Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • yc darasi na 4 pp. 10-11
  • Ta Sa Babanta da Jehobah Farin Ciki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Sa Babanta da Jehobah Farin Ciki
  • Ku Koyar da Yaranku
  • Makamantan Littattafai
  • Allah da Kuma Abokanta Sun Ƙaunace Ta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Alkawarin Jephthah
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Allah Yana Albarkar Wadanda Suka Kasance da Aminci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Alkawarin da Jephthah Ya Yi
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Ku Koyar da Yaranku
yc darasi na 4 pp. 10-11
Jephthah yana tare da ’yarsa sa’ad da take karama

DARASI NA 4

Ta Sa Babanta da Jehobah Farin Ciki

Jephthah yana addu’a ga Jehovah yayin da Isra’ilawa suke yaki da makiyansu

Wane alkawari ne Jephthah ya yi wa Jehobah?

Jephthah yana dawowa daga yaki kuma ya rungumi ’yarsa da ta zo ta marabce shi

’Yar Jephthah ta cika alkawarin babanta, ko da yake hakan bai yi mata sauki ba

Ka ga yarinyar da ke cikin wannan hoton?— Ita yarinyar wani mutumi ne mai suna Jephthah. Littafi Mai Tsarki bai faɗi sunanta ba, amma mun san cewa ta sa babanta da kuma Jehobah farin ciki. Yanzu za mu koya game da ita da kuma babanta Jephthah.

Jephthah mutumin kirki ne kuma ya koya wa ’yarsa game da Jehobah sosai. Shi mutumi ne mai ƙarfi da kuma shugaba mai kyau. Shi ya sa Isra’ilawa suka ce ya zama shugabansu a lokacin da za su je su yaƙi maƙiyansu.

Jephthah ya yi addu’a cewa Allah ya taimake shi ya ci nasara. Jephthah ya yi alkawari cewa idan suka ci yaƙin, zai ba Jehobah duk wanda ya fara fitowa daga cikin gidansa sa’ad da ya dawo. Wannan mutumin zai zauna kusa da mazaunin Allah kuma ya riƙa aiki a cikin mazaunin duk rayuwarsa. Mazauni wuri ne da mutane suke zuwa su bauta wa Allah a lokacin. Ka san wani abu ne? Jephthah ya ci nasara a yaƙin! Ka san wanda ya fara fitowa sa’ad da Jephthah ya dawo gida?—

Yarinyar Jephthah ce! Ita kaɗai ya haifa, kuma yanzu dole ne Jephthah ya rabu da ita. Hakan ya sa shi baƙin ciki sosai. Amma, ka tuna cewa ya riga ya yi alkawari. Nan da nan sai yarinyar ta ce: ‘Baba, ka riga ka yi wa Jehobah alkawari, sai ka cika.’

’Yar Jephthah tana tattara itatuwa a mazaunin; kawayenta sun kawo mata ziyara

Kowace shekara, kawayen ’yar Jephthah suna zuwa wajenta su gaishe ta

’Yar Jephthah ma ta yi baƙin ciki sosai. Me ya sa? Domin a mazaunin, ba za ta iya yin aure ba balle ma ta haihu. Amma, tana son babanta ya cika alkawarinsa kuma tana so ta sa Jehobah farin ciki. Ta fi son hakan maimakon ta yi aure ko kuma ta haihu. Sai ta bar gida kuma ta soma aiki a mazaunin duk rayuwarta.

Kana ganin abin da ta yi ya sa babanta da Jehobah farin ciki?— E, haka ne! Idan kana biyayya kuma kana ƙaunar Jehobah, za ka zama kamar ’yar Jephthah. Kai ma za ka sa iyayenka da Jehobah farin ciki sosai.

KARANTA NASSOSIN NAN

  • Kubawar Shari’a 6:4-6

  • Alƙalawa 11:30-40

TAMBAYOYI:

  • Wane ne Jephthah? Wane alkawari ne ya yi?

  • Me ya sa bai yi wa ’yar Jephthah sauƙi ta cika alkawarin da babanta ya yi ba?

  • Mene ne ’yar Jephthah ta fi so ta yi?

  • Ta yaya za ka bi misalin ’yar Jephthah?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba