Ta Hannun Markus
16 Bayan Ranar Assabaci, Maryamu Magdalin, da Maryamu mamar Yaƙub, da Salomi sun sayo kayan ƙamshi don su shafa wa jikin Yesu. 2 Da sassafe a ranar farko ta mako, da fitowar rana, sai suka zo kabarin. 3 Suna ce wa juna: “Wane ne zai tura mana dutsen da aka rufe kabarin da shi?” 4 Amma da suka ɗaga idanu, sai suka ga cewa an riga an ture dutsen, duk da cewa yana da girma sosai. 5 Da suka shiga kabarin, sai suka ga wani saurayi yana zaune a hannun dama, sanye da farin riga, kuma suka yi mamaki sosai. 6 Sai ya ce musu: “Kada ku yi mamaki. Kuna neman Yesu mutumin Nazaret wanda aka kashe a kan gungume. An tashe shi. Kuma ba ya nan. Ga wurin da suka kwantar da shi dā ma. 7 Ku je ku gaya wa almajiransa da kuma Bitrus cewa, ‘Za shi Galili ya jira ku. Za ku gan shi a wurin, kamar yadda ya riga ya gaya muku.’” 8 Da suka fita daga kabarin, sai suka soma guduwa, suna rawar jiki kuma cike da mamaki. Ba su faɗa ma kowa wani abu ba domin suna jin tsoro.*