WAƘA TA 82
‘Mu Bari Haskenmu Ya Haskaka’
Hoto
1. Yesu ya ce mana
Mu haskaka fa,
Kamar ranar da ke
Haska ko’ina.
Kalmar Allah tana
Da iko sosai.
Mu sa a ga hasken nan
Ta wa’azinmu.
2. Mu riƙa wa’azi
Ga duk mutane.
Don mu ’yantar da su
Daga duhun nan.
Maganar Jehobah
Muke yaɗawa.
Za ta taimaka musu
Su bauta masa.
3. Muna haskakawa
Ta halayenmu,
Furucinmu kuma
Na da daraja.
Bari mu haskaka
Ta ayyukanmu,
Hakan zai faranta ran
Allah Jehobah.
(Ka kuma duba Zab. 119:130; Mat. 5:14, 15, 45; Kol. 4:6.)