Ayyukan Manzanni
19 Yayin da Afollos yake Korinti, Bulus ya zagaya cikin garuruwan har ya zo Afisa. A wurin ya haɗu da wasu almajirai 2 kuma ya ce musu: “Kun karɓi ruhu mai tsarki bayan kun zama masu bi ne?” Sai suka amsa suka ce masa: “Ba mu ma taɓa jin cewa akwai ruhu mai tsarki ba.” 3 Sai ya ce musu: “Wace irin baftisma ce aka yi muku?” Suka ce: “Baftismar Yohanna ce.” 4 Bulus ya ce: “Yohanna ya yi wa mutane baftisma don su nuna cewa sun tuba, yana gaya wa mutane su ba da gaskiya ga wanda yake zuwa bayansa, wato, ga Yesu.” 5 Da jin hakan, sai suka yi baftisma cikin sunan Ubangiji Yesu. 6 Da Bulus ya sa hannayensa a kansu, sai ruhu mai tsarki ya sauko musu kuma suka soma yin magana a yaruka dabam-dabam, da yin annabci. 7 Dukansu wajen mazaje goma sha biyu ne.
8 Bulus ya yi wata uku yana shiga majamiꞌa yana magana da ƙarfin hali, yana ba da jawabai da kuma rinjayar mutanen su ba da gaskiya ga Mulkin Allah. 9 Amma saꞌad da wasu suka yi taurin kai, suka ƙi ba da gaskiya kuma suna baƙar magana game da Hanyar Ubangiji a gaban jamaꞌar, sai Bulus ya fita daga cikinsu kuma ya ware almajiran daga tsakaninsu. Yana ba da jawabai kowace rana a babban ɗakin taro da ke makarantar Tiranus. 10 Ya yi hakan har na shekaru biyu, kuma dukan waɗanda suke zama a yankin Asiya, Yahudawa da kuma mutanen Girka sun ji kalmar Ubangiji.
11 Kuma Allah ya ci-gaba da yin ayyukan ban mamaki da ba a saba gani ba ta hannayen Bulus, 12 har ma idan aka ɗauki rigunan da suka taɓa jikinsa kuma aka kai wa marasa lafiya, sukan warke daga cututtukansu, kuma mugayen ruhohi sukan rabu da su. 13 Amma wasu Yahudawa waɗanda suke zuwa wurare dabam-dabam suna fitar da aljanu, sun yi ƙoƙari su yi amfani da sunan Ubangiji Yesu a kan waɗanda suke da mugayen ruhohi; sukan ce: “A cikin sunan Yesu wanda Bulus yake waꞌazinsa, na umurce ka ka fito.” 14 Akwai wani babban firist na Yahudawa mai suna Sikeba, da ke da yara maza bakwai da su ma suke yin hakan. 15 Amma mugun ruhun ya amsa musu ya ce: “Na san Yesu kuma na san Bulus; amma ku wane ne?” 16 Sai mutumin da ke da mugun ruhun ya yi tsalle ya faɗi a kansu, ya sha ƙarfinsu ɗaya bayan ɗaya, har suka gudu suka bar gidan tsirara da raunuka a jikinsu. 17 Wannan labarin ya yaɗu a koꞌina a tsakanin Yahudawa da mutanen Girka da suke zama a Afisa; tsoro ya kama dukansu, kuma an ci-gaba da ɗaukaka sunan Ubangiji Yesu. 18 Mutane da yawa daga cikin waɗanda suka ba da gaskiya, sukan zo su faɗi zunubansu da abubuwan da suka yi a gaban dukan mutane. 19 Mutane da yawa masu yin sihiri a dā suka tattaro littattafansu suka ƙona su a gaban kowa. Da suka yi lissafin kuɗin littattafan, sai suka ga ya kai tsabar azurfa dubu hamsin. 20 Don haka, ta gagarumar hanya, kalmar Jehobah* ta ci-gaba da yaɗuwa da kuma yin nasara.
21 Bayan abubuwan nan sun faru, Bulus ya shirya a ransa cewa bayan ya zagaya Makidoniya da Akaya, zai je Urushalima. Ya ce: “Bayan na je wurin, dole ne kuma in je Roma.” 22 Sai ya aiki mutane biyu daga cikin waɗanda suke taimaka masa, wato Timoti da Erastus zuwa Makidoniya, amma shi da kansa ya ci-gaba da zama na ɗan lokaci a yankin Asiya.
23 A lokacin, an yi babban tashin hankali game da Hanyar Ubangiji. 24 Domin wani mutum mai suna Dimitiriyus, wanda maƙeri ne da yake ƙera siffar haikalin Artemis, da waɗanda suke sanaꞌar nan suna samun kuɗi sosai. 25 Sai ya tara su da wasu da suke yin irin aikin nan kuma ya ce: “ꞌYanꞌuwana, kun san cewa daga wannan sanaꞌar ce muke samun arzikinmu. 26 Kuna gani kuma kuna ji ba kawai a Afisa ba amma a kusan dukan yankin Asiya, yadda wannan Bulus ya rinjayi mutane da yawa kuma sun juya ga wani raꞌayi dabam. Yana cewa allolin da aka yi da hannaye ba alloli na gaskiya ba ne. 27 Ƙari ga haka, wannan zai sa mutane ba za su riƙa daraja sanaꞌarmu ba, kuma mutane ba za su ɗauki haikalin allahiya mai girma Artemis a matsayin wani abu ba, kuma allahiyar nan da ake bauta wa a dukan yankin Asiya da dukan duniya, za a raba ta da darajarta.” 28 Da suka ji haka, mutanen suka yi fushi sosai kuma suka soma ihu suna cewa: “Girma ta tabbata ga Artemis ta Afisawa!”
29 Sai birnin gabaki-ɗaya ya ruɗe, kuma dukan mutanen suka kama Gayus da Aristarkus, mutanen Makidoniya da suke tafiya tare da Bulus, kuma suka ruga da su zuwa filin wasa. 30 Bulus ya so ya shiga inda jamaꞌar suke amma almajiran sun hana shi. 31 Har ma wasu masu shirya bukukuwa da wasanni, waɗanda abokan Bulus ne, sun aika masa saƙo suna roƙan sa kada ya sa ransa cikin haɗari ta wajen shiga filin. 32 Mutanen da suka taru a filin wasan sun ruɗe, wasu suna ihu suna cewa abu kaza, waɗansu kuma wani abu dabam, yawancin mutanen ma ba su san dalilin da ya sa suka taru ba. 33 Sai suka fitar da Alekzanda daga cikin jamaꞌa, Yahudawa kuwa suna tura shi gaba. Sai Alekzanda ya yi wa mutanen alama da hannunsa cewa su yi shuru don yana so ya kāre kansa. 34 Amma saꞌad da suka gane cewa shi Bayahude ne, sai dukansu suka soma ihu gabaki-ɗaya na wajen awa biyu suna cewa: “Girma ta tabbata ga Artemis ta Afisawa!”
35 Saꞌad da magajin garin ya sa taron suka yi shuru a ƙarshe, sai ya ce: “Ya ku mutanen Afisa, wane ne bai sani ba cewa birnin Afisa ne yake lura da haikalin Artemis mai girma da siffarta da ta faɗo daga sama? 36 Tun da yake ba wanda ya isa ya yi mūsun abubuwan nan, ya kamata ku kwantar da hankalinku, kuma kada ku yi abu da garaje. 37 Ga shi kun kawo mutanen nan a nan, waɗanda ba masu fashi a haikali ba ne, kuma ba su saɓa wa allahiyarmu ba. 38 Saboda haka, idan Dimitiriyus da maƙera da suke aiki tare da shi suna da ƙara a kan wani, akwai ranakun da ake kai ƙara kotu kuma akwai gwamnoni, sai su kawo ƙarar juna. 39 Amma idan kuna neman wani abu fiye da hakan, dole ne mu taru bisa doka don mu tsai da shawara a kan batun. 40 Abin da ya faru yau zai iya sa mu cikin haɗari sosai, za a iya tuhumar mu da yi wa gwamnati tawaye, don ba mu da dalilin da za mu bayar wanda ya sa jamaꞌa suka taru suna tashin hankali.” 41 Bayan da ya faɗi wannan, sai ya sallami taron jamaꞌar.