Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • rq darasi na 2 pp. 4-5
  • Wanene Allah?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wanene Allah?
  • Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Fada Game da Allah da Kuma Kristi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
  • Wane Ne Allah na Gaskiya?
    Albishiri Daga Allah!
  • Ka Girmama Jehovah Domin Shi ne Allah Makaɗaici na Gaskiya
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Wane Ne Allah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
rq darasi na 2 pp. 4-5

Darasi na 2

Wanene Allah?

Wanene Allah na gaskiya, kuma minene sunansa? (1, 2)

Wane irin jiki ya ke da shi? (3)

Minene ingancinsa na musamman? (4)

Ashe ya kamata mu yi amfani da siffofi da alamu cikin sujadarmu gareshi? (5)

Ina hanyoyi biyu da zamu iya koya game da Allah? (6)

1. Mutane suna bauta ma abubuwa dayawa. Amma Littafi Mai-Tsarki ya gaya mana cewa Allah na GASKIYA ɗaya ne kaɗai. Ya halicci dukan abubuwan da ke sama da ƙasa. Domin ya ba mu rai, shi kaɗai ne Wanda ya kamata mu yi wa sujada.​—1 Korinthiyawa 8:​5, 6; Ru’ya ta Yohanna 4:11.

2. Allah yana da lakabi dayawa amma sunan sa na gaskiya ɗaya ne. Wannan sunan shine JEHOVAH. An riga an cire sunan Allah kuma sa lakabi kamar UBANGIJI ko kuwa ALLAH cikin yawancin Littafi Mai-Tsarki. Amma lokacinda aka rubuta Littafi Mai-Tsarki, sunan Jehovah ya bayana sau 7,000!​—​Fitowa 3:15; Zabura 83:18.

3. Jehovah yana da jiki, amma ba kamar namu ba. “Allah Ruhu ne,” in ji Littafi Mai-Tsarki. (Yohanna 4:24) Ruhu wani irin rai ne da ke fiye da namu sosai. Babu ɗan-Adam da ya taba ganin Allah. Mazaunin Jehovah a sama ne, amma yana ganin dukan abubuwa. (Zabura 11:​4, 5; Yohanna 1:18) To, minene fa ruhu mai-tsarki? Ba wani ne kamar Allah ba. Maimako fa, ikon aikin Allah ne.​—Zabura 104:30.

4. Littafi Mai-Tsarki ya bayana mana mutumtakar Jehovah. Ya bayana cewa shahararrun ingancinsa, ƙauna, shari’a, da kuma iko ne. (Kubawar Shari’a 32:4; Ayuba 12:13; Ishaya 40:26; 1 Yohanna 4:8) Littafi Mai-Tsarki ya kuma gaya mana cewa yana da jinƙai, alheri, gafartawa, mai-karamci ne, da kuma haƙuri. Mu, kamar yara masu biyayya, ya kamata mu yi ƙoƙarin yin koyi da shi.​—Afisawa 5:​1, 2.

5. Shin ya kamata mu durkusa ko kuwa yi addu’a ga siffofi, hotuna, ko kuwa alamu cikin sujadarmu? Babu! (Fitowa 20:​4, 5) Jehovah ya ce tilas ne mu yi sujada gareshi kaɗai. Ba zai yi rabon ɗaukakarsa da kowa ko wani abu ba. Siffofi ba su da ikon taimakonmu.​—Zabura 115:​4-8; Ishaya 42:8.

6. Ta yaya zamu zo ga sanin Allah sosai? Hanya ɗaya ita ce ta wurin lura da abubuwan da ya halitta kuma yi bimbini sosai game da abinda suke nufi garemu. Halittun Allah na nuna mana cewa yana da iko da kuma hikima sosai. Muna ganin ƙaunarsa cikin dukan abubuwan da ya yi. (Zabura 19:​1-6; Romawa 1:20) Wata hanya da zamu iya koya game da Allah shine ta wurin nazarta Littafi Mai-Tsarki. A cikinsa fa yakan gaya mana ƙarin abubuwa game da irin Allah da ya ke. Yana kuma gaya mana game da ƙudurinsa da kuma abin da ya ke son mu yi.​—Amos 3:7; 2 Timothawus 3:​16, 17.

[Hoto a shafi na 5]

Muna koya game da Allah daga halittu kuma daga Littafi Mai-Tsarki

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba