14-20 GA YULI
KARIN MAGANA 22
Waƙa ta 79 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. Shawarwari Masu Kyau don Renon Yara
(minti 10)
Ku taimaka wa yaranku su zama a shirye don su iya magance matsaloli a nan gaba (K. Mag. 22:3; w20.10 shafi na 27 sakin layi na 7)
Ku soma koyar da yaranku tun suna ƙanana (K. Mag. 22:6; w19.12 26 sakin layi na 17-19)
Ku nuna ƙauna saꞌad da kuke koyar da su (K. Mag. 22:15; w15 11/15 shafi na 5 sakin layi na 6)
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
K. Mag. 22:29—Ta yaya za mu yi amfani da wannan ayar saꞌad da muke yin ayyukan ikilisiya, kuma mene ne amfanin yin hakan? (w21.08 shafi na 22 sakin layi na 11)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) K. Mag. 22:1-19 (th darasi na 10)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 3) WAꞌAZI GIDA-GIDA. (lmd darasi na 5 batu na 4)
5. Fara Magana da Mutane
(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka nuna wa mutumin yadda zai sami bayanai da suke taimaka wa iyaye a dandalin jw.org/ha (lmd darasi na 1 batu na 4)
6. Jawabi
(minti 5) ijwyp talifi na 100—Jigo: Me Zan Yi Idan Na Taka Dokar Iyayena? (th darasi na 20)
Waƙa ta 134
7. Ku Yi Haƙuri Saꞌad da Kuke Yin Horo, Amma Kada Ku Yi Sakaci
(minti 15) Tattaunawa.
Iyaye suna bukatar haƙuri sosai saꞌad da suke renon yaransu. Wajibi ne iyaye su dinga kasancewa da yaransu don su tattauna da su kullum, kuma kada su yi hakan cikin hanzari. (M. Sha. 6:6, 7) Don iyaye su san abin da yaransu suna tunani a kai, wajibi ne su yi musu tambayoyi kuma su saurare su sosai. (K. Mag. 20:5) Kafin yara su fahimci abin da suke koya kuma su aikata shi, wajibi ne iyaye su riƙa maimaita umurnin da suke bayarwa.
Amma iyaye da suke da haƙuri ba sa sakaci. Jehobah ya ba iyaye hakkin koyar da yaransu abin da ya kamata su yi da wanda bai kamata su yi ba. Ban da haka ma, su suke da hakkin horar da yaransu idan ba su bi umurninsu ba.—K. Mag. 6:20; 23:13.
Karanta Afisawa 4:31. Sai ka tambayi masu sauraro:
Me ya sa bai kamata iyaye su horar da yaransu da fushi ba?
Karanta Galatiyawa 6:7. Sai ka tambayi masu sauraro:
Me ya sa yake da muhimmanci iyaye su koya wa yaransu cewa abin da suka shuka, shi za su girbe?
Ku kalli BIDIYON “Da Haƙuri, . . . Ku Yarda da Juna Cikin Ƙauna”—Yaranku. Sai ka tambayi masu sauraro:
Waɗanne darussa ne kuka koya daga bidiyon nan?
8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) lfb “Wasiƙa Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah,” gabatarwar sashe na 1 da kuma darasi na 1