Ta Hannun Luka
15 Wata rana, sai dukan masu karɓan haraji, da masu zunubi suka yi ta taruwa kusa da Yesu don su saurare shi. 2 Sai Farisiyawa da marubuta suna ta gunaguni suna cewa: “Wannan mutumin yana shaꞌani da masu zunubi kuma yana cin abinci tare da su.” 3 Sai ya ba su wannan misalin yana cewa: 4 “Wane ne a cikinku, da yake da tumaki ɗari, sai ɗaya a cikinsu ta ɓata, da ba zai bar sauran casaꞌin da tara a cikin daji ya je ya nemi ɗayan da ta ɓata ba? 5 Kuma idan ya same ta, zai sa ta a kafaɗarsa yana murna. 6 Kuma saꞌad da ya koma gida, zai kira abokansa da maƙwabtansa yana ce musu, ‘Ku taya ni murna, domin na ga tunkiyata da ta ɓata.’ 7 Haka ma, ina gaya muku, za a yi murna sosai a sama, a kan mai zunubi ɗaya da ya tuba, fiye da masu adalci casaꞌin da tara da ba sa bukatar su tuba.
8 “Ko kuma a ce wata mata tana da tsabar kuɗin drakma guda goma, idan ɗaya daga cikinsu ya ɓata, ba kwa ganin za ta kunna fitila, ta share gidanta, kuma ta nemi kuɗin da kyau har sai ta same shi ba? 9 Kuma idan ta sami kuɗin, za ta kira ƙawayenta, da maƙwabtanta, tana cewa, ‘Ku taya ni murna, domin na sami tsabar kuɗin drakma da na ɓatar.’ 10 Haka nan ma, ina gaya muku, malaꞌikun Allah suna farin ciki idan mai zunubi ɗaya ya tuba.”
11 Sai ya ce: “Akwai wani mutum da yake da yara maza biyu. 12 Sai ƙaramin ya ce wa babansa: ‘Baba, ka ba ni rabon gādona yanzu.’ Sai baban ya raba musu dukiyarsa. 13 Bayan ꞌyan kwanaki, sai ƙaramin ɗansa, ya tattara dukan kayayyakinsa, ya tafi wata ƙasa mai nisa, a wurin ya cinye dukan dukiyarsa ta wajen yin rayuwar iskanci. 14 Saꞌad da ya cinye dukan dukiyarsa, sai aka soma yunwa mai tsanani a dukan ƙasar, kuma bai da kome. 15 Sai ya je ya zauna da wani mutumin ƙasar, mutumin ya tura shi ya yi kiwon aladunsa. 16 Yunwa ta dame shi sosai har ya so ya ci abincin aladu,* amma ba wanda ya yarda ya ba shi kome.
17 “Saꞌad da ya dawo cikin hankalinsa, sai ya ce, ‘Maꞌaikata da yawa suna yi wa babana aiki kuma suna cin abinci har su ƙoshi, amma ga ni nan, yunwa tana so ta kashe ni a banza! 18 Zan tashi in koma wurin babana in ce masa: “Baba, na yi wa Allah da ke sama zunubi kuma na yi maka zunubi. 19 Ban cancanci a kira ni ɗanka ba. Ka sa in zama kamar ɗaya daga cikin maꞌaikatanka.”’ 20 Sai ya tashi ya tafi wurin babansa. Tun yana nesa, babansa ya hango shi, kuma ya tausaya masa. Sai baban ya gudu ya same shi, ya rungume shi, kuma ya yi masa sumba. 21 Sai ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa Allah da ke sama zunubi kuma na yi maka zunubi. Ban cancanci a kira ni ɗanka ba.’ 22 Amma baban ya ce wa bayinsa, ‘Ku yi sauri! ku kawo riga mafi kyau, ku sa masa, ku sa masa zobe a hannu, da kuma takalma a ƙafa. 23 Ƙari ga haka, ku kawo saniya mai ƙiba, ku yanka ta, mu ci kuma mu yi murna, 24 domin wannan ɗana ya mutu, amma ya tashi; ya ɓata, an kuma samo shi.’ Sai suka soma shagali.
25 “A lokacin, babban ɗansa yana gona, kuma da yake dawowa, saꞌad da ya yi kusa da gida, sai ya ji ana kiɗi da rawa. 26 Sai ya kira ɗaya daga cikin bayin, ya tambaye shi abin da ke faruwa. 27 Sai ya ce masa, ‘Ɗanꞌuwanka ya dawo, kuma babanka ya yanka saniya mai ƙiba, domin ya dawo lafiya.’ 28 Amma ya yi fushi, ya ƙi ya shiga cikin gida. Sai babansa ya fito yana ba shi haƙuri. 29 Sai ya amsa ya ce wa babansa, ‘Na yi shekaru da yawa ina yi maka aiki kamar bawa kuma ban taɓa yi maka rashin biyayya ba, amma duk da haka, ba ka taɓa ba ni ɗan akuya don in ci tare da abokaina ba. 30 Amma, saꞌad da wannan ɗanka ya dawo, wanda ya kashe dukiyarka tare da karuwai, nan da nan ka yanka masa saniya mai ƙiba.’ 31 Sai baban ya ce masa, ‘Ɗana, kullum kana nan tare da ni, duk abin da nake da shi, ai naka ne. 32 Amma dole ne mu yi farin ciki da murna, domin ɗanꞌuwanka ya mutu amma ya tashi; ya ɓata, an kuma same shi.’”