Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lr babi na 8 pp. 47-51
  • Wasu Sun Fi Mu Matsayi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wasu Sun Fi Mu Matsayi
  • Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Makamantan Littattafai
  • Yaya Rayuwa Take a Lambun Adnin?
    Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada
  • Adamu da Hauwa’u Sun Ki Bin Dokar Allah
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Abin Da Ya Sa Suka Yi Rashin Gidansu
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Ana Iya Ɓata wa Allah Rai​—⁠Ta Yaya Za Mu Iya Sa Shi Farin Ciki?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
lr babi na 8 pp. 47-51

BABI NA 8

Wasu Sun Fi Mu Matsayi

NA TABBATA za ka yarda cewa wasu sun fi mu matsayi, girma ko kuma ƙarfi. Wa za ka ce ya fi mu?— Jehovah Allah ya fi mu. Ɗansa Babban Malami kuma fa? Shi ma ya fi mu ne?— Hakika shi ma ya fi mu.

Yesu ya rayu tare da Allah a sama. Shi Ɗa ne na ruhu, ko kuma mala’ika. Allah ya yi wasu mala’iku ne, ko kuma ’ya’ya na ruhu?— E, ya yi su da yawa sun kai miliyoyi. Waɗannan mala’iku ma sun fi mu matsayi kuma sun fi mu ƙarfi sosai.—Zabura 104:4; Daniel 7:10.

Ka tuna sunan mala’ika da ya yi magana da Maryamu?— Sunansa Jibra’ilu. Ya gaya wa Maryamu cewa za a kira ɗanta Ɗan Allah. Allah ya saka ran Ɗansa na ruhu a cikin Maryamu domin haka aka haifi Yesu jariri a duniya.—Luka 1:26, 27.

Maryamu and Yusufu suna wa Yesu magana sa’ad da yake karami

Me wataƙila Maryamu da Yusufu suka gaya wa Yesu?

Ka yarda da wannan mu’ujiza? Ka yarda cewa Yesu ya rayu da Allah a sama?— Yesu ya ce ya rayu a sama. Ta yaya Yesu ya sani game da waɗannan abubuwa? E, sa’ad da yake yaro, wataƙila Maryamu ta gaya masa abin da Jibra’ilu ya faɗa. Kuma, wataƙila Yusufu ya gaya wa Yesu cewa Allah ne Ubansa na ainihi.

Sa’ad da aka yi wa Yesu baftisma, Allah ya yi magana daga sama, ya ce: “Wannan Ɗana ne.” (Matta 3:17) Kuma a daren da zai mutu, Yesu ya yi addu’a: “Uba, ka ɗaukaka ni da kanka da daraja wadda ni ke da ita tare da kai tun duniya ba ta zama ba.” (Yohanna 17:5) Hakika, Yesu ya roƙa a mai da shi zuwa sama ya sake zama tare da Allah a sama. Ta yaya zai zauna a can?— Sai dai Jehovah Allah ya sake mai da shi ruhu da ba a gani, ko kuma mala’ika.

Yanzu ina so in yi maka wata tambaya mai muhimmanci. Dukan mala’iku masu nagarta ne? Me ka ce?— E, akwai lokacin da dukansu suna da nagarta. Wannan saboda Jehovah ne ya halicce su, kuma dukan abin da ya yi nagari ne. Amma wani cikin mala’ikun ya zama mugu. Ta yaya wannan ya faru?

Domin amsar, dole ne mu koma lokacin da Allah ya halicci mata da miji na farko, Adamu da Hauwa’u. Wasu sun ce tarihinsu ƙage ne kawai. Amma Babban Malami ya sani cewa tarihinsu gaskiya ne.

Sa’ad da Allah ya halicci Adamu da Hauwa’u, ya saka su a cikin lambu mai kyau da ake kira Adnin. Aljanna ce. Da za su samu yara da yawa, iyali mai girma, kuma su zauna a Aljanna har abada. Amma da akwai darasi mai muhimmanci da suke bukatar su koya. Abin da mun riga mun yi magana a kai ne. Bari mu gani ko za mu tuna shi.

Adamu da Hauwa’u a lambun Adnin

Da ta yaya Adamu da Hauwa’u za su zauna a cikin Aljanna har abada?

Jehovah Allah ya gaya wa Adamu da Hauwa’u cewa za su iya cin ’ya’yan itatuwan da suke cikin lambun. Amma akwai itace ɗaya da ya ce kada su ci. Allah ya gaya musu abin da zai faru idan suka ci. Ya ce: “Mutuwa za ka yi lallai.” (Farawa 2:17) To, wane darasi ne Adamu da Hauwa’u suke bukatar su koya?—

Darasin yin biyayya ne. Hakika, rai ya dangana ne a kan biyayya ga Jehovah Allah! Ba kawai Adamu da Hauwa’u su ce za su yi masa biyayya ba. Dole ne su nuna cewa za su yi biyayya ta wajen abubuwa da suke yi. Idan suka yi wa Allah biyayya, za su nuna suna ƙaunarsa kuma suna so ya zama Mai Sarautarsu. Da sai su zauna har abada a cikin Aljanna. Amma idan suka ci daga itacen, menene wannan zai nuna?—

Zai nuna cewa lallai ba su yi godiya ba ga abin da Allah ya ba su. Da za ka yi biyayya ga Jehovah da a ce kana wajen?— Da farko, Adamu da Hauwa’u sun yi biyayya. Amma wani da ya fi su ya ruɗi Hauwa’u. Ya sa ta yi wa Jehovah rashin biyayya. Wanene wannan?—

Hauwa’u tana rike da ’ya’yan itacen da aka hana su tabawa kuma macijin yana magana da ita

Waye ya sa macijin yake magana da Hauwa’u?

Littafi Mai Tsarki ya ce maciji ya yi wa Hauwa’u magana. Amma ka sani cewa maciji ba zai iya yin magana da kansa ba. To, ta yaya ya yi magana?— Wani mala’ika ya sa ya bayyana kamar macijin ne yake magana. Amma ainihi mala’ikan ne yake magana. Mala’ikan ya fara tunanin abubuwa marasa kyau. Yana so Adamu da Hauwa’u su bauta masa. Yana so su yi abin da ya faɗa. Yana so ya ɗauki matsayin Allah.

Sai wannan mugun mala’ika ya saka ra’ayin da babu kyau a zuciyar Hauwa’u. Ta wajen macijin, ya gaya mata: ‘Allah bai gaya muku gaskiya ba. Ba za ku mutu ba idan kuka ci daga itacen. Za ku zama kamar Allah.’ Da za ka yarda da abin da muryar ta faɗa?—

Hauwa’u ta fara son abin da Allah bai ba ta ba. Ta ci ’ya’yan itacen da aka hana ta. Sai ta ba wa Adamu. Adamu bai yarda da abin da macijin ya ce ba. Amma muradinsa ya zauna tare da Hauwa’u ya yi ƙarfi fiye da ƙaunarsa ga Allah. Sai ya ci ’ya’yan itacen shi ma.—Farawa 3:1-6; 1 Timothawus 2:14.

Menene sakamakon haka?— Adamu da Hauwa’u suka zama ajizai, suka tsufa, kuma suka mutu. Kuma domin ajizai ne su, dukan ’ya’yansu ma ajizai ne kuma a hankali za su tsufa su mutu. Allah bai yi ƙarya ba! Rai ya dangana ne a kan biyayya gare shi. (Romawa 5:12) Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa mala’ikan da ya yi wa Hauwa’u ƙarya sunansa Shaiɗan Iblis, kuma wasu mala’iku da suka zama miyagu ana kiransu aljanu.—Yaƙub 2:19; Ru’ya ta Yohanna 12:9.

Adamu da hauwa’u sa’ad da suka tsufa

Menene ya faru da Adamu da Hauwa’u bayan sun yi wa Allah rashin biyayya?

Yanzu ka fahimci dalilin da ya sa mala’ika nagari da Allah ya halitta ya zama mugu?— Domin ya fara tunanin abin da ba shi da kyau. Yana so ya zama na Fari. Ya sani cewa Allah ya gaya wa Adamu da Hauwa’u su haifi ’ya’ya, yana so dukansu su bauta masa. Iblis yana so ya saka kowa ya yi rashin biyayya ga Jehovah. Saboda haka yana so ya saka miyagun abubuwa a cikin zukatanmu.—Yaƙub 1:13-15.

Iblis ya ce babu wanda da gaske yake ƙaunar Jehovah. Ya ce wai ni da kai ba ma ƙaunar Allah da gaske, cewa ba ma so mu yi abin da Allah ya ce. Ya ce muna yi wa Jehovah biyayya ne kawai idan kome ya faru yadda muke so. Gaskiyar Iblis ne? Haka muke?

Babban Malami ya ce Iblis maƙaryaci ne! Yesu ya nuna cewa yana ƙaunar Jehovah da gaske ta wajen yi masa biyayya. Kuma Yesu bai yi wa Allah biyayya ba kawai a lokacin da yake da sauƙi. Ya yi haka a dukan lokaci, har a lokacin da mutane suka sa ya yi wuya a gare shi. Ya kasance da aminci ga Jehovah har zuwa ƙarshen ransa. Abin da ya sa ke nan Allah ya sake ba shi rai ya zauna har abada.

To, wa za ka ce shi ne babban abokin gabanka?— Shaiɗan Iblis ne. Za ka iya ganinsa?— A’a! Amma mun sani yana wanzuwa kuma ya fi mu matsayi kuma yana da ƙarfi fiye da mu. Amma kuma waye ya fi Iblis matsayi?— Jehovah Allah ya fi shi matsayi. Saboda haka mun sani cewa Allah zai kāre mu.

Ka karanta game da Wanda ya kamata mu bauta masa: Kubawar Shari’a 30:19, 20; Joshua 24:14, 15; Misalai 27:11; da kuma Matta 4:10.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba