Ta Hannun Matiyu
23 Sai Yesu ya yi magana da jamaꞌar da kuma almajiransa, yana cewa: 2 “Marubuta da Farisiyawa sun ɗauka cewa su ma suna da irin ikon da Musa yake da shi. 3 Don haka, ku bi kuma ku yi dukan abubuwan da suka gaya muku. Amma kada ku yi abubuwan da suke yi, domin ba sa yin abin da suke koyarwa. 4 Suna ɗaura kaya masu nauyi kuma su sa su a kafaɗar mutane, amma su da kansu ba sa so su taɓa kayan da yatsarsu. 5 Duk abubuwan da suke yi, suna yi ne don mutane su gan su. Suna ƙara girman ƙunshin da ke ɗauke da nassosi* da suke sakawa don kāriya, kuma suna ƙara tsawon bakin rigarsu. 6 Sun cika son wurin zama mafi daraja a biki da kuma kujerun gaba* a majamiꞌu. 7 Suna so mutane su riƙa gaishe su a kasuwanni kuma su kira su Malamai.* 8 Amma ku, kada a kira ku Malamai, domin mutum ɗaya ne Malaminku, dukanku kuwa ꞌyanꞌuwa ne. 9 Ƙari ga haka, kada ku kira wani a duniya ubanku, domin Uba ɗaya kuke da shi, Wanda yake cikin sama. 10 Kada a kira ku shugabanni, domin Shugaba ɗaya ne gare ku, wato Kristi. 11 Amma wanda ya fi girma a tsakaninku, dole ne ya zama mai yi muku hidima. 12 Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi, amma duk wanda ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.
13 “Kaiton ku, marubuta da Farisiyawa, munafukai! domin kun rufe wa mutane ƙofar shiga Mulkin sama; ku kanku ba ku shiga ba, kuma ba ku bar waɗanda suke hanyar shiga su shiga ba. 14* ——
15 “Kaiton ku, marubuta da Farisiyawa, munafukai! domin kukan ƙetare teku kuma ku je koꞌina a busasshiyar ƙasa don ku sa mutum ɗaya ya karɓi Yahudanci kuma bayan hakan, sai ku sa shi ya shiga Gehenna,* kuma zunubinsa zai fi naku har sau biyu.
16 “Kaiton ku, makafi da ke yi ma wasu ja-goranci. Kukan ce, ‘Idan mutum ya yi rantsuwa da haikali, ba wani abu ba ne. Amma idan ya yi rantsuwa da zinariya da ke haikalin, dole ne ya cika alkawarin da ya yi.’ 17 Wawaye da makafi! Wanne ne ya fi girma, zinariya ne ko kuma haikalin da ya tsarkake zinariyar? 18 Kuna kuma cewa, ‘Idan wani ya yi rantsuwa da bagade ba wani abu ba ne. Amma idan ya yi rantsuwa da kyautar da ke kan bagaden, dole ne ya cika alkawarinsa.’ 19 Makafi! Wanne ne ya fi girma, kyautar ne, ko kuma bagaden da ya tsarkake kyautar? 20 Saboda haka, duk wanda ya yi rantsuwa da bagade, ya yi rantsuwa ne da bagaden da duk abubuwan da ke kan bagaden. 21 Kuma duk wanda ya yi rantsuwa da haikali, ya yi rantsuwar ne da haikalin da kuma Allah da ke zama a cikinsa. 22 Ƙari ga haka, duk wanda ya yi rantsuwa da sama, ya yi rantsuwa ne da kursiyin Allah, har ila ya yi rantsuwa da Allah da ke zama a kan kursiyin.
23 “Kaiton ku, marubuta da Farisiyawa, munafukai! domin kuna ba da kashi goma na mint da dill da kuma kumin,* amma kun yi watsi da abubuwan da suka fi muhimmanci a cikin Doka,* wato adalci da jinƙai da kuma aminci. Yana da muhimmanci ku yi abubuwa na farkon, amma ba wai ku yi watsi da sauran abubuwan nan ba. 24 Makafi masu yi ma wasu ja-goranci, kukan tace ƙaramin ƙwaro daga abin da kuke sha, amma ku haɗiye raƙumi.
25 “Kaiton ku, marubuta da Farisiyawa, munafukai! domin kukan wanke bayan kofi da na kwano, amma zuciyarku na cike da haɗama da son bin shaꞌawar jiki. 26 Ku Farisiyawa makafi, ku soma da wanke cikin kofi da kuma kwano, domin bayansu ma ya kasance da tsabta.
27 “Kaiton ku, marubuta da Farisiyawa, munafukai! domin kuna kama da kaburbura da aka shafa musu farin fenti, masu kyaun gani daga waje, amma abubuwan da ke ciki, ƙasusuwan matattu da datti iri-iri ne. 28 Haka ku ma kuke, a waje mutane suna ganin kamar ku masu adalci ne, amma a ciki, kuna cike da munafunci da mugunta.*
29 “Kaiton ku, marubuta da Farisiyawa, munafukai! domin kuna gina kaburburan annabawa, kuma kuna yi wa kaburburan masu adalci ado. 30 Kuma kun ce, ‘Da a ce mun yi rayuwa a zamanin kakanninmu da ba mu sa hannu a kisan annabawa da suka yi ba.’ 31 Ta haka, kuna ba da shaida da bakinku cewa ku ne ꞌyaꞌyan waɗanda suka kashe annabawa. 32 Don haka, ku ƙarasa aikin da kakanninku suka fara.
33 “Ku macizai, ꞌyaꞌyan macizai masu dafi, ta yaya za ku iya kauce ma hukuncin Gehenna?* 34 Saboda haka, ina aika muku annabawa da masu hikima da masu koyar da jamaꞌa. Wasunsu za ku kashe su kuma ku rataye su a kan gungume, wasunsu kuma za ku yi musu bulala a majamiꞌunku kuma ku bi su daga gari zuwa gari kuna tsananta musu, 35 don ku ɗauki alhakin jinin duk masu adalci da aka kashe a duniya, tun daga jinin Habila mai adalci har zuwa na Zakariya ɗan Barakiya, wanda kuka kashe a gaban haikali kusa da bagade. 36 A gaskiya ina gaya muku, dukan abubuwan nan za su faru da zamanin nan.
37 “Urushalima, Urushalima, wadda take kashe annabawa, da jifar waɗanda aka aiko gare ta, sau da yawa na so in tattara yaranki kamar yadda kaza take tattara ꞌyaꞌyanta a cikin fikafikanta, amma kin ƙi. 38 Ga shi! An bar muku gidanku.* 39 Gama ina gaya muku, ba za ku sake ganina ba, har sai kun ce, ‘Mai Albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Jehobah!’”*