Ta Hannun Matiyu
17 Bayan kwana shida, Yesu ya ɗauki Bitrus da Yaƙub da Yohanna ɗanꞌuwan Yaƙub, ya kai su wani tudu mai tsawo inda suka kasance su kaɗai. 2 Sai kamannin Yesu ya canja a gabansu; fuskarsa ta yi haske kamar rana, mayafinsa kuma ya yi fari fat. 3 Sai nan da nan suka ga Musa da Iliya sun fito, kuma suna magana da shi. 4 Sai Bitrus ya ce wa Yesu: “Ubangiji, yana da kyau da muka zo nan. Idan kana so, zan kafa tentuna* guda uku a nan. Ɗaya domin ka, ɗaya na Musa, ɗaya kuma na Iliya.” 5 Yayin da yake kan magana, sai gajimare mai haske ya rufe su, kuma wata murya daga cikin gajimaren ta ce: “Wannan shi ne Ɗana wanda nake ƙauna, na amince da shi. Ku saurare shi.” 6 Da almajiran suka ji haka, sai tsoro ya kama su sosai, kuma suka rusuna. 7 Sai Yesu ya zo ya taɓa su, kuma ya ce: “Ku tashi. Kada ku ji tsoro.” 8 Da suka ɗaga kai, ba su ga kowa ba, sai Yesu kaɗai. 9 Da suke saukowa daga kan tudun, sai Yesu ya ja musu kunne cewa: “Kada ku gaya wa kowa game da wahayin, har sai Ɗan mutum ya tashi daga mutuwa.”
10 Amma almajiransa suka yi masa tambaya cewa: “To, don me marubuta suka ce Iliya ne zai fara zuwa?” 11 Sai ya amsa musu ya ce: “Lallai Iliya zai zo, zai kuma mai da abubuwa yadda suke a dā. 12 Amma ina gaya muku, Iliya ya riga ya zo, amma ba su gane shi ba. Har ma suka yi masa abin da suka ga dama. Haka ma, Ɗan mutum zai sha wahala a hannunsu.” 13 Sai almajiran suka gane cewa yana yi musu magana a kan Yohanna Mai Baftisma ne.
14 Da suka yi kusa da inda jamaꞌa suke, sai wani mutum ya zo wurin Yesu, kuma ya durƙusa a gabansa, ya ce: 15 “Ubangiji, ka tausaya wa ɗana, domin yana da ciwon farfaɗiya kuma hakan na wahalar da shi sosai. Yana yawan faɗi a cikin wuta da kuma ruwa. 16 Na kawo shi wurin almajiranka, amma sun kasa warkar da shi.” 17 Sai Yesu ya ce: “Ku mutanen zamanin nan marasa bangaskiya, masu mugunta, har yaushe zan ci-gaba da kasancewa tare da ku? Har yaushe zan ci-gaba da yin haƙuri da ku? Ku kawo mini shi nan.” 18 Sai Yesu ya tsawata wa aljanin, aljanin ya bar yaron, kuma yaron ya warke nan take. 19 Sai almajiran Yesu suka same shi shi kaɗai kuma suka ce masa: “Me ya sa ba mu iya fitar da aljanin ba?” 20 Ya ce musu: “Domin ƙarancin bangaskiyarku ne. A gaskiya ina gaya muku, ko da bangaskiyarku ƙarama ce kamar ƙwayar mastad,* za ku iya gaya ma wannan tudun, ‘Ka tashi daga nan zuwa can,’ zai kuwa tashi, kuma babu abin da zai gagare ku.” 21* ——
22 Saꞌad da suke tare a Galili ne Yesu ya gaya musu cewa: “Za a ci amanar Ɗan mutum kuma a ba da shi ga mutane, 23 za su ma kashe shi, kuma a rana ta uku za a ta da shi.” Sai almajiransa suka damu sosai.
24 Da suka isa Kafarnahum, sai masu karɓan haraji* suka sami Bitrus kuma suka ce masa: “Malaminku yana biyan harajin haikali kuwa?” 25 Sai Bitrus ya ce: “E, yana biya.” Amma, da Bitrus ya dawo gida, sai Yesu ya fara yi masa magana ya ce: “Mene ne raꞌayinka Siman? Daga wurin wa sarakunan duniyar nan suke karɓan kuɗin haraji? Daga wurin ꞌyaꞌyansu ne ko daga wurin baƙi?” 26 Da Bitrus ya ce masa: “Daga wurin baƙi,” sai Yesu ya amsa masa ya ce: “Don haka, ꞌyaꞌyan ba sa bukatar su biya haraji. 27 Amma don kada mu sa su tuntuɓe, ka je teku, kuma ka jefa ƙugiya, sai ka buɗe bakin kifin da ka fara kamawa, za ka ga tsabar kuɗin azurfa guda ɗaya.* Ka ɗauki kuɗin ka biya harajinka da nawa.”