Ayyukan Manzanni
8 Shawulu kuwa, ya goyi bayan kisan Istifanus.
A ranar, ikilisiyar da ke Urushalima ta fuskanci tsanantawa sosai; dukan masu bin Yesu ban da manzannin, sun watse zuwa yankunan Yahudiya da kuma Samariya. 2 Amma waɗansu mutane masu tsoron Allah sun ɗauki Istifanus, domin su je su binne shi, kuma sun yi makoki sosai domin sa. 3 Shawulu kuwa, ya soma tsananta wa masu bi sosai. Yana shiga gida-gida yana jawo maza da mata, yana sa su a cikin kurkuku.
4 Amma, waɗanda suka watse, sun tafi suna shelar labari mai daɗi na kalmar Allah a ƙasar. 5 Ana nan sai Filibus ya tafi birnin* Samariya kuma ya soma yi musu waꞌazi game da Kristi. 6 Sai jamaꞌar suka mai da hankali da nufi ɗaya ga abin da Filibus yake faɗa, suna saurara da kuma lura da alamun ban mamaki da yake yi. 7 Mutane da yawa suna da ruhohi masu ƙazanta, kuma ruhohin sukan yi ihu da babbar murya kuma su fito. Ƙari ga haka, an warkar da mutane da yawa da jikinsu ya shanye da kuma guragu. 8 Saboda haka, mutane sun yi farin ciki sosai a birnin.
9 Akwai wani mutum a birnin, mai suna Siman, wanda kafin wannan lokacin yake yin sihiri a birnin, har yana ba wa mutanen ƙasar Samariya mamaki, yana cewa shi wani babban mutum ne. 10 Dukansu, yara da manya, sukan saurare shi kuma su ce: “Wannan mutum shi ne Ikon Allah da ake ce da shi, Mai Girma.” 11 Don haka, sukan saurare shi domin ya daɗe yana ba su mamaki da ayyukansa na sihiri. 12 Amma saꞌad da suka ba da gaskiya ga Filibus, wanda yake shelar labari mai daɗi na Mulkin Allah, da kuma sunan Yesu Kristi, sai aka yi wa maza da mata baftisma. 13 Siman ma da kansa ya zama mai ba da gaskiya, kuma bayan da aka yi masa baftisma, ya ci-gaba da bin Filibus; ya kuma yi mamaki da ganin alamu da kuma ayyukan ban mamaki da suke faruwa.
14 Saꞌad da manzanni a Urushalima suka ji cewa mutanen Samariya sun karɓi kalmar Allah, sai suka aike Bitrus da Yohanna zuwa wurinsu. 15 Sai Bitrus da Yohanna suka tafi, kuma suka yi wa mutanen adduꞌa don su sami ruhu mai tsarki. 16 Domin ruhu mai tsarki bai sauko a kan ko ɗayansu ba tukuna. Amma sun yi baftisma ne kawai a cikin sunan Ubangiji Yesu. 17 Sai Bitrus da Yohanna suka sa hannayensu a kan mutanen, kuma mutanen suka soma samun ruhu mai tsarki.
18 Da Siman ya ga cewa ana ba wa mutane ruhu mai tsarki domin manzannin sun saka hannaye a kan mutanen, sai ya miƙa wa manzannin kuɗi, 19 yana cewa: “Ku ba ni wannan ikon ni ma, domin duk wanda na saka hannayena a kansa, ya samu ruhu mai tsarki.” 20 Amma Bitrus ya ce masa: “Bari kai da azurfarka ku hallaka, domin ka ɗauka za ka iya sayan kyautar Allah da kuɗi. 21 Babu ruwanka da wannan batun, domin zuciyarka ba daidai take a gaban Allah ba. 22 Saboda haka, ka tuba daga ayyukanka na mugunta, ka roƙi Jehobah* cewa, idan zai yiwu, ya gafarta maka domin mugun nufin zuciyarka; 23 domin na ga cewa kai mai kishi* ne, da kuma bawan rashin adalci.” 24 Sai Siman ya amsa musu ya ce: “Ku roƙi Jehobah* a madadina domin kada ɗaya daga cikin abubuwan da kuka faɗa ya faru da ni.”
25 Saboda haka, bayan da suka ba da shaida sosai kuma suka gaya wa mutane kalmar Jehobah,* sai suka soma komawa Urushalima, suna yin shelar labari mai daɗi a ƙauyuka da yawa na Samariyawa.
26 Sai malaꞌikan Jehobah* ya yi magana da Filibus, yana cewa: “Ka tashi, ka je kudu zuwa hanyar da ta gangara daga Urushalima zuwa Gaza.” (Wannan hanyar hamada ce.) 27 Da jin haka, sai ya tashi ya tafi. Sai ya ga wani mutumin Itiyofiya wanda bābā* ne. Mutumin yana da matsayi a mulkin Kandis, sarauniyar Itiyofiya, shi ne yake kula da dukan dukiyarta. Dā ma ya je Urushalima ne domin ya yi ibada, 28 kuma yana dawowa zaune a kan keken-dokinsa,* yana karanta littafin annabi Ishaya da babbar murya. 29 Sai ruhu mai tsarki ya ce wa Filibus: “Ka je, ka yi kusa da wannan keken-dokin.”* 30 Sai Filibus ya gudu, ya je gefen keken-dokin* kuma ya ji shi yana karanta littafin annabi Ishaya da babbar murya, sai Filibus ya ce: “Ka gane abin da kake karantawa kuwa?” 31 Sai mutumin ya ce: “A ina kuwa? Ai ba zan gane ba, sai dai wani ya bayyana mini.” Sai ya roƙi Filibus ya hau keken-dokin* su zauna tare. 32 Sashen Nassin da yake karantawa ya ce: “An kai shi kamar tunkiya zuwa wurin yanka, kuma kamar yadda ɗan rago yake shuru a hannun mai aske masa gashin jikinsa, haka ma bai buɗe bakinsa ba. 33 A lokacin da aka wulaƙanta shi, ba a yi masa adalci ba. Wane ne zai iya bayyana labarin zuriyarsa? Domin an ɗauki ransa daga duniya.”
34 Sai bābān ya ce wa Filibus: “Ina roƙon ka, annabin yana magana game da wane ne? Game da kansa ne, ko kuma game da wani mutum ne?” 35 Sai Filibus ya soma magana, kuma daga wannan nassin, ya yi masa shelar labari mai daɗi game da Yesu. 36 Yayin da suke tafiya a kan hanya, sai suka kai wurin da akwai ruwa, kuma bābān ya ce: “Ga ruwa a nan! Me zai hana ni yin baftisma?” 37* —— 38 Sai mutumin ya ba da umurni a dakatar da keken-dokin,* sai Filibus da mutumin suka sauka suka shiga cikin ruwan, kuma Filibus ya yi wa mutumin baftisma. 39 Yayin da suka fito daga cikin ruwan, sai nan take ruhun Jehobah* ya sa Filibus ya bar wurin, kuma bābān bai sake ganin sa ba, sai ya ci-gaba da tafiya yana farin ciki. 40 Filibus kuwa, ya sami kansa a Ashdod, kuma ya bi ta cikin yankin, ya ci-gaba da yin shelar labari mai daɗi a cikin dukan garuruwan, har sai da ya isa Kaisariya.