Ta Hannun Luka
18 Sai Yesu ya ba su misalin da ya nuna muhimmancin nacewa a yin adduꞌa, 2 yana cewa: “A wani gari, akwai wani alƙali da ba ya jin tsoron Allah, kuma ba ya daraja mutane. 3 Akwai kuma wata mata a garin da mijinta ya mutu, tana ta zuwa wurin alƙalin tana cewa, ‘Don Allah, ka tabbata cewa an yi mini adalci a batun da ke tsakanina da ɗayan mutumin.’ 4 Ko da yake matar ta ɗau lokaci tana ta roƙonsa, ya ƙi ya yarda. Amma daga baya ya ce wa kansa, ‘Duk da cewa ba na tsoron Allah kuma ba na daraja kowane mutum, 5 amma saboda matar nan ta ci-gaba da damu na, zan tabbata cewa ta samu adalci don kada ta ci-gaba da zuwa ta yi ta damu na da bukatarta.’” 6 Sai Ubangiji ya ce: “Kun ga abin da alƙalin ya ce, duk da cewa shi ba mai adalci ba ne! 7 Ba kwa ganin cewa Allah zai yi adalci ga mutanen da ya zaɓa da suke kuka gare shi dare da rana, yayin da yake haƙuri da su ba? 8 Ina gaya muku, zai tabbata cewa an yi musu adalci da sauri. Duk da haka, saꞌad da Ɗan mutum ya iso, zai samu irin bangaskiyar nan a duniya kuwa?”
9 Yesu ya kuma ba da misalin nan ga wasu da suka dogara da adalcinsu, kuma suke ganin wasu mutane ba kome ba ne, ya ce: 10 “Mutane biyu sun je haikali don su yi adduꞌa, ɗaya Bafarisi ne, ɗayan kuma mai karɓan haraji ne. 11 Sai Bafarisin ya tashi, ya soma adduꞌa a zuciyarsa, yana cewa, ‘Ya Allah, na gode maka cewa, ni ba kamar sauran mutane ba, wato masu sata, da marasa adalci, da kuma masu zina, ko ma kamar mai karɓan harajin nan. 12 Nakan yi azumi sau biyu a mako; Nakan ba da kashi goma na dukan abubuwan da nake da su.’ 13 Amma mai karɓan harajin ya tsaya da nisa, bai ko ɗaga idanunsa sama ba, ya ci-gaba da buga ƙirji don ya nuna baƙin cikinsa, yana cewa, ‘Ya Allah, ka tausaya mini, ni mai zunubi ne.’ 14 Ina gaya muku cewa, wannan mai karɓan harajin ya koma gidansa a matsayin mai adalci fiye da Bafarisin. Domin duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi, amma duk wanda ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.”
15 Mutane suna kawo yaransu ƙanana wurin Yesu don ya sa hannunsa a kansu. Da ganin haka, almajiransa suka soma tsawata musu. 16 Amma Yesu ya kira ƙananan yaran zuwa wurinsa, yana cewa: “Ku bar ƙananan yaran su zo wurina kuma kada ku hana su, domin Mulkin Allah na irinsu ne. 17 A gaskiya ina gaya muku, duk wanda bai karɓi Mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga cikinsa ba.”
18 Sai wani mai mulki ya zo ya tambaye shi cewa: “Malam Nagari, me zan yi don in gāji rai na har abada?” 19 Sai Yesu ya ce masa: “Me ya sa ka kira ni nagari? Babu wani nagari, sai Allah kaɗai. 20 Ka san abubuwan da aka faɗa a cikin dokoki: ‘Kada ka yi zina, kada ka yi kisa, kada ka yi sata, kada ka ba da shaidar ƙarya, ka girmama babanka da mamarka.’” 21 Sai mutumin ya ce: “Ai ina yin dukan abubuwan nan tun ina ƙarami.” 22 Da jin haka, sai Yesu ya ce masa, “Akwai abu ɗaya da ya rage maka ka yi: Ka je ka sayar da dukan abubuwan da kake da su, ka ba talakawa kuɗin, za ka samu dukiya a sama; kuma ka zo ka bi ni.” 23 Saꞌad da mutumin ya ji haka, sai ya yi baƙin ciki, domin shi mai arziki ne sosai.
24 Yesu ya kalle shi kuma ya ce: “Zai yi ma waɗanda suke da kuɗi wuya su shiga Mulkin Allah! 25 A gaskiya, zai fi wa raƙumi sauƙi ya bi ta ramin allurar ɗinki da mai arziki ya shiga Mulkin Allah.” 26 Waɗanda suka ji wannan suka ce: “Wa zai iya samun ceto?” 27 Yesu ya ce: “Abubuwan da ba za su yiwu ba ga mutane, a wurin Allah za su yiwu.” 28 Amma Bitrus ya ce masa: “Ga shi, mun bar abubuwan da muke da su kuma mun bi ka.” 29 Sai Yesu ya ce musu: “A gaskiya ina gaya muku, babu wanda ya bar gida, ko mata, ko ꞌyanꞌuwa, ko iyaye, ko kuma yara, saboda Mulkin Allah 30 wanda ba zai sami fiye da hakan a wannan lokacin ba, kuma a zamani mai zuwa,* zai sami rai na har abada.”
31 Sai ya ɗauki almajiransa goma sha biyun, ya kai su gefe, ya ce musu: “Ga shi! Za mu haura zuwa Urushalima, kuma dukan abubuwan da annabawa suka rubuta game da Ɗan mutum za su cika. 32 Alal misali, za su ba da shi ga mutanen alꞌummai, za su yi masa baꞌa, su wulaƙanta shi, kuma su tofa masa miyau. 33 Bayan sun yi masa bulala, za su kashe shi, amma a rana ta uku, zai tashi.” 34 Ba su gane maꞌanar ko ɗaya daga cikin abubuwan nan ba, domin an ɓoye musu maꞌanar kalmomin nan, shi ya sa ba su gane abubuwan da yake faɗa ba.
35 Da Yesu ya yi kusa da Jeriko, sai ga wani makaho yana zaune a bakin hanya yana bara.* 36 Da ya ji mutane da yawa suna wucewa, sai ya soma tambayar abin da yake faruwa. 37 Sai suka gaya masa cewa: “Yesu mutumin Nazaret yana wucewa!” 38 Sai ya ta da murya yana cewa: “Yesu, Ɗan Dauda, ka ji tausayi na!” 39 Waɗanda suke tsaye a gabansa suka soma tsawata masa, suna ce masa ya yi shuru. Amma sai ƙara ɗaga murya yake yi, yana cewa: “Ɗan Dauda, ka ji tausayi na!” 40 Sai Yesu ya tsaya, ya ce a kawo masa mutumin. Bayan da mutumin ya zo kusa, sai Yesu ya tambaye shi cewa: 41 “Me kake so in yi maka?” Sai ya ce: “Ubangiji, ina so in soma gani.” 42 Sai Yesu ya ce masa: “Ka soma gani; bangaskiyarka ta warkar da kai.” 43 Nan da nan mutumin ya soma gani, kuma ya soma bin Yesu, yana yabon Allah. Da mutane suka ga haka, sai dukansu suka yabi Allah.