Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)

Abubuwan da Ke Cikin Littafin Luka

LUKA

ABUBUWAN DA KE CIKIN LITTAFIN NAN

  • 1

    • Abin da ya gaya wa Tiyofilus (1-4)

    • Jibraꞌilu ya faɗa cewa za a haifi Yohanna Mai Baftisma (5-25)

    • Jibraꞌilu ya faɗa cewa za a haifi Yesu (26-38)

    • Maryamu ta ziyarci Alisabatu (39-45)

    • Maryamu ta yabi Jehobah (46-56)

    • An haifi Yohanna kuma an ba shi suna (57-66)

    • Annabcin da Zakariya ya yi (67-80)

  • 2

    • Haifuwar Yesu (1-7)

    • Malaꞌiku sun fito wa makiyaya (8-20)

    • An yi wa Yesu kaciya kuma an tsarkake shi (21-24)

    • Simeyon ya ga Kristi (25-35)

    • Anna ta yi magana game da yaron (36-38)

    • Sun koma Nazaret (39, 40)

    • Yesu a haikali saꞌad da yake da shekara goma sha biyu (41-52)

  • 3

    • Lokacin da Yohanna ya soma hidimarsa (1, 2)

    • Yohanna yana gaya wa mutane su yi baftisma (3-20)

    • An yi wa Yesu baftisma (21, 22)

    • Tarihin Yesu Kristi (23-38)

  • 4

    • Ibilis ya gwada Yesu (1-13)

    • Yesu ya soma waꞌazi a Galili (14, 15)

    • An ƙi gaskata da Yesu a Nazaret (16-30)

    • Yesu yana majamiꞌa a Kafarnahum (31-37)

    • An warkar da mamar matar Siman da kuma wasu (38-41)

    • Jamaꞌa sun sami Yesu a wurin da babu kowa (42-44)

  • 5

    • Yesu ya yi muꞌujizar da ta sa aka kama kifaye da yawa; almajiransa na farko (1-11)

    • An warkar da wani kuturu (12-16)

    • Yesu ya warkar da wani mutum da jikinsa ya shanye (17-26)

    • Yesu ya kira Lawi (27-32)

    • Tambaya game da yin azumi (33-39)

  • 6

    • Yesu “Ubangiji ne na Assabaci” (1-5)

    • An warkar da mutumin da hannunsa ya shanye (6-11)

    • Manzannin Yesu goma sha biyu (12-16)

    • Yesu ya yi koyarwa da kuma warkarwa (17-19)

    • Farin ciki da kaito (20-26)

    • Ku ƙaunaci abokan gābanku (27-36)

    • Ku daina shariꞌanta mutane (37-42)

    • Ana gane itace ta wajen ꞌyaꞌyansa (43-45)

    • Gidan da aka gina da kyau da gidan da bai da tushe mai kyau (46-49)

  • 7

    • Bangaskiyar da wani jamiꞌin soja ya nuna (1-10)

    • Yesu ya ta da ɗan wata mata a Nayin da mijinta ya mutu (11-17)

    • An yabi Yohanna Mai Baftisma (18-30)

    • Yesu ya tsawata wa zamanin da suka ƙi saurarar sa (31-35)

    • An gafarta ma wata mata mai zunubi (36-50)

      • Misalin waɗanda suka karɓi bashi (41-43)

  • 8

    • Matan da suke bin Yesu (1-3)

    • Misalin mai shuki (4-8)

    • Abin da ya sa Yesu ya yi amfani da misalai (9, 10)

    • Ya bayyana maꞌanar misalin mai shuki (11-15)

    • Ba a rufe fitila (16-18)

    • Mamar Yesu da kuma ꞌyanꞌuwansa (19-21)

    • Yesu ya dakatar da iska mai ƙarfi (22-25)

    • Yesu ya tura aljanu su shiga jikin aladu (26-39)

    • ꞌYar Yayirus; wata mata ta taɓa mayafin Yesu (40-56)

  • 9

    • Yesu ya ba wa almajiransa goma sha biyu umurnin yin waꞌazi (1-6)

    • Hirudus ya rikice saboda Yesu (7-9)

    • Yesu ya ciyar da maza dubu biyar (10-17)

    • Bitrus ya ce Yesu ne Kristi (18-20)

    • Yesu ya ce za a kashe shi (21, 22)

    • Almajiran Yesu na gaske (23-27)

    • Kamannin Yesu ya canja (28-36)

    • An warkar da yaron da ke da aljani (37-43a)

    • Yesu ya sake faɗa cewa za a kashe shi (43b-45)

    • Almajiran Yesu sun yi gardama a kan wanda ya fi girma (46-48)

    • Duk wanda ba ya gāba da mu yana tare da mu (49, 50)

    • Mutanen wani ƙauye a Samariya sun ƙi Yesu (51-56)

    • Yadda za a bi Yesu (57-62)

  • 10

    • Yesu ya aika almajiransa sabaꞌin (1-12)

    • Kaiton biranen da suka ƙi tuba (13-16)

    • Almajiran Yesu sabaꞌin sun dawo (17-20)

    • Yesu ya yaba wa Ubansa don gatan da ya ba wa masu sauƙin kai (21-24)

    • Misalin mutumin Samariya mai kirki (25-37)

    • Yesu ya ziyarci Marta da Maryamu (38-42)

  • 11

    • Yadda za a yi adduꞌa (1-13)

      • Adduꞌar da Yesu ya koyar (2-4)

    • An fitar da aljanu da yatsar Allah (14-23)

    • Yadda ruhu mai ƙazanta ke dawowa (24-26)

    • Farin ciki na gaske (27, 28)

    • Alamar Yunana (29-32)

    • Fitilar jiki (33-36)

    • Kaiton munafukai (37-54)

  • 12

    • Yistin Farisiyawa (1-3)

    • Ku ji tsoron Allah, ba mutane ba (4-7)

    • Mutumin da ya ce ya san Kristi (8-12)

    • Misalin mai arziki marar wayo (13-21)

    • Ku daina yawan damuwa (22-34)

      • Ƙaramin garke (32)

    • Yin tsaro (35-40)

    • Bawa mai aminci da kuma bawa marar aminci (41-48)

    • Ba salama ba, amma rashin haɗin kai (49-53)

    • Muhimmancin gane abin da yake faruwa a lokacin nan (54-56)

    • Yadda za a sasanta (57-59)

  • 13

    • Ku tuba ko a hallaka ku (1-5)

    • Misalin itacen ɓaure marar ꞌyaꞌya (6-9)

    • An warkar da wata gurguwa a Ranar Assabaci (10-17)

    • Misalin ƙwayar mastad da kuma yisti (18-21)

    • Ana bukatar ƙoƙari domin a shiga ta ƙaramar ƙofa (22-30)

    • Hirudus, “karen dajin nan” (31-33)

    • Yesu ya tausaya wa Urushalima (34, 35)

  • 14

    • An warkar da wani mutum mai ciwon kumburi a Ranar Assabaci (1-6)

    • Ka ƙasƙantar da kanka idan aka gayyace ka (7-11)

    • Ka gayyaci waɗanda ba za su iya biyan ka ba (12-14)

    • Misalin waɗanda aka gayyace su kuma suka ƙi zuwa (15-24)

    • Abin da zai sa mutum ya cancanci zama almajirin Yesu (25-33)

    • Gishiri da ya rasa ɗanɗanonsa (34, 35)

  • 15

    • Misalin tunkiyar da ta ɓata (1-7)

    • Misalin tsabar kuɗi da ya ɓata (8-10)

    • Misalin ɗa da ya ɓata (11-32)

  • 16

    • Misalin bawa marar adalci (1-13)

      • ‘Wanda za a iya amince da shi a ƙaramin abu, za a iya amince da shi a babban abu’ (10)

    • Doka da kuma Mulkin Allah (14-18)

    • Misalin mutum mai arziki da kuma Liꞌazaru (19-31)

  • 17

    • Tuntuɓe, gafartawa, da kuma bangaskiya (1-6)

    • Bayin da ba su cancanci yabo ba (7-10)

    • An warkar da kutare goma (11-19)

    • Zuwan Mulkin Allah (20-37)

      • “Mulkin Allah yana tsakaninku” (21)

      • “Ku tuna da matar Lutu” (32)

  • 18

    • Misalin matar da mijinta ya mutu da ta ci-gaba da nacewa (1-8)

    • Bafarisi da mai karɓan haraji (9-14)

    • Yesu da ƙananan yara (15-17)

    • Tambayar wani mai mulki da ke da arziki (18-30)

    • Yesu ya sake faɗa cewa za a kashe shi (31-34)

    • An warkar da wani makaho mai bara (35-43)

  • 19

    • Yesu ya ziyarci Zakka (1-10)

    • Misalin kuɗin mina goma (11-27)

    • Yesu ya shiga Urushalima a kan jaki (28-40)

    • Yesu ya yi kuka don Urushalima (41-44)

    • Yesu ya tsabtace haikali (45-48)

  • 20

    • An tambayi Yesu wa ya ba shi iko (1-8)

    • Misalin manoma masu kisa (9-19)

    • Allah da Kaisar (20-26)

    • Tambaya game da tashin matattu (27-40)

    • Kristi ɗan Dauda ne? (41-44)

    • Gargaɗin da Yesu ya yi game da marubuta (45-47)

  • 21

    • Tsabar kuɗi biyu na matar da mijinta ya mutu (1-4)

    • ALAMUN ABUBUWAN DA ZA SU FARU (5-36)

      • Yaƙe-yaƙe, girgizar ƙasa, annoba, ƙarancin abinci (10, 11)

      • Sojoji za su kewaye Urushalima (20)

      • Lokacin alꞌummai (24)

      • Zuwan Ɗan mutum (27)

      • Misalin itacen ɓaure (29-33)

      • “Ku zauna a shirye” (34-36)

    • Yesu yana yin koyarwa a haikali (37, 38)

  • 22

    • Firistoci sun ƙulla su kashe Yesu (1-6)

    • Shiri don Bikin Ƙetarewa na ƙarshe (7-13)

    • Yesu ya kafa Abincin Yamma na Ubangiji (14-20)

    • “Wanda zai ci amanata yana cin abinci tare da ni a teburi” (21-23)

    • Gardama sosai a kan wanda ya fi girma (24-27)

    • Yesu ya yi yarjejeniya game da wani mulki (28-30)

    • Yesu ya ce Bitrus zai yi mūsun sanin sa (31-34)

    • Yesu ya gaya wa mabiyansa su yi shiri; takubba biyu (35-38)

    • Adduꞌar da Yesu ya yi a Tudun Zaitun (39-46)

    • An kama Yesu (47-53)

    • Bitrus ya yi mūsun sanin Yesu (54-62)

    • An yi wa Yesu baꞌa (63-65)

    • An yi masa shariꞌa a gaban membobin Sanhedrin (66-71)

  • 23

    • Yesu a gaban Bilatus da Hirudus (1-25)

    • An rataye Yesu a kan gungume tare da mutane biyu masu laifi (26-43)

      • “Za ka kasance tare da ni a Aljanna” (43)

    • Mutuwar Yesu (44-49)

    • An binne Yesu (50-56)

  • 24

    • An ta da Yesu (1-12)

    • A kan hanyar zuwa Imawus (13-35)

    • Yesu ya bayyana ga almajiransa (36-49)

    • Allah ya ɗauki Yesu zuwa sama (50-53)

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba