Ayyukan Manzanni
13 A ikilisiya da ke Antakiya, akwai annabawa da malamai kamar su: Barnabas, da Simeyon wanda ake kira Baƙi,* da Lushiyus daga Sayirin, da Manayen wanda ya yi karatu tare da Hirudus* mai mulkin yanki, da kuma Shawulu. 2 Yayin da suke yi wa Jehobah* hidima da kuma azumi, sai ruhu mai tsarki ya ce: “Ku ware mini Barnabas da Shawulu domin aiki wanda na kira su su yi.” 3 Bayan da suka gama azumi da adduꞌa, sai suka sa hannayensu a kan Barnabas da Shawulu, kuma suka sallame su.
4 Waɗannan mutanen da ruhu mai tsarki ya aike su, sun gangara zuwa Salukiya, kuma daga wurin sun shiga jirgin ruwa zuwa Saifrus. 5 Saꞌad da suka isa Salamis, sai suka soma shelar kalmar Allah a majamiꞌun Yahudawa. Kuma suna tare da Yohanna wanda yake yi musu hidima.*
6 Da suka gama zagaya tsibirin har suka isa Fafos, sai suka haɗu da wani Bayahude mai suna Ba-Yesu, shi mai yin sihiri ne kuma annabin ƙarya ne. 7 Yana tare da wani gwamna* mai suna Sarjiyus Bulus, gwamnan mai hikima ne sosai. Gwamnan yana so ya ji kalmar Allah, sai ya kira Barnabas da Shawulu su zo wurinsa. 8 Amma Elimas mai yin sihirin (gama haka aka fassara sunansa) ya soma gāba da Barnabas da Shawulu kuma yana ƙoƙarin hana gwamnan ba da gaskiya. 9 Sai aka cika Shawulu, wanda kuma ake kira Bulus, da ruhu mai tsarki, kuma ya zuba ma Elimas ido, 10 sai ya ce: “Ya kai da kake cike da kowane irin ruɗu, da kowane irin mugunta, kai ɗan Ibilis, mai gāba da duk abin da ke na adalci, ba za ka daina ɓata hanyoyin adalci na Jehobah* ba? 11 Ga shi hannun Jehobah* yana kanka, kuma za ka makance, za ka ɗau lokaci ba ka ga hasken rana ba.” Nan take, sai hazo da duhu suka faɗo masa kuma ya yi ta lalubawa, yana neman wanda zai riƙe hannunsa ya yi masa ja-gora. 12 Da gwamnan ya ga abin da ya faru, sai ya zama mai bi, gama koyarwar Jehobah* ta ba shi mamaki.
13 Sai Bulus da abokan tafiyarsa suka shiga jirgin ruwa daga Fafos, kuma suka isa Ferga da ke Famfiliya. Amma Yohanna ya bar su, ya koma Urushalima. 14 Su kuwa suka ci-gaba daga Ferga zuwa Antakiya da ke Bisidiya. Da suka shiga majamiꞌa a Ranar Assabaci, sai suka zauna. 15 Bayan da aka karanta wa jamaꞌa littafin Doka* da na annabawa, sai shugabannin majamiꞌar suka aika musu saƙo, suna cewa: “ꞌYanꞌuwa, idan kuna da wata maganar ƙarfafa don jamaꞌar, sai ku yi.” 16 Sai Bulus ya tashi tsaye, kuma ya yi alama da hannunsa ya ce:
“Mutanen Israꞌila da kuma sauranku da kuke tsoron Allah, ku saurara. 17 Allahn mutanen Israꞌila ya zaɓi kakanninmu, kuma ya ɗaukaka mutanen, saꞌad da suke zama a ƙasar Masar a matsayin baƙi, ya kuma yi amfani da ikonsa ya fitar da su daga wurin. 18 Kuma ya yi wajen shekaru arbaꞌin yana haƙuri da su a cikin daji. 19 Bayan da ya hallaka alꞌummai bakwai a ƙasar Kanꞌana, sai ya ba su ƙasar mutanen a matsayin gādo. 20 Dukan abubuwan nan sun faru a cikin wajen shekaru ɗari huɗu da hamsin.
“Bayan haka, sai ya naɗa musu alƙalai, har zuwa zamanin annabi Samaꞌila. 21 Daga baya, sai suka ce a ba su sarki, sai Allah ya naɗa musu Shawulu ɗan Kish, wanda ya fito daga kabilar Benjamin a matsayin sarki, kuma ya yi sarauta na shekaru arbaꞌin. 22 Bayan ya cire shi, sai ya naɗa musu Dauda a matsayin sarki, ya kuma ba da shaida game da shi, ya ce: ‘Na sami Dauda ɗan Jesse, mutumin da zuciyata take ƙauna; zai yi dukan abubuwan da nake so.’ 23 Bisa ga alkawarinsa, ta wurin zuriyar mutumin nan, Allah ya kawo wa Israꞌila mai ceto, wato Yesu. 24 Kafin zuwan wannan, Yohanna ya yi wa dukan mutanen Israꞌila waꞌazi a fili yana cewa su yi baftisma don su nuna cewa sun tuba. 25 Amma yayin da Yohanna yake kammala hidimarsa, yakan ce: ‘Kuna tsammanin ni wane ne? Ba ni ba ne shi. Amma akwai wanda yake zuwa a bayana, wanda ko takalman ƙafafunsa ban isa in cire ba.’
26 “Ya ku ꞌyanꞌuwa, zuriyar Ibrahim, da masu tsoron Allah da ke tare da ku, Allah ya aika mana saƙo game da yadda za mu sami ceto. 27 Mazaunan Urushalima da shugabanninsu ba su yarda da shi ba, amma saꞌad da suke yi masa shariꞌa, sun cika abubuwan da annabawa suka faɗa, waɗanda ake karanta wa jamaꞌa a kowace Ranar Assabaci. 28 Ko da yake ba su kama shi da laifin da ya kai a kashe shi ba, duk da haka sun roƙi Bilatus ya sa a kashe shi. 29 Kuma bayan da suka cika dukan abubuwan da aka rubuta game da shi, sai suka saukar da shi daga kan gungumen, kuma suka kwantar da shi a cikin kabari. 30 Amma Allah ya ta da shi daga mutuwa, 31 ya bayyana na kwanaki da yawa ga waɗanda suka zo tare da shi daga Galili zuwa Urushalima. A yanzu, waɗannan su ne shaidunsa ga mutane.
32 “Don haka, muna yi muku shelar labari mai daɗi game da alkawarin da aka yi wa kakanninmu. 33 Allah ya sa dukan abubuwan da aka faɗa a cikin alkawarin sun cika mana, mu ꞌyaꞌyansu, ta wurin ta da Yesu daga mutuwa; kamar yadda aka rubuta a zabura ta biyu cewa: ‘Kai ne ɗana, kuma yau na zama babanka.’ 34 Tun da yake Allah ya ta da shi daga mutuwa kuma ba zai sake ruɓewa ba, Allah ya faɗa cewa: ‘Zan nuna muku wannan ƙauna marar canjawa da na yi alkawarin ta ga Dauda, wadda tabbatacciya ce.’* 35 An kuma faɗa a wata zabura cewa: ‘Ba za ka bar wanda yake da aminci a gare ka ya ruɓe ba.’ 36 Dauda ya bauta wa Allah a zamaninsa, amma ya mutu kuma an binne shi tare da kakanninsa. Don haka, ya ruɓe. 37 Amma shi wanda Allah ya tayar daga mutuwa, bai ruɓe ba.
38 “Saboda haka ꞌyanꞌuwa, bari ku san cewa, ta wurin wannan ne ake muku shelar gafarar zunubai. 39 Kuma daga dukan zunubai da Dokar Musa ta kasa ꞌyantar da ku, ta wurin mutumin nan, Allah ya ce duk wanda ya ba da gaskiya, an ꞌyantar da shi daga zunubansa. 40 Don haka, ku lura fa domin kada abubuwan nan da annabawa suka rubuta su cika a kanku, wato: 41 ‘Ku dube shi, ku masu yin baꞌa, don ku yi mamaki kuma ku hallaka domin ina yin aiki a kwanakinku, aikin da ba za ku taɓa yarda da shi ba, ko da wani ya bayyana muku shi dalla-dalla.’”
42 Yayin da suke fita, sai mutanen suka roƙe su su sake tattauna batutuwan nan a Ranar Assabaci mai zuwa. 43 Bayan da aka sallami jamaꞌar da suka taru a majamiꞌar, sai Yahudawa da yawa da mutanen da suka karɓi addinin Yahudawa* kuma suke bauta wa Allah suka bi Bulus da Barnabas, yayin da Bulus da Barnabas suke magana da su, sun ƙarfafa su su ci-gaba da kasancewa cikin alherin Allah.
44 Da Ranar Assabaci ta zagayo, kusan dukan mutanen birnin sun taru don su ji kalmar Jehobah.* 45 Da Yahudawan suka ga jamaꞌar, sai kishi ya kama su, kuma suka soma maganganun saɓo da mūsun abubuwan da Bulus yake faɗa. 46 Sai Bulus da Barnabas suka yi magana ba tsoro suka ce: “Ku Yahudawa ne ya kamata a fara gaya muku kalmar Allah, amma tun da kun ƙi, kuma kun nuna cewa ba ku cancanci samun rai na har abada ba, za mu je wurin mutanen alꞌummai. 47 Domin Jehobah* ya umurce mu da kalmomin nan cewa: ‘Na naɗa ka ka zama kamar haske ga alꞌummai domin ka zama ceto har zuwa iyakar duniya.’”*
48 Da mutanen alꞌummai suka ji hakan, sai suka soma farin ciki da kuma ɗaukaka kalmar Jehobah,* kuma dukan waɗanda suke marmarin samun rai na har abada, sun zama masu bi. 49 Ƙari ga haka, kalmar Jehobah* ta yaɗu zuwa koꞌina a cikin ƙasar. 50 Amma Yahudawan suka zuga matan da ake girmamawa, waɗanda suke tsoron Allah, da kuma manyan mutanen garin, sai suka sa aka soma tsananta wa Bulus da Barnabas, kuma suka kore su daga garinsu. 51 Sai suka kakkaɓe ƙurar da ke ƙafafunsu don ya zama shaida a kan mutanen garin kuma suka tafi Ikoniya. 52 Almajiran sun ci-gaba da kasancewa cike da farin ciki da kuma ruhu mai tsarki.