Ayyukan Manzanni
11 Ana nan, sai manzannin da ꞌyanꞌuwa da ke Yahudiya sun ji cewa mutanen alꞌummai ma sun karɓi kalmar Allah. 2 Da Bitrus ya shiga Urushalima, sai waɗanda suke goyon bayan yin kaciya suka soma gardama da shi, 3 suna cewa: “Ka shiga cikin gidan mutanen da ba a yi musu kaciya ba, kuma ka ci abinci tare da su.” 4 Da jin hakan, sai Bitrus ya soma bayyana musu batun dalla-dalla, yana cewa:
5 “Saꞌad da nake birnin Joffa ina adduꞌa, sai na ga wahayi. A cikin wahayin na ga wani abu kamar babban yadin lilin da ake saukar da shi ta gefe huɗu na yadin daga sama, kuma ya sauko daidai inda nake. 6 Da na duba da kyau, sai na ga dabbobi masu ƙafafu huɗu, da dabbobin daji, da dabbobi masu rarrafe, da kuma tsuntsayen sama. 7 Na kuma ji wata murya ta ce mini: ‘Ka tashi Bitrus, ka yanka ka ci!’ 8 Amma na ce: ‘Aꞌa, ya Ubangiji, domin abu mai ƙazanta kuma marar tsabta bai taɓa shiga bakina ba.’ 9 A karo na biyu, muryar daga sama ta amsa mini cewa: ‘Ka daina kiran abin da Allah ya tsabtace, abu mai ƙazanta.’ 10 Hakan ya faru har sau uku, sai aka ɗauke kome zuwa sama. 11 Ƙari ga haka, a daidai wannan lokacin, mutane uku suna tsaye a gidan da muke zama, an aiko su wurina daga Kaisariya. 12 Sai ruhun ya ce mini in bi su, kada in yi shakka ko kaɗan. Waɗannan ꞌyanꞌuwa shida ma sun bi ni, kuma tare muka shiga gidan mutumin.
13 “Ya ba mu labarin yadda ya ga wani malaꞌika yana tsaye a gidansa kuma ya ce masa: ‘Ka aika mutane zuwa Joffa su kira Siman, wanda ake kira Bitrus, 14 kuma zai gaya maka abin da zai sa kai da dukan mutanen gidanka ku sami ceto.’ 15 Da na soma magana, sai ruhu mai tsarki ya sauko a kansu kamar yadda ya sauko a kanmu da farko. 16 Da jin haka, sai na tuna abin da Ubangiji ya sha faɗa cewa: ‘Yohanna ya yi baftisma da ruwa, amma za a yi muku baftisma da ruhu mai tsarki.’ 17 Don haka, idan Allah ya ba su irin kyautar da ya ba mu, mu da muka ba da gaskiya ga Ubangiji Yesu Kristi, to wane ne ni da zan hana Allah?”
18 Da suka ji abubuwan nan, sai suka daina gardama da shi,* kuma sun ɗaukaka Allah, suna cewa: “Ashe, Allah ya buɗe hanya ga mutanen alꞌummai su iya tuba kuma su sami rai.”
19 Waɗanda suka watse saboda tsanantawa da ta taso saboda Istifanus, sun gudu zuwa wurare kamar Finikiya, da Saifrus, da kuma Antakiya. Amma sun yi waꞌazin kalmar Allah ga Yahudawa ne kaɗai. 20 Sai wasu mutane daga cikinsu, daga Saifrus da Sayirin sun zo Antakiya kuma sun soma magana da mutanen da ke yaren Girka, suna yi musu shelar labari mai daɗi na Ubangiji Yesu. 21 Ƙari ga haka, Jehobah* yana tare da su, kuma mutane masu yawa sosai sun ba da gaskiya kuma suka juyo wurin Ubangiji.
22 Labarinsu ya isa ikilisiyar da ke Urushalima, sai ikilisiyar ta aiki Barnabas zuwa can Antakiya. 23 Saꞌad da ya isa wurin kuma ya ga yadda Allah ya nuna musu alherinsa, ya yi murna kuma ya soma ƙarfafa dukansu su ci-gaba da bin Ubangiji da dukan zuciyarsu; 24 domin Barnabas mutumin kirki ne kuma yana cike da ruhu mai tsarki da bangaskiya. Kuma an sami ƙarin mutane masu yawa da suka soma bin Ubangiji. 25 Sai ya tafi Tarsus domin ya nemi Shawulu da kyau. 26 Da ya same shi, sai ya kawo shi Antakiya. Don haka, sun yi shekara ɗaya suna taruwa da ikilisiyar da ke Antakiya kuma sun koyar da mutane da yawa. A Antakiya ne aka soma kiran almajiran Yesu Kiristoci, bisa ga umurnin da Allah ya bayar.
27 A kwanakin, annabawa suka zo Antakiya daga Urushalima. 28 Ɗaya daga cikinsu mai suna Agabus ya tashi kuma ya yi annabci ta wurin ruhu mai tsarki cewa an kusan soma yunwa mai tsanani a dukan duniya. Kuma hakan ya faru da gaske a zamanin Klaudiyus. 29 Sai almajiran suka yanke shawara a kan abin da kowannensu zai iya bayarwa, don su aika agaji* ga ꞌyanꞌuwa da ke zama a Yahudiya; 30 haka kuwa suka yi, sun ba da agajin ga dattawan ta wurin Barnabas da Shawulu.