Ta Hannun Markus
6 Ya bar wurin, sai ya shigo yankin da ya yi girma, kuma almajiransa sun bi shi. 2 A Ranar Assabaci, ya soma koyarwa a majamiꞌa kuma yawancin waɗanda suka saurare shi, suka yi mamaki sosai kuma suka ce: “Daga ina ne mutumin nan ya samo abubuwan nan? Me ya sa aka ba shi hikimar nan? Kuma me ya sa aka yi waɗannan ayyukan ban mamaki ta wurinsa? 3 Wannan ba shi ne kafinta, ɗan Maryamu ba? Ba ꞌyanꞌuwansa ne Yaƙub, da Yusufu, da Yahuda, da kuma Siman ba? Kuma ba ꞌyanꞌuwansa mata suna tare da mu ba?” Sai suka ƙi yarda da shi. 4 Amma Yesu ya ce musu: “Ai, annabi ba ya rasa daraja sai dai a yankinsa da cikin danginsa da kuma cikin gidansa.” 5 Saboda haka, Yesu bai iya yin wani aikin ban mamaki a wurin ba, sai dai ya sa hannunsa a kan marasa lafiya kaɗan kuma ya warkar da su. 6 Yesu ya yi mamaki saboda rashin bangaskiyarsu. Sai ya zagaya ƙauyuka yana koyarwa.
7 Yesu ya kira almajiransa goma sha biyu, ya soma aika su bibbiyu, kuma ya ba su iko a kan ruhohi masu ƙazanta. 8 Ya umurce su kada su ɗauki wani abu domin tafiyar, sai sanda. Kada su ɗauki burodi, ko jakar abinci, kuma kada su ɗauki jakar kuɗi, 9 amma su ɗauki takalma kuma kada su sa riguna biyu.* 10 Ƙari ga haka, ya ce musu: “A duk inda kuka shiga wani gida, ku zauna a wurin har sai lokacin da za ku tashi. 11 Kuma a duk wurin da an ƙi karɓan ku, ko an ƙi a saurare ku, yayin da kuke barin wurin, ku kakkaɓe ƙurar da ke ƙafafunku, domin ya zama shaida a gare su.” 12 Sai suka tafi, suna waꞌazi cewa mutane su tuɓa. 13 Sun fitar da aljanu da yawa, sun shafa wa mutane da yawa da ke rashin lafiya māi, kuma sun warkar da su.
14 Sai Sarki Hirudus* ya ji labarin, domin sunan Yesu ya yaɗu sosai kuma mutane suna cewa: “An ta da Yohanna Mai Baftisma daga mutuwa, shi ya sa ake yin ayyukan ban mamakin nan ta wurinsa.” 15 Wasu suna cewa: “Iliya ne.” Har ila wasu sun ce: “Annabi ne kamar ɗaya daga cikin annabawan dā.” 16 Amma saꞌad da Hirudus ya ji hakan, sai ya ce: “Yohanna da na yanke kansa, shi ne wanda aka ta da.” 17 Domin Hirudus da kansa ya aika mutane su kama Yohanna kuma ya saka shi a kurkuku saboda Hirudiya, matar ɗanꞌuwansa Filibus wadda Hirudus ya aura. 18 Domin Yohanna ya sha gaya wa Hirudus cewa: “Bai dace da ka ƙwace matar ɗanꞌuwanka ba.” 19 Saboda haka, Hirudiya ta riƙe Yohanna a zuciya kuma ta so ta kashe shi, amma ba ta samu dama ba. 20 Hirudus yana tsoron Yohanna, domin ya san cewa Yohanna mutum ne mai adalci, mai bauta wa Allah, kuma Hirudus yana kāre shi. A duk lokacin da ya saurari Yohanna, ba ya sanin abin da zai yi da shi, duk da haka ya yi farin cikin ci-gaba da saurarar Yohanna.
21 Amma Hirudiya ta sami zarafi mai kyau a ranar da Hirudus ya shirya liyafa da yamma a ranar tunawa da haihuwarsa, don manyan hakimansa da shugabannin sojoji da kuma sanannun mutane a Galili. 22 Sai ꞌyar Hirudiya ta shigo, ta yi rawa a bikin kuma hakan ya sa Hirudus da waɗanda suke cin abinci tare farin ciki sosai. Sarkin ya ce wa yarinyar: “Ki roƙe ni duk abin da kike so kuma zan ba ki.” 23 Hakika, ya rantse ya ce mata: “Duk abin da kike so zan ba ki, ko da rabin mulkina ne.” 24 Sai ta fita, ta je wurin mamarta, ta ce: “Mene ne zan roƙa?” Sai mamar ta ce: “Kan Yohanna Mai Baftisma.” 25 Sai nan take ta gudu ta je wurin sarkin ta gaya masa abin da take so, ta ce: “Ina so ka ba ni kan Yohanna Mai Baftisma a kan faranti yanzu-yanzu.” 26 Ko da yake sarkin ya yi baƙin ciki sosai, amma saboda rantsuwar da ya riga ya yi, da kuma waɗanda* suke cin abinci tare da shi, ba ya so ya yi watsi da abin da ta roƙa. 27 Nan take, sarkin ya aika mai tsaronsa kuma ya umurce shi ya kawo kan Yohanna. Sai mai tsaron ya je ya yanke kan Yohanna a kurkuku. 28 Sai ya kawo kan Yohanna a kan faranti, ya ba wa yarinyar. Ita kuwa, ta ba wa mamarta. 29 Da almajiran Yohanna suka ji hakan, sai suka zo suka ɗauki gawarsa suka binne.
30 Saꞌad da manzanni goma sha biyun suka dawo, sai suka gaya wa Yesu dukan abubuwan da suka yi da abubuwan da suka koyar. 31 Sai Yesu ya ce musu: “Ku zo mu tafi wurin da ba kowa don ku ɗan huta.” Domin akwai mutane da yawa da ke kai da kawowa, har ba su da lokacin hutawa, ko su ci abinci. 32 Sai suka shiga jirgin ruwa don su tafi wurin da ba kowa. 33 Amma da suke barin wurin, mutane sun gan su, kuma da yawa daga cikinsu sun gane su. Mutane daga dukan garuruwa suka yi ta gudu da ƙafa kuma suka riga su zuwa wurin. 34 Da Yesu ya isa wurin, sai ya ga jamaꞌa da yawa kuma ya ji tausayin su domin suna kama da tumaki da ba su da makiyayi. Sai ya soma koya musu abubuwa da yawa.
35 Da yamma ta yi, sai almajiransa suka zo suka ce masa: “Ba kowa a wurin nan fa, kuma yamma ta riga ta yi. 36 Ka sallami mutanen nan su je yankuna da ƙauyuka da suke kewaye, kuma su saya wa kansu abinci.” 37 Sai Yesu ya ce musu: “Ku ba su abin da za su ci.” Sai suka ce masa: “Kana so mu je mu saya burodi na dinari* ɗari biyu kuma mu ba wa mutanen nan su ci?” 38 Sai ya ce musu: “Burodi nawa ne kuke da su? Ku je ku duba!” Bayan da suka duba, sai suka ce: “Burodi biyar ne da kifi biyu.” 39 Sai ya gaya wa dukan mutanen su zauna rukuni-rukuni a kan ciyawa. 40 Sai suka zauna a rukunoni ɗari-ɗari da hamsin-hamsin. 41 Sai ya ɗauki burodi guda biyar ɗin, da kifi biyun, ya kalli sama kuma ya yi godiya. Sai ya rarraba burodin, ya soma ba wa almajiransa don su ba wa mutanen, kuma ya raba wa dukansu kifi biyun. 42 Sai dukansu suka ci suka ƙoshi. 43 Kuma suka tattara abin da ya rage har ya cika kwanduna goma sha biyu, ban da kifin. 44 Waɗanda suka ci burodin, maza dubu biyar ne.
45 Ba tare da ɓata lokaci ba, sai ya sa almajiransa su shiga jirgin ruwa, su haye zuwa ɗayan gefen tekun a Betsaida, shi kuwa ya tsaya don ya sallami jamaꞌar. 46 Bayan da ya sallami jamaꞌar, sai ya haura kan tudu don ya yi adduꞌa. 47 Da rana ta faɗi, jirgin yana tsakiyar teku, Yesu kuma yana kan tudu shi kaɗai. 48 Amma saꞌad da Yesu ya ga suna fama da tuƙa jirgin ruwan domin iska mai ƙarfi tana busowa tana mai da jirgin baya, da asuba,* sai ya zo wajensu yana takawa a kan tekun; amma ya yi kamar zai wuce su. 49 Da suka gan shi yana tafiya a kan tekun, sai suka ce: “Fatalwa ce!” Kuma suka yi ihu. 50 Domin dukansu sun gan shi kuma suka ji tsoro. Amma nan da nan ya yi musu magana ya ce: “Ku kwantar da hankalinku! Ni ne; kada ku ji tsoro.” 51 Sai ya shiga jirgin ruwan ya same su, kuma iskar ta tsaya. Hakan ya ba su mamaki sosai, 52 don ba su gane darasin da ya kamata su koya daga burodin da ya rarraba musu ta hanyar alꞌajibi ba, kuma har yanzu yana yi musu wuya su fahimci abubuwa a zuciyarsu.
53 Da suka ƙetare tekun, sai suka isa Ganisaret kuma suka ɗaura jirgin ruwan kusa da wurin. 54 Da suka fita daga cikin jirgin ruwan, nan da nan mutane suka gane shi. 55 Sai suka yi gudu suka gaya wa kowa a yankin kuma mutane suka soma kawo masa marasa lafiya a kan tabarma* zuwa duk inda suka ji cewa Yesu yake. 56 A duk ƙauyuka, ko birane, ko yankin da ya shiga, mutane sukan ajiye marasa lafiya a kasuwanni, kuma sukan roƙe shi ya bar su su taɓa ko da bakin mayafinsa ne. Dukan waɗanda suka taɓa kuwa sun warke.