Ayyukan Manzanni
28 Bayan da dukanmu muka tsira, sai muka gano cewa sunan tsibirin shi ne Malta. 2 Kuma mutanen tsibirin sun yi mana alheri sosai. Sun kunna mana wuta, kuma suka karɓi dukanmu hannu bibbiyu saboda ruwan sama da sanyi da ake yi. 3 Amma saꞌad da Bulus ya tattaro itatuwa ya saka a wutar, sai maciji ya fito saboda zafi, kuma ya nannaɗe jikinsa a hannun Bulus. 4 Da mazaunan wurin suka ga macijin yana lilo a hannun Bulus, sai suka soma gaya wa junansu cewa: “Lallai wannan mutum mai kisa ne. Kuma ko da yake ya tsira daga teku, ba zai ci-gaba da rayuwa ba domin akwai alhaki* a kansa.” 5 Saꞌad da Bulus ya jijjiga hannunsa, sai macijin ya faɗi a cikin wutar, kuma babu abin da ya same Bulus. 6 Amma mutanen suna tsammanin cewa Bulus zai kumbura ko kuma ya faɗi ya mutu. Bayan da suka jira na dogon lokaci kuma suka ga babu abin da ya same shi, sai suka canja raꞌayinsu kuma suka soma cewa shi allah ne.
7 Shugaban tsibirin mai suna Fubiliyus yana zama kusa da wurin kuma yana da filaye. Ya marabce mu a gidansa kuma ya kula da mu har kwana uku. 8 A daidai lokacin kuwa, baban Fubiliyus yana kwance yana fama da zazzaɓi da zawo,* Bulus ya shiga wurinsa kuma ya yi masa adduꞌa, sai ya sa hannayensa a kan baban Fubiliyus kuma ya warkar da shi. 9 Bayan wannan ya faru, sai sauran mutane da ke rashin lafiya a tsibirin suka soma zuwa wurinsa, kuma ya warkar da su. 10 Sai suka ba mu kyaututtuka da yawa, kuma da muke shirin barin wurin da jirgin ruwa, sun ba mu dukan abubuwan da muke bukata.
11 Bayan wata uku, sai muka tashi a wani jirgin ruwa da ke da siffar “ꞌYaꞌyan Zeyus” a gabansa. Jirgin ruwan daga Alekzandiriya ne, kuma ya kasance a tsibirin a lokacin sanyi. 12 Bayan mun isa tashar jirgin ruwa da ke Sirakus, sai muka zauna a wurin na kwana uku. 13 Daga wurin mun tashi muka iso Rigiyum. Bayan kwana ɗaya, sai wata iskar kudu ta taso, kuma muka kai Futiyoli washegari. 14 A nan mun haɗu da wasu ꞌyanꞌuwa kuma sun roƙe mu mu yi kwana bakwai da su. Daga wurin mun kama hanya zuwa Roma. 15 Saꞌad da ꞌyanꞌuwa a Roma suka ji labari cewa muna zuwa, sai suka zo Kasuwar Affiyus da kuma Masauki Uku don su haɗu da mu. Da Bulus ya gan su, sai ya gode wa Allah kuma ya yi ƙarfin zuciya. 16 Saꞌad da muka isa Roma, sai aka yarda Bulus ya zauna a gidan haya tare da soja da ke gadin sa.
17 Amma bayan kwana uku, sai ya kira shugabannin Yahudawa. Saꞌad da suka taru, sai ya ce musu: “ꞌYanꞌuwana, ko da yake ban yi wa jamaꞌarmu wani laifi ba, ko laifi game da alꞌadun kakanninmu, duk da haka an kama ni a Urushalima kuma an ba da ni ga Romawa a matsayin fursuna. 18 Bayan sun bincika ƙarar da aka kawo a kaina, sun so su sake ni, domin ba su same ni da laifin da ya kai a kashe ni ba. 19 Saꞌad da Yahudawa suka ƙi, ya zama mini dole in ɗaukaka ƙara zuwa wurin Kaisar, ba wai domin ina da wani zargin da zan kawo a kan mutanena ba. 20 Shi ya sa na nemi in gan ku kuma in tattauna da ku, domin begen da alꞌummar Israꞌila take da shi ne aka ɗaure ni da sarƙar nan.” 21 Sai suka ce masa: “Ba mu samu wasiƙu daga Yahudiya game da kai ba, kuma babu wani ɗanꞌuwa da ya zo daga can da ya kawo wani labari ko ya faɗi wani abu marar kyau game da kai ba. 22 Amma muna ganin ya dace mu ji raꞌayinka, domin a gaskiya ana maganar da ba ta dace ba game da wannan ƙungiyar a koꞌina.”
23 Sai suka shirya su haɗu da shi wata rana, kuma adadin mutanen da suka zo wurin da Bulus yake zama sun fi na dā yawa. Daga safe zuwa yamma, ya bayyana musu batun ta wajen yi musu waꞌazi sosai game da Mulkin Allah, ya yi amfani da Dokar Musa da abubuwan da annabawa suka rubuta don ya sa su ba da gaskiya ga Yesu. 24 Wasu sun ba da gaskiya ga abubuwan da ya faɗa, wasu kuma sun ƙi ba da gaskiya. 25 Da yake ba su yarda da juna ba, sai suka soma barin wurin. Bulus kuma ya yi wata magana ya ce:
“Ruhu mai tsarki ya faɗi gaskiya saꞌad da ya yi wa kakanninku magana ta bakin annabi Ishaya, 26 yana cewa, ‘Ka je wurin mutanen nan kuma ka ce: “Hakika, za ku ji, amma ba za ku taɓa fahimta ba. Hakika, za ku duba, amma ba za ku taɓa ganin wani abu ba. 27 Domin zuciyar mutanen nan ta yi tauri, suna ji da kunnuwansu amma ba sa yin abubuwan da suka ji. Sun kuma rufe idanunsu don kada su taɓa gani da idanunsu, kada kuma su ji da kunnuwansu domin kada su fahimta har su juyo in kuma warkar da su.”’ 28 Saboda haka, ina so ku san cewa, ana yi wa mutanen alꞌummai waꞌazin wannan saƙo na yadda Allah zai ceci mutane, kuma a gaskiya za su saurara.” 29* ——
30 Don haka, Bulus ya ci-gaba da zama a gidan da yake haya har na shekara biyu, kuma dukan waɗanda suka zo wurinsa, yakan marabce su hannu bibbiyu, 31 yana yi musu waꞌazin Mulkin Allah, da koya musu game da Ubangiji Yesu Kristi ba tsoro,* kuma ba tare da wani abu ya hana shi ba.