Ta Hannun Matiyu
19 Bayan da Yesu ya gama faɗan waɗannan abubuwan, sai ya bar Galili kuma ya zo iyakar Yahudiya a ƙetaren Kogin Jodan. 2 Sai taron jamaꞌa suka bi shi, kuma ya warkar da su a wurin.
3 Sai Farisiyawa suka zo suka same shi da niyyar gwada shi, kuma suka tambaye shi cewa: “Ya dace bisa Doka* mutum ya kashe aurensa a kan kowane dalili?” 4 Sai ya amsa musu ya ce: “Ba ku karanta cewa wanda ya halicce su tun daga farko ya halicce su namiji da ta mace ba? 5 Kuma ya ce: ‘Saboda haka, mutum zai bar babansa da mamarsa, ya manne wa matarsa kuma su biyun za su zama jiki ɗaya’ ba? 6 Ta hakan su ba mutum biyu ba kuma, amma mutum ɗaya ne. Don haka, abin da Allah ya haɗa, kada wani ya raba.” 7 Suka ce masa: “To, me ya sa Musa ya ce mutum ya ba wa matarsa takardar kashe aure, saꞌan nan ya sallame ta?” 8 Sai Yesu ya ce musu: “Saboda taurin zuciyarku, shi ya sa Musa ya yarda muku ku kashe aurenku, amma ba haka yake tun daga farko ba. 9 Ina gaya muku cewa, duk wanda ya kashe aurensa, ba tare da matar ta yi lalata* ba kuma ya auri wata ya yi zina.”
10 Almajiransa suka ce masa: “Idan haka yake tsakanin mutum da matarsa, ai, gwamma mutum bai yi aure ba.” 11 Sai Yesu ya ce musu: “Ba kowa ba ne zai iya yin hakan, sai dai wanda yake da baiwar. 12 Domin akwai waɗanda aka haifa da ba za su iya yin aure ba,* akwai waɗanda mutane ne suka mai da su haka, akwai kuma waɗanda suka zaɓa ba za su yi aure ba domin Mulkin sama. Duk wanda zai iya yin hakan, bari ya yi.”
13 Sai mutane suka kawo wa Yesu yara ƙanana don ya sa hannunsa a kansu kuma ya yi musu adduꞌa, amma almajiransa suka tsawata wa mutanen. 14 Sai Yesu ya ce musu: “Ku bar ƙananan yaran su zo wurina kuma kada ku hana su, domin Mulkin sama na irinsu ne.” 15 Sai ya sa hannu a kansu, saꞌan nan ya bar wurin.
16 Sai wani ya zo ya same shi ya ce: “Malam, wane nagarin aiki* ne zan yi don in samu rai na har abada?” 17 Sai Yesu ya ce masa: “Don me kake tambaya na a kan abin da yake nagari? Allah kaɗai ne nagari. Idan kana so ka sami rai, ka ci-gaba da bin dokoki.” 18 Sai ya ce wa Yesu, waɗanne dokoki? Yesu ya ce: “Kada ka yi kisa, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kuma kada ka ba da shaidar ƙarya. 19 Ka girmama babanka da mamarka, kuma dole ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.” 20 Sai saurayin ya ce masa: “Ina yin dukan abubuwan nan, mene ne kuma ya rage da ban yi ba?” 21 Sai Yesu ya ce masa: “Idan kana so ka zama cikakke,* ka je ka sayar da dukan abubuwan da kake da su, ka ba wa talakawa, za ka sami dukiya a sama, sai ka zo ka bi ni.” 22 Da jin haka, sai saurayin ya tafi yana baƙin ciki sosai domin yana da dukiya mai yawa. 23 Sai Yesu ya ce wa almajiransa: “A gaskiya ina gaya muku, zai yi wa mai arziki wuya ya shiga Mulkin sama. 24 Ina kuma gaya muku, zai fi wa raƙumi sauƙi ya bi ta ramin allura da mai arziki ya shiga Mulkin Allah.”
25 Da almajiransa suka ji haka, suka yi mamaki sosai suka ce: “Wa zai iya samun ceto?” 26 Amma, da Yesu ya kalle su da kyau, sai ya ce musu: “A wurin mutane kam, ba zai yiwu ba, amma a wurin Allah kowane abu zai yiwu.”
27 Sai Bitrus ya amsa ya ce: “Ga shi, mun bar kome mun bi ka, to, wane lada ne za mu samu?” 28 Yesu ya ce musu: “A gaskiya ina gaya muku, a lokacin da aka mai da kome sabo, saꞌad da Ɗan mutum ya zauna a kujerar mulkinsa mai ɗaukaka, ku da kuka bi ni, za ku zauna a kujerun mulki goma sha biyu, kuna mulkin kabilu goma sha biyu na Israꞌila. 29 Kuma duk wanda ya bar gidaje, ko ꞌyanꞌuwa maza, ko ꞌyanꞌuwa mata, ko baba, ko mama, ko yara, ko gonaki, saboda sunana, zai sami fiye da hakan sau ɗari, kuma zai gāji rai na har abada.
30 “Amma mutane da yawa waɗanda suke na farko, za su zama na ƙarshe, na ƙarshe kuma za su zama na farko.