Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)

Abubuwan da Ke Cikin Littafin Markus

MARKUS

ABUBUWAN DA KE CIKIN LITTAFIN NAN

  • 1

    • Yohanna Mai Baftisma yana waꞌazi (1-8)

    • An yi wa Yesu baftisma (9-11)

    • Shaiɗan ya gwada Yesu (12, 13)

    • Yesu ya soma waꞌazi a Galili (14, 15)

    • Yesu ya kira almajiransa na farko (16-20)

    • Yesu ya fitar da ruhu mai ƙazanta (21-28)

    • Yesu ya warkar da mutane da yawa a Kafarnahum (29-34)

    • Yesu ya yi adduꞌa a wurin da babu kowa (35-39)

    • An warkar da wani kuturu (40-45)

  • 2

    • Yesu ya warkar da mutumin da jikinsa ya shanye (1-12)

    • Yesu ya kira Lawi (13-17)

    • Tambaya game da yin azumi (18-22)

    • Yesu ‘Ubangiji ne na Assabaci’ (23-28)

  • 3

    • An warkar da mutumin da hannunsa ya shanye (1-6)

    • Jamaꞌa sun taru a bakin teku (7-12)

    • Manzannin Yesu goma sha biyu (13-19)

    • Maganar saɓo game da ruhu mai tsarki (20-30)

    • Mamar Yesu da kuma ꞌyanꞌuwansa (31-35)

  • 4

    • MISALAI GAME DA MULKI (1-34)

      • Misalin mai shuki (1-9)

      • Abin da ya sa Yesu ya yi amfani da misalai (10-12)

      • Ya bayyana maꞌanar misalin mai shuki (13-20)

      • Ba a rufe fitila (21-23)

      • Mudun da ka yi amfani da shi (24, 25)

      • Misalin mai shukin da ya yi barci (26-29)

      • Misalin ƙwayar mastad (30-32)

      • Yin amfani da misalai (33, 34)

    • Yesu ya dakatar da iska mai ƙarfi (35-41)

  • 5

    • Yesu ya tura aljanu su shiga jikin aladu (1-20)

    • ꞌYar Yayirus; wata mata ta taɓa mayafin Yesu (21-43)

  • 6

    • An ƙi Yesu a garinsa (1-6)

    • Yesu ya ba wa almajiransa goma sha biyu umurni a kan yadda za su yi waꞌazi (7-13)

    • Mutuwar Yohanna Mai Baftisma (14-29)

    • Yesu ya ciyar da maza dubu biyar (30-44)

    • Yesu ya yi tafiya a kan ruwa (45-52)

    • Yesu ya warkar da mutane a Ganisaret (53-56)

  • 7

    • Yesu ya fallasa alꞌadun ꞌyanꞌadam (1-13)

    • Abin da ke ƙazantar da mutum daga zuciya ne (14-23)

    • Bangaskiyar ꞌYar Finikiya da ke ƙasar Siriya (24-30)

    • Yesu ya warkar da wani kurma (31-37)

  • 8

    • Yesu ya ciyar da maza dubu huɗu (1-9)

    • An ce Yesu ya nuna alama (10-13)

    • Yistin Farisiyawa da na Hirudus (14-21)

    • Yesu ya warkar da wani makaho a Betsaida (22-26)

    • Bitrus ya ce Yesu ne Kristi (27-30)

    • Yesu ya ce za a kashe shi (31-33)

    • Almajiran Yesu na gaske (34-38)

  • 9

    • Kamannin Yesu ya canja (1-13)

    • An warkar da yaron da ke da aljani (14-29)

      • Kowane abu mai yiwuwa ne idan mutum yana da bangaskiya (23)

    • Yesu ya sake faɗa cewa za a kashe shi (30-32)

    • Almajiran Yesu sun yi gardama a kan wanda ya fi girma (33-37)

    • Duk wanda ba ya gāba da mu, yana tare da mu (38-41)

    • Abubuwan da ke sa mutane tuntuɓe (42-48)

    • “Ku kasance da gishiri a cikinku” (49, 50)

  • 10

    • Aure da kuma kashe aure (1-12)

    • Yesu ya albarkaci yara (13-16)

    • Tambayar wani mai arziki (17-25)

    • Sadaukarwa saboda Mulkin (26-31)

    • Yesu ya sake faɗa cewa za a kashe shi (32-34)

    • Abin da Yaƙub da Yohanna suka roƙi Yesu (35-45)

      • Yesu zai ba da ransa don mutane da yawa (45)

    • An warkar da wani makaho mai suna Bartimawus (46-52)

  • 11

    • Yesu ya shiga Urushalima a kan jaki (1-11)

    • Yesu ya laꞌanta itacen ɓaure (12-14)

    • Yesu ya tsabtace haikali (15-18)

    • Darasi daga itacen ɓaure da ya bushe (19-26)

    • An tambayi Yesu wa ya ba shi iko (27-33)

  • 12

    • Misalin manoma masu kisa (1-12)

    • Allah da Kaisar (13-17)

    • Tambaya game da tashin matattu (18-27)

    • Dokoki biyu mafi girma (28-34)

    • Kristi ɗan Dauda ne? (35-37a)

    • Gargaɗin da Yesu ya yi game da marubuta (37b-40)

    • Tsabar kuɗi biyu na matar da mijinta ya mutu (41-44)

  • 13

    • ALAMUN ƘARSHEN ZAMANI (1-37)

      • Yaƙe-yaƙe, girgizar ƙasa, da ƙarancin abinci (8)

      • Za a yi waꞌazin labari mai daɗi (10)

      • Ƙunci mai girma (19)

      • Zuwan Ɗan mutum (26)

      • Misalin itacen ɓaure (28-31)

      • Ku zauna da shiri (32-37)

  • 14

    • Firistoci sun ƙulla su kashe Yesu (1, 2)

    • An zuba wa Yesu mān ƙamshi (3-9)

    • Yahuda ya ci amanar Yesu (10, 11)

    • Bikin Ƙetarewa na ƙarshe (12-21)

    • Yesu ya kafa Abincin Yamma na Ubangiji (22-26)

    • Yesu ya ce Bitrus zai yi mūsun sanin sa (27-31)

    • Yesu ya yi adduꞌa a Getsemani (32-42)

    • An kama Yesu (43-52)

    • An yi masa shariꞌa a gaban membobin Sanhedrin (53-65)

    • Bitrus ya yi mūsun sanin Yesu (66-72)

  • 15

    • Yesu a gaban Bilatus (1-15)

    • An yi wa Yesu baꞌa a gaban jamaꞌa (16-20)

    • An rataye shi a kan gungume a Golgota (21-32)

    • Mutuwar Yesu (33-41)

    • An binne Yesu (42-47)

  • 16

    • An ta da Yesu (1-8)

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba