Darasi na 7
Jawowa Kurkusa da Allah Cikin Addu’a
Me yasa muhimmin abu ne a yi addu’a kullayaumi? (1)
Ga wanene ya kamata mu yi addu’a, kuma ta yaya? (2, 3)
Wane batu ne sun dace don addu’a? (4)
Wane lokaci ya kamata ka yi addu’a? (5, 6)
Ashe Allah yana jin dukan addu’o’i ne? (7)
1. Addu’a shine yin magana da Allah cikin tawali’u. Ka yi addu’a ga Allah kullayaumi. Hakanan zaka yi kusa da shi kamar aboki na sarai. Jehovah yana da girma da kuma iko, duk da haka yana jin addu’o’inmu! Kana addu’a ga Allah kullayaumi?—Zabura 65:2; 1 Tassalunikawa 5:17.
2. Addu’a wata sashen sujadarmu ne. Saboda haka, sai mu yi addu’a ga Allah, Jehovah, ne kadai. Lokacinda Yesu ke duniya, yakan yi addu’a kullum ga Ubansa, ba ga wani dabam ba. Sai mu yi haka nan. (Matta 4:10; 6:9) Amma dai, ya kamata mu yi dukan addu’o’inmu a cikin sunan Yesu. Wannan yana nuna cewa muna ladabi ga matsayin Yesu kuma cewa muna da bangaskiya cikin haɗayar fansa nasa.—Yohanna 14:6; 1 Yohanna 2:1, 2.
3. Yayinda muke addu’a ya kamata mu yi ma Allah magana daga zuciyarmu. Kada mu haddace addu’armu ko kuwa karanta shi daga wani littafin addu’a. (Matta 6:7, 8) Muna iya yin addu’a a cikin ladabi, kowane lokaci, da kuma a kowane wuri. Allah yana jin addu’a da muke yi cikin zuciyarmu ma. (1 Samuila 1:12, 13) Yana da kyau mu nemi wurin da babu mutane don mu yi addu’a na kai.—Markus 1:35.
4. Waɗanne abubuwa ne za ka yi addu’a game da su? Duk abinda zai tabi abokantakarka da shi. (Filibbiyawa 4:6, 7) Addu’an gurbi ya nuna cewa zamu yi addu’a game da sunan Jehovah da ƙudurinsa. Zamu iya roƙa ya tanadar da bukatunmu na jiki, ya gafarce mu, kuma taimake mu tsayayya ma jaraba. (Matta 6:9-13) Kada addu’armu shi zama na sonkai. Ya kamata mu yi addu’a don abubuwan da sun yi daidai da nufin Allah.—1 Yohanna 5:14.
5. Zaka iya addu’a duk lokacinda zuciyarka ta motsa ka ka gode wa Allah ko kuwa yabe shi. (1 Labarbaru 29:10-13) Ka yi addu’a yayinda ka ke da matsaloli da kuma lokacinda an jaraba bangaskiyarka. (Zabura 55:22; 120:1) Ya dace ka yi addu’a kafin ka ci abincinka. (Matta 14:19) Jehovah ya ce, mu yi addu’a a “kowane loto.”—Afisawa 6:18.
6. Muna bukatar addu’a musamman idan mun yi zunubi mai-girma. A waɗannan lokutta sai mu roƙi jinƙai da gafarar Jehovah. Idan mun bayana zunubanmu gareshi kuma yi iyakacin ƙoƙarinmu don kada mu maimaita shi, Allah “mai-hanzarin gafartawa” ne.—Zabura 86:5; Misalai 28:13.
7. Jehovah yana jin addu’ar masu-adilci ne kaɗai. Domin Allah ya ji addu’o’inka fa, tilas ne ka yi ƙoƙarin rayuwa bisa dokokinsa. (Misalai 15:29; 28:9) Dole ka kasance da tawali’u sa’anda ka ke yin addu’a. (Luka 18:9-14) Ya kamata ka aika cikin jituwa da abinda ka ke addu’a game da shi. Ta haka zaka nuna cewa kana da bangaskiya kuma kana nufin abinda ka faɗi da gaske. Sai ta haka ne kaɗai Jehovah zai amsa addu’o’inka.—Ibraniyawa 11:6.