Ta Hannun Luka
13 A lokacin, waɗansu mutane da suke wurin sun gaya wa Yesu labarin mutanen Galili da Bilatus ya kashe saꞌad da suke miƙa hadaya. 2 Sai Yesu ya amsa musu ya ce: “Da yake hakan ya faru da mutanen nan, kuna ganin sun fi sauran mutanen Galili zunubi ne? 3 Aꞌa, amma ina gaya muku; idan ba ku tuba ba, ku ma za a hallaka ku duka. 4 Ko kuwa mutane goma sha takwas da gini ya faɗi a kansu a Siluwam kuma ya kashe su, kuna ganin zunubinsu ya fi na dukan mutanen da suke zama a Urushalima ne? 5 Aꞌa, amma ina gaya muku; idan ba ku tuba ba, dukanku za ku hallaka kamar su.”
6 Sai Yesu ya ba su wannan misalin kuma ya ce: “Akwai wani mutum da ya shuka itacen ɓaure a gonar inabinsa, ya zo don ya tsinka ꞌyaꞌyan amma bai samu ko ɗaya ba. 7 Sai ya ce wa mutumin da ke kula da gonar, ‘Ya kai shekara uku ke nan da nake zuwa ina neman ꞌyaꞌyan itacen ɓauren nan, amma ban samu ko ɗaya ba. Ka sare shi! Don me za a bar shi ya tare wuri a banza?’ 8 Sai mai kula da gonar ya amsa ya ce masa, ‘Maigida, mu ƙara masa shekara ɗaya har sai na tona rami kewaye da shi kuma in zuba taki. 9 Idan ya ba da ꞌyaꞌya a nan gaba, da kyau; amma idan bai ba da ꞌyaꞌya ba, sai ka sare shi.’”
10 Akwai lokacin da Yesu yake koyarwa a wata majamiꞌa a Ranar Assabaci. 11 Sai ga wata mata a wurin da wani aljani ya sa ta rashin lafiya na shekara goma sha takwas, matar ta tanƙware kuma ba ta iya miƙewa. 12 Saꞌad da Yesu ya gan ta, sai ya ce mata: “ꞌYarꞌuwata, an warkar da ke daga rashin lafiyarki.” 13 Sai ya sa hannayensa a kanta, nan da nan ta miƙe kuma ta soma yabon Allah. 14 Amma shugaban majamiꞌar ya yi fushi don Yesu ya yi warkarwar a Ranar Assabaci, sai ya ce wa jamaꞌar: “Akwai ranaku shida da ya kamata a yi aiki, don haka ku zo a ranakun nan a warkar da ku, ba a Ranar Assabaci ba.” 15 Amma Ubangiji ya amsa masa cewa: “Munafukai, ba kowannenku yakan kunce bijiminsa ko jakinsa daga wurin da ya ɗaura shi kuma ya kai shi inda zai sha ruwa a Ranar Assabaci ba? 16 Wannan matar ꞌyar Ibrahim ce, kuma Shaiɗan ya riƙe ta na shekara goma sha takwas, ba kwa ganin ya dace a warkar da ita a Ranar Assabaci?” 17 Saꞌad da ya faɗi abubuwan nan, dukan masu adawa da shi suka soma jin kunya, amma dukan jamaꞌar suka soma farin ciki don dukan abubuwa masu ban mamaki da ya yi.
18 Sai Yesu ya ci-gaba da magana, ya ce: “Yaya Mulkin Allah yake, kuma da me zan kwatanta shi? 19 Yana kama da ƙwayar mastad* da wani mutum ya ɗauko ya shuka a lambunsa, sai ta yi girma ta zama bishiya, kuma tsuntsayen sama suka yi gidansu a rassanta.”
20 Ƙari ga haka, ya ce: “Da mene ne zan kwatanta Mulkin Allah? 21 Yana kama da yisti wanda wata mata ta ɗauka ta kwaɓa da mudu uku na garin fulawa, har sai da dukan garin da aka kwaɓa ya kumbura.”
22 Da Yesu ya ci-gaba da tafiya zuwa Urushalima, sai ya bi garuruwa da ƙauyuka yana koyar da mutane. 23 Sai wani mutum ya ce masa: “Ubangiji, mutane kaɗan ne kawai za su sami ceto?” Sai Yesu ya ce musu: 24 “Ku yi ƙoƙari sosai ku shiga ta ƙaramar ƙofa, domin ina gaya muku, mutane da yawa za su so su shiga, amma ba za su iya ba. 25 Saꞌad da maigidan ya rufe ƙofarsa, za ku tsaya a waje kuna ƙwanƙwasawa kuna cewa, ‘Ubangiji, ka buɗe mana ƙofa.’ Shi kuma zai amsa muku ya ce: ‘Ban san daga ina kuka fito ba.’ 26 Saꞌan nan za ku soma cewa, ‘Mun ci, mun sha tare da kai, kuma ka koyar da mutane a titunanmu.’ 27 Amma zai ce muku, ‘Ban san daga ina kuka fito ba. Ku rabu da ni, dukanku masu yin rashin adalci!’ 28 Saꞌad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, da dukan annabawa a Mulkin Allah, amma ku kuma an jefar da ku waje, a wurin ne za ku yi ta kuka da cizon haƙora. 29 Ƙari ga haka, mutane za su zo daga gabas, da yamma, da arewa, da kuma kudu, za su zauna su ci abinci a teburi a Mulkin Allah. 30 Kuma akwai waɗanda suke na ƙarshe da za su zama na farko. Waɗanda suke na farko kuma za su zama na ƙarshe.”
31 A lokacin, wasu Farisiyawa suka zo suka ce masa: “Ka tashi ka bar nan, domin Hirudus* yana so ya kashe ka.” 32 Shi kuma ya ce musu: “Ku je ku gaya wa karen dajin nan, ‘Ga shi, yau da gobe ina fitar da aljanu, da kuma warkar da mutane, jibi zan gama.’ 33 Duk da haka dai, zan ci-gaba da aikina yau, da gobe, da jibi, domin ba zai yiwu a kashe annabi a wani wuri idan ba Urushalima ba. 34 Urushalima, Urushalima, wadda take kashe annabawa, da jifar waɗanda aka aiko gare ta, sau da yawa na so in tattara ꞌyaꞌyanki kamar yadda kaza take tattara ꞌyaꞌyanta a cikin fikafikanta, amma kin ƙi. 35 Ga shi! An bar muku gidanku. Ina gaya muku, ba za ku sake gani na ba har sai kun ce: ‘Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Jehobah!’”*