WAƘA TA 1
Babu Wani Kamar Jehobah
Hoto
(Ru’ya ta Yohanna 4:11)
1. Jehobah Allah, Mai iko duka,
Mahaliccin rai, rana da taurari.
Sararin sama da duniyar nan,
Za su wanzu har abada fa.
2. Sarautar Allah, babu kamarta.
Kai ka koya mana duk dokokinka.
Karanta Kalmarka na sa mu yi
Hikima da hankali sosai.
3. Ƙauna kyauta ce mai muhimmanci,
Mun gode Allah domin wannan kyauta.
Halayenka har da sunanka ma,
Za mu yi shelar su da ƙwazo.
(Ka kuma duba Zab. 36:9; 145:6-13; M. Wa. 3:14; Yaƙ. 1:17.)