6-12 GA OKTOBA
MAI-WAꞌAZI 5-6
Waƙa ta 42 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
Wasu ꞌyan Israꞌila suna sauraro yayin da wani firist yana bayyana musu Dokar Allah a kofar birnin
1. Yadda Muke Girmama Ubanmu Jehobah
(minti 10)
Muna girmama Jehobah a taro ta wurin sauraro da kuma saka tufafi da yin ado mai kyau (M. Wa 5:1; w08 8/15 15-16 sakin layi na 17-18)
Idan muna adduꞌa a cikin jamaꞌa, bai kamata adduꞌar ta yi dogo ba, kuma abin da za mu faɗa ya nuna muna girmama Jehobah (M. Wa 5:2; w09 11/15 11 sakin layi na 21)
Mu cika alkawarin da muka yi na bauta wa Jehobah (M. Wa 5:4-6; w17.04 6 sakin layi na 12)
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
M. Wa 5:8—Ta yaya wannan ayar za ta ƙarfafa mu idan muka fuskanci rashin adalci? (w20.09 31 sakin layi na 3-5)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) M. Wa 5:1-17 (th darasi na 12)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 1) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Mutumin yana so ya yi gardama da kai. (lmd darasi na 4 batu na 5)
5. Fara Magana da Mutane
(minti 2) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka tattauna da mutumin wani batu daga “Gaskiyar da Muke Jin Daɗin Koya wa Mutane” da ke ƙarin bayani na 1 na ƙasidar Ƙaunar Mutane. (lmd darasi na 1 batu na 3)
6. Komawa Ziyara
(minti 3) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Ka nuna wa mutumin wani bidiyo daga Kayan Aiki don Koyarwa. (lmd darasi na 7 batu na 3)
7. Almajirtarwa
(minti 5) lff darasi na 17 da batu na 1-3 (lmd darasi na 11 batu na 3)
Waƙa ta 160
8. Shin Kuna Amfani da “Gaskiyar da Muke Jin Daɗin Koya wa Mutane” Kuwa?
(minti 15) Tattaunawa.
Tun lokacin da aka fitar da ƙasidar nan Ƙaunar Mutane Za Ta Sa Ka Almajirtar da Su, ƙasidar ta taimaka mana mu inganta yadda muke tattaunawa da mutane a waꞌazi. An tsara Ƙarin Bayani Na 1 musamman don ya taimaka mana mu iya yin waꞌazi a hanya mai sauƙi. (Ibr 4:12) Shin ka san batutuwa tara da ke ƙarƙashin jigon nan “Gaskiyar da Muke Jin Daɗin Koya wa Mutane”?
Idan kana tattaunawa da wani, ta yaya za ka san lokacin da ya dace ka gaya masa wata gaskiya daga Littafi Mai Tsarki?—lmd ƙarin bayani na 1
Waɗanne batutuwa ne mutanen da ke yankinku suka fi so?
Me za ka iya yi don ka saba da nassosin da ke ƙarin bayani na 1?
Idan muna amfani da nassosin nan a kullum, za mu saba da su. Amma kafin mu sami damar yin amfani da nassosin, dole mu nemi mutane da za mu tattauna da su a yankinmu.
Ku kalli BIDIYON “Karfe Yakan Wasa Karfe”—Yin Waꞌazi a Koꞌina. Sai ka tambayi masu sauraro:
Me zai taimaka mana mu sami mutane da yawa da za mu tattauna da su a yankinmu?
9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) lfb darasi na 24-25