Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb24 Satumba pp. 2-3
  • 2-8 ga Satumba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • 2-8 ga Satumba
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2024
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2024
mwb24 Satumba pp. 2-3

2-8 GA SATUMBA

ZABURA 79-81

Waƙa ta 29 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. Ku Zama Masu Ƙaunar Sunan Jehobah

(minti 10)

Ku guji ayyuka da ke ɓata sunan Jehobah (Za 79:9; w17.02 9 sakin layi na 5)

Ku riƙa amfani da sunan Jehobah (Za 80:18; ijwbv-E 3 sakin layi na 4-5)

Jehobah zai yi wa waɗanda suke masa biyayya da kuma ƙaunar sunansa albarka (Za 81:​13, 16)

Wani danꞌuwa yana ba ma wani abokin aikinsa katin jw.org saꞌad da suke hutawa a wurin aiki.

Don halinmu ya ɗaukaka sunan Jehobah, wajibi ne mu sa mutane su san cewa mu Shaidunsa ne

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • Za 80:1—Me ya sa a wasu lokuta ake amfani da sunan Yusuf saꞌad da ake magana game da dukan ƙabilun Israꞌila? (it-2-E 111)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) Za 79:1–80:7 (th darasi na 10)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 1) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Ka tambayi mutumin ko zai so a yi nazari da shi. (lmd darasi na 4 batu na 4)

5. Fara Magana da Mutane

(minti 3) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka tambayi mutumin ko zai so a yi nazari da shi. (lmd darasi na 4 batu na 3)

6. Fara Magana da Mutane

(minti 2) WAꞌAZI A INDA JAMAꞌA SUKE. Ka tambayi mutumin ko zai so a yi nazari da shi. (lmd darasi na 3 batu na 3)

7. Komawa Ziyara

(minti 5) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Ka nuna wa wani mutum da ya taɓa ƙin yin nazari yadda muke gudanar da nazari. (lmd darasi na 8 batu na 3)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 10

8. Za Su Tsarkake Sunana

(minti 15) Tattaunawa.

Shaiɗan ya soma ɓata sunan Jehobah a lambun Adnin. Tun daga lokacin, ɗaukaka sunan Jehobah ya zama batu mafi muhimmanci ga ꞌyan Adam da kuma malaꞌiku.

Ga wasu ƙaryace-ƙaryacen da Shaiɗan ya yi game da Jehobah. Ya zarge Shi cewa ba ya ƙaunar bayinsa kuma ba ya jin tausayin su. (Fa 3:​1-6; Ayu 4:​18, 19) Ya kuma ce bayin Jehobah ba sa ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarsu. (Ayu 2:​4, 5) Ya riga ya ruɗi miliyoyin mutane cewa ba Jehobah ba ne ya halicci wannan duniyar da halittun da ke ciki.—Ro 1:​20, 21.

Yaya kake ji game da waɗannan ƙaryace-ƙaryacen? Wataƙila, hakan zai sa ka ƙuduri niyyar goyon bayan Jehobah! Jehobah ya san cewa mutanensa za su so su tsarkake sunansa. (Ka duba Ishaya 29:23.) Ta yaya za ka taimaka wajen yin hakan?

  • Ka taimaka wa mutane su san Jehobah kuma su ƙaunace Shi. (Yoh 17:​25, 26) Ka kasance a shirye don ka tabbatar wa mutane cewa Jehobah Allah ne na gaske, kuma ka koya musu game da halayensa masu kyau.—Ish 63:7

  • Ka ƙaunaci Jehobah da dukan zuciyarka. (Mt 22:​37, 38) Ka bi umurnin Jehobah domin kana so ka faranta masa rai, ba don za su amfane ka kawai ba.—K. Ma 27:11.

Hotuna: Hotuna daga bidiyon “Ku Nuna Kaunar da Ba Ta Karewa Ko Da . . . Kuna Fuskantar Mummunan Tasiri a Makaranta.” 1. Ariel tana zaune a kujeranta a aji, sai wani dan ajinsu yana nuna da yasa yana tambayar ta dalilin da ya sa ba ta tsara wa tuta. 2. Tana amfani da Littafi Mai Tsarki da kuma darasi na 61 na littafin “Darussa daga Littafi Mai Tsarki don ta yi nazari. 3.Tana tsaya a gaban ꞌyan ajinsu tana waꞌazi . 4. Wani ꞌyan ajin su Diego yana ba shi sigari. 5. Yana amfani da babbar waya wajen yin bincike. 6.Yana dawowa daga makaranta, da murmushi yana tafiya babu tsoro.

Ku kalli BIDIYON Ku Nuna Kaunar da Ba Ta Karewa Ko Da . . . Kuna Fuskantar Mummunan Tasiri a Makaranta. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Ta yaya Ariel da Diego suka kāre sunan Jehobah?

  • Me ya sa suka goyi bayan Jehobah?

  • Ta yaya za ka iya yin koyi da su?

9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

(minti 30) kr babi na 15 sakin layi na 29-36, da akwatin da ke shafi na 167

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 90 da Adduꞌa

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba