BABI NA 19
“Hikima ta Allah Cikin Asiri”
1, 2. Wane “asiri” ne ya kamata mu so, kuma me ya sa?
ASIRAI! Domin suna ta da hankali, sau da yawa yana yi wa mutane wuya su riƙe. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ga Allah, ɗaukakarsa ita ce a rufe alꞌamari.” (Karin Magana 25:2) Hakika, tun da shi ne Mamallakin Duka kuma Mahalicci, Jehobah yana rufe wasu abubuwa daga mutane har sai lokaci ya kai ya bayyana su.
2 Amma, da akwai asiri mai ban mamaki da Jehobah ya bayyana a cikin Kalmarsa. An kira shi “asirin nufin [Allah].” (Afisawa 1:9) Sani game da shi zai yi fiye da cika burinka na son saninsa. Sani na wannan asirin zai kai ka ga ceto kuma zai ba ka fahimi cikin hikimar Jehobah marar iyaka.
An Bayyana Shi da Kaɗan Kaɗan
3, 4. Ta yaya annabci da aka rubuta a cikin Farawa 3:15 ya ba da bege, wane “asiri” ya ƙunsa?
3 Sa’ad da Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi, kamar dai nufin Jehobah na cewa kamiltattun mutane su zauna cikin aljanna ta duniya ya wargaje. Amma babu ɓata lokaci Allah ya warware matsalar. Ya ce: “Kai da macen, zan sa ƙiyayya tsakaninku, tsakanin zuriyarka da zuriyarta kuma. Shi zai murƙushe kanka, kai kuma za ka sari diddigen ƙafarsa.”—Farawa 3:15.
4 Waɗannan kalmomin suna da wuyar fahimtawa. Wacece wannan mace? Wanene macijin? Wanene “zuriyar” da zai ƙuje kan macijin? Adamu da Hauwa’u sai dai su yi zato. Duk da haka, kalmar Allah ta ba da bege ga dukan wani amintaccen ɗan waɗannan marasa aminci. Nagarta za ta yi nasara. Nufin Jehobah zai cika. Amma ta yaya? To, wannan ai shi ne asirin! Littafi Mai Tsarki ya kira shi “hikimar Allah wadda take a asirce, hikimar da dā a ɓoye take.”—1 Korintiyawa 2:7.
5. Ka ba da misalin abin da ya sa Jehobah yake bayyana asirinsa da kaɗan kaɗan.
5 Tun da “Mai Tone asiri” ne, Jehobah a ƙarshe zai ba da bayani dalla-dalla game da cika asirinsa. (Daniyel 2:28) Amma zai yi haka a hankali, da kaɗan kaɗan. Alal misali, za mu iya tunanin yadda uba mai ƙauna yake amsawa sa’ad da ɗansa ya yi tambaya, “Baba, ta yaya aka haife ni?” Uba mai hikima zai yi masa bayani iyakacin yadda yaron zai iya fahimta. Yayin da yaron ya ƙara girma, baban sai ya ba shi ƙarin bayani. Hakanan, Jehobah ne ya san lokacin da mutanensa ya kamata ya ba su bayani game da nufinsa.—Karin Magana 4:18; Daniyel 12:4.
6. (a) Mene ne muhimmancin alkawari? (b) Me ya sa abin mamaki ne cewa Jehobah yana yin alkawari da mutane?
6 Ta yaya Jehobah yake ba da irin wannan bayanin? Ya yi amfani da jerin alkawura, ya bayyana da yawansu. Wataƙila, ka taɓa sa hannu cikin wata yarjejeniya—ƙila don ka sayi gida ko kuma ka ari kuɗi ko kuma ka ba da bashi. Irin wannan alkawarin yana ɗauke da tabbaci cewa abin da aka yi dawajewa a kai za a cika. Amma me ya sa Jehobah yake bukatar ya yi alkawari da mutane? Hakika, kalmarsa ta isa tabbaci na alkawarinsa. Hakan gaskiya ne, duk da haka, sau da yawa Allah ya tabbatar da maganarsa da alkawari. Irin wannan alkawari mai ƙarfi yana ba mu mu mutane ajizai dalili mai ƙarfi na dogara ga alkawarin Jehobah.—Ibraniyawa 6:16-18.
Alkawari da Ibrahim
7, 8. (a) Wane alkawari Jehobah ya yi da Ibrahim, kuma wane bayani ya bayar game da asirin? (b) Ta yaya Jehobah da kaɗan kaɗan ya bayyana zuriyar Ɗa na alkawarin?
7 Fiye da shekaru dubu biyu bayan an kori mutum daga cikin Aljanna, Jehobah ya gaya wa bawansa mai aminci Ibrahim: “Zan mai da zuriyarka su yi yawa kamar taurarin sararin sama, . . . Ta wurin zuriyarka, dukan kabilun duniya za su roƙa wa kansu albarka, saboda ka yi biyayya ga abin da na ce maka ka yi.’ ” (Farawa 22:17, 18) Wannan ba alkawari ba ne kawai; Jehobah ya yi dawajewa ne kuma ya toƙare shi da rantsuwa. (Farawa 17:1, 2; Ibraniyawa 6:13-15) Lallai abin mamaki ne Mamallakin Dukan Halitta ya yi alkawarin zai albarkaci mutane!
“Zan mai da zuriyarka su yi yawa kamar taurarin sararin sama”
8 Alkawarin da ya yi da Ibrahim ya bayyana cewa Ɗan alkawarin zai kasance mutum, domin zai zama daga zuriyar Ibrahim. Amma zai kasance wanene? Da shigewar lokaci, Jehobah ya bayyana cewa ɗan Ibrahim Ishaƙu ne zai kasance kakan Ɗan. A tsakanin ’ya’yan Ishaƙu biyu, an zaɓi Yakubu. (Farawa 21:12; 28:13, 14) Daga baya, Yakubu ya furta wannan kalmomi na annabci bisa ɗaya cikin ’ya’yansa goma sha biyun: “Kai Yahuda, sandan iko ba zai rabu da hannunka ba, ko sandan mulki daga zuriyarka, domin a kawo maka haraji, kabilu kuma su yi maka biyayya.” (Farawa 49:10) Yanzu an sani cewa Ɗan zai zama sarki, wanda zai fito daga Yahuda!
Alkawari da Isra’ila
9, 10. (a) Wane alkawari Jehobah ya yi da al’umma ta Isra’ila, kuma wace kāriya wannan alkawari ya yi? (b) Ta yaya Dokar ta nuna bukatar fansa ta mutane ?
9 A shekara ta 1513 K.Z., Jehobah ya yi tanadin da ya gyara hanya domin ƙarin bayani game da asirin. Ya yi alkawari da zuriyar Ibrahim, al’ummar Isra’ila. Ko da yake a yanzu bai kasance ba, wannan Alkawari na Dokar Musa ɓangare ne mai muhimmanci na nufin Jehobah don kawo Ɗa na alkawarin. Ta yaya? Ka yi la’akari da hanyoyi uku. Na farko, Dokar tana kama da ganuwa ce ta kāriya. (Afisawa 2:14) Umurnanta na adalci sun kasance kamar katanga ne tsakanin Yahudawa da Mutanen wasu Al’ummai. Ta haka Dokar ta taimaka wajen tsare zuriyar Ɗa na alkawarin. Godiya ta tabbata ga wannan kāriyar, al’ummar ta kasance sa’ad da lokacin Allah ya yi da za a haifi Almasihu a ƙabilar Yahuda.
10 Na biyu, Dokar ta nuna bukatar da mutane suke da ita na fansa. Kamiltacciyar Doka, ta nuna kasawar mutane masu zunubi su bi ta daidai. Saboda haka, ta bayyana “domin a nuna mana zunubanmu a fili. An kawo ta da nufi cewa za a yi aiki da ita har ranar da zuriyar nan ta Ibrahim za ta zo, wadda dominsa ne aka yi alkawarin.” (Galatiyawa 3:19) Ta wajen hadayar dabbobi, Dokar ta yi tanadin kafarar zunubai. Amma tun dā, kamar yadda Bulus ya rubuta, “ba yadda zai yiwu jinin bijimai da na awaki ya kawar da zunubai,” waɗannan hadayu suna alamta hadayar fansa ce ta Kristi. (Ibraniyawa 10:1-4) Ga Yahudawa masu aminci, wannan alkawarin ya kasance domin ya “kai mu ga Almasihu.”—Galatiyawa 3:24.
11. Wane bege Dokar alkawari ta bai wa Isra’ila, amma me ya sa wannan al’ummar gabaki ɗayanta ta yi hasara?
11 Na uku, wannan alkawarin ya ba wa al’ummar Isra’ila bege mai girma. Jehobah ya gaya musu idan suka kasance amintattu ga alkawarin, za su zama ‘mulki na firistoci kuma, al’umma mai tsarki.’ (Fitowa 19:5, 6) Isra’ila ta jiki a ƙarshe ta yi tanadin mutane na farko waɗanda suke cikin mulkin firistoci na sama. Duk da haka, gabaki ɗayanta, Isra’ila ta yi wa Dokar alkawarin tawaye, ta ƙi Ɗa Almasihun, ta yi hasarar wannan begen. To, su waye za su cika wannan mulkin firistoci? Kuma ta yaya wannan al’umma mai albarka za ta kasance da nasaba da Ɗa na alkawarin? Wannan ɓangaren asirin za a bayyana shi a nan gaba a lokaci na Allah.
Alkawarin Mulki da Dauda
12. Wane alkawari Jehobah ya yi da Dauda, kuma wane bayani ya ƙara yi game da asirin Allah?
12 A ƙarni na 11 K.Z., Jehobah ya ƙara ba da bayani game da asirin sa’ad da ya yi wani alkawari. Ya yi wa Sarki Dauda mai aminci alkawari: “Zan tā da ɗaya daga cikin ’ya’yanka waɗanda ka haifa ya zama sarki. Zan kuma kafa mulkinsa ya yi ƙarfi sosai. . . . Zan kafa kujerar mulkinsa har abada.” (2 Sama’ila 7:12, 13; Zabura 89:3) Yanzu an nuna cewa Ɗa na alkawarin zai fito ne daga gidan Dauda. Amma mulkin ɗan Adam zai iya kasance “har abada”? (Zabura 89:20, 29, 34-36) Kuma irin wannan sarki ɗan Adam zai iya ya ceci mutane daga zunubi da mutuwa?
13, 14. (a) In ji Zabura ta 110, wane alkawari Jehobah ya yi wa Sarkinsa da ya naɗa? (b) Wane ƙarin bayani game da Ɗan mai zuwa aka yi ta wajen annabawan Jehobah?
13 An hure Dauda ya rubuta: “Yahweh ya ce wa ubangijina, ‘Zauna nan a damana sai na sa abokan gābanka a ƙarƙashin ƙafafunka.’ Yahweh ya yi rantsuwa bai zai canja ra’ayinsa ba cewa, ‘Kai firist ne na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.’ ” (Zabura 110:1, 4) Kalmomin Dauda ya shafi Ɗa na alkawarin kai tsaye, ko kuma Almasihu. (Ayyukan Manzanni 2:35, 36) Wannan Sarkin zai yi sarauta, ba a Urushalima ba amma daga sama a “hannun damana” Jehobah. Wannan zai ba shi iko ba bisa ƙasar Isra’ila ba kawai, amma bisa dukan duniya. (Zabura 2:6-8) A nan an bayyana ƙarin abu. Ka lura cewa Jehobah ya rantse cewa Almasihun zai zama “[firist] . . . bisa ga tsarin Melkizedek.” Kamar Melchizedek, wanda ya yi hidima na sarki da firist a zamanin Ibrahim, Ɗan mai zuwa, Allah ne zai naɗa shi ya yi hidima ta Sarki da Firist!—Farawa 14:17-20.
14 A cikin shekaru da yawa, Jehobah ya yi amfani da annabawansa su ba da ƙarin bayani game da asirinsa. Alal misali, Ishaya ya bayyana cewa Ɗan zai mutu mutuwar hadaya. (Ishaya 53:3-12) Mika ya faɗi wurin da za a haifi Almasihun. (Mika 5:2) Daniel ya annabta daidai lokacin da Ɗan zai bayyana da kuma mutuwarsa.—Daniyel 9:24-27.
An Bayyana Asirin!
15, 16. (a) Ta yaya Ɗan Jehobah ya zo ya kasance ta wurin “mace”? (b) Mene ne Yesu ya gāda daga wajen iyayensa mutane, kuma yaushe Ɗan alkawarin ya zo?
15 Yadda waɗannan annabce-annabce za su cika ya kasance asiri har sai da Ɗan ya bayyana. Galatiyawa 4:4 ta ce: “Amma sa’anda cikar kwanaki ta zo, Allah ya aiko Ɗansa, haifaffe daga mace.” A shekara ta 2 K.Z., mala’ika ya gaya wa budurwa Bayahudiya mai suna Maryamu: “Ga shi za ki yi ciki, za ki kuma haifi ɗa, za ki ba shi suna Yesu. Zai zama babban mutum, kuma za a ce da shi Ɗan Mafi Ɗaukaka. Ubangiji Allah zai ba shi kujerar mulkin kakansa Dawuda. . . . Ruhu mai tsarki zai sauko a kanki, ikon Mafi Ɗaukaka kuma zai rufe ki. Saboda haka yaron nan da za a haifa, za a ce da shi mai tsarki, Ɗan Allah.”—Luka 1:31, 32, 35.
16 Daga baya, Jehobah ya ƙaurar da ran Ɗansa daga sama zuwa cikin Maryamu, sai ya zamanto mace ta haife shi. Maryamu mace ce ajiza. Duk da haka, Yesu bai gaji ajizanci ba daga wajenta, domin “Ɗan Allah” ne shi. Amma duk da haka, iyayen Yesu na jiki, da yake suna daga zuriyar Dauda ne sun ba shi ikon magājin Dauda. (Ayyukan Manzanni 13:22, 23) A lokacin baftismar Yesu a shekara ta 29 A.Z., Jehobah ya naɗa shi da ruhu mai tsarki kuma ya ce: “Wannan shi ne Ɗana da nake ƙauna.” (Matiyu 3:16, 17) A ƙarshe, Ɗan ya zo! (Galatiyawa 3:16) Lokaci ya yi domin bayyana abubuwa da yawa game da asirin.—2 Timoti 1:10.
17. Ta yaya aka ba da bayani game da ma’anar Farawa 3:15?
17 A lokacin hidimarsa, Yesu ya bayyana macijin Farawa 3:15 cewa Shaiɗan ne kuma zuriyar macijin, mabiyan Shaiɗan ne. (Matiyu 23:33; Yohanna 8:44) Daga baya, an bayyana yadda dukan waɗannan za a ƙuje su har abada. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 20:1-3, 10, 15) Kuma an bayyana macen cewa “Urushalima ta sama” ce, wato sashen ƙungiyar Jehobah ta halittun ruhu wadda take sama kamar matarsa.a—Galatiyawa 4:26; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:1-6.
Sabon Alkawari
18. Mece ce dalilin “sabuwar yarjejeniya”?
18 Wataƙila bayyana mafi ban mamaki duka ta zo ne a daren mutuwar Yesu sa’ad da ya gaya wa mabiyansa masu aminci game da “sabuwar yarjejeniya.” (Luka 22:20) Kamar wanda ya shige, alkawarin Dokar Musa, wannan sabon alkawari domin ya ba da “mulki na firistoci” ne. (Fitowa 19:6; 1 Bitrus 2:9) Amma, wannan alkawarin zai tabbatar da al’umma ce ta ruhaniya ba ta jiki ba, “Isra’ila ta Allah,” da ta ƙunshi kawai mabiya Kristi masu aminci. (Galatiyawa 6:16) Waɗanda suke cikin wannan sabon alkawari za su yi aiki tare da Yesu wajen kawo albarka ga zuriyar ’yan Adam!
19. (a) Me ya sa sabon alkawari ya yi nasara wajen ba da “mulki na firistoci”? (b) Me ya sa aka kira shafaffu Kiristoci “sabuwar halitta,” kuma nawa ne za su yi hidima a sama da Kristi?
19 Amma me ya sa sabon alkawarin ya yi nasara wajen ba da “mulki na firistoci” su albarkaci ’yan Adam? Domin maimakon hukunta almajiran Kristi cewa masu zunubi ne, ya yi tanadin gafara ga zunubansu ta wajen hadayarsa. (Irmiya 31:31-34) Da zarar sun kasance da tsabta a gaban Jehobah, zai ɗauke su zuwa iyalinsa na sama kuma ya shafe su da ruhu mai tsarki. (Romawa 8:15-17; 2 Korintiyawa 1:21) Saboda da haka suna shaida ‘sake haihuwa . . . zuwa ga bege mai-rai . . . da aka ajiye a sama.’ (1 Bitrus 1:3, 4) Domin wannan matsayi mai girma sabo ne ga mutane, shafaffu Kiristoci da aka naɗa ana kirar su “sabuwar halitta.” (2 Korintiyawa 5:17) Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa a ƙarshe mutane 144,000 ne za su saka hannu wajen sarauta a sama bisa ’yan Adam da aka cece su.—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 5:9, 10; 14:1-4.
20. (a) Wane bayani ne aka yi game da asirin a shekara ta 36 A.Z.? (b) Su waye za su more alkawarin albarka da aka yi wa Ibrahim?
20 Tare da Yesu, waɗannan shafaffu suka zama “zuriyar Ibrahim.”b (Galatiyawa 3:29) Waɗanda aka zaɓa da farko Yahudawa ne na jiki. Amma a shekara ta 36 A.Z., wani ɓangaren asirin ya bayyana: Mutanen Al’ummai, ko kuma waɗanda ba Yahudawa ba, su ma za su samu begen zuwa sama. (Romawa 9:6-8; 11:25, 26; Afisawa 3:5, 6) Shafaffu Kiristoci ne kawai za su more albarkar da aka yi wa Ibrahim alkawarinsa? A’a, domin hadayar Yesu za ta amfani dukan duniya. (1 Yohanna 2:2) Da shigewar lokaci, Jehobah ya bayyana cewa “babban taro” marar iyaka zai tsira a ƙarshen zamanin Shaiɗan. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:9, 14) Da yawa kuma za a ta da su daga matattu da begen rayuwa har abada a Aljanna!—Luka 23:43; Yohanna 5:28, 29; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 20:11-15; 21:3, 4.
Hikimar Allah da Kuma Asirin
21, 22. A waɗanne hanyoyi ne asirin Jehobah ya bayyana hikimarsa?
21 Asirin nuna “hikimar Allah iri-iri” ce mai ban mamaki. (Afisawa 3:8-10) Lallai Jehobah ya nuna hikima wajen fito da wannan asirin, sai kuma a bayyana shi kaɗan kaɗan! Ya yi la’akari da iyakar ’yan Adam, yana ƙyale su su nuna ainihin zuciyarsu.—Zabura 103:14.
22 Jehobah har ila ya nuna hikima marar kama wajen zaɓan Yesu ya zama Sarki. Ɗan Jehobah ya fi dukan wata halitta tabbaci. Da yake raye da jini da tsoka, Yesu ya fuskanci masifu iri iri da yawa. Ya fahimci matsalolin mutane ƙwarai. (Ibraniyawa 5:7-9) Waɗanda suke sarauta tare da Yesu fa? A cikin ƙarnuka, maza da mata—da aka zaɓa daga dukan launin fata, harsuna, da kuma wurare dabam dabam—an naɗa su. Babu wata matsala da wani cikinsu bai fuskanta ba kuma ya yi nasara. (Afisawa 4:22-24) Rayuwa ƙarƙashin waɗannan sarakuna firistoci masu jinƙai zai zama da daɗi!
23. Wace gata Kiristoci suke da ita game da asirin Jehobah?
23 Manzo Bulus ya rubuta: “Wannan labarin da nake sanar muku, asiri ne wanda yake a ɓoye tun zamani da tsara masu yawa, amma yanzu an bayyana shi ga tsarkakansa.” (Kolosiyawa 1:26) Hakika, shafaffu masu tsarki na Jehobah sun zo ga fahimtar asirin sosai, kuma sun koya wa miliyoyi wannan ilimin. Lallai gata ce da dukanmu muke da ita! Jehobah ‘ya sa mun san asirin nufinsa.’ (Afisawa 1:9) Bari mu gaya wa wasu wannan asiri mai ban mamaki, mu taimake su su fahimci hikimar Jehobah Allah mai wuyar fahimta!
a “Asirin bangaskiya” ya bayyana a kan Yesu. (1 Timoti 3:16) Ya daɗe yana asiri, cewa ko wani zai iya kasance da cikakken aminci ga Jehobah. Yesu ya bayyana amsar. Ya kasance da amincinsa a cikin dukan wani gwaji da Shaiɗan ya kawo masa.—Matiyu 4:1-11; 27:26-50.
b Yesu ma ya yi alkawarin mulki da wannan rukunin. (Luka 22:29, 30) Wato, Yesu ya yi alkawari da “ƙaramin garke” cewa za su yi sarauta tare da shi a sama, suna matsayi na biyun na zuriyar Ibrahim.—Luka 12:32.