya karɓa kuma ya ci a gabansu.
44 Sai ya ce musu: “Waɗannan ne abubuwan da na gaya muku saꞌad da nake tare da ku, cewa dukan abubuwan da aka rubuta game da ni a cikin Dokar Musa da abubuwan da annabawa suka rubuta da kuma Zabura, dole ne su cika.” 45 Sai ya taimaka musu sosai su gane maꞌanar Nassosi, 46 kuma ya ce musu: “An rubuta cewa: Kristi zai sha wahala, kuma a rana ta uku zai tashi daga mutuwa, 47 kuma a cikin sunansa, za a yi waꞌazi ga dukan alꞌummai. Za a soma hakan daga Urushalima, cewa su tuba don a gafarta zunubansu. 48 Za ku ba da shaidar abubuwan nan. 49 Ga shi, zan aika muku abin da Ubana ya yi alkawarin sa. Amma ku dai, ku zauna a cikin birnin har sai an ba ku iko daga sama.”
50 Sai ya kai su bayan birnin har zuwa Betani, kuma ya ɗaga hannayensa ya albarkace su. 51 Yayin da yake yi musu albarka, sai Allah ya raba shi da su kuma ya ɗauke shi zuwa sama. 52 Sai suka rusuna masa, suka koma Urushalima suna farin ciki. 53 Kuma a kullum suna cikin haikali suna yabon Allah.