WAƘA TA 140
Za Mu Yi Rayuwa Har Abada!
Hoto
1. Za mu more aljanna
Da Jehobah zai kawo.
Ba ɓacin rai, ba cuta,
Sai dai kwanciyar rai.
(AMSHI)
Mu yi waƙar yabo
Domin albarkun nan!
Mu yi ɗokin kasance
“A cikin Aljanna!”
2. Dukanmu a Aljanna
Za mu zama matasa.
Za mu daina jin tsoro,
Har da yin kuka ma.
(AMSHI)
Mu yi waƙar yabo
Domin albarkun nan!
Mu yi ɗokin kasance
“A cikin Aljanna!”
3. Za mu riƙa ɗaukaka
Allahnmu a Aljanna.
Har abada, za mu yi
Wa Allah godiya.
(AMSHI)
Mu yi waƙar yabo
Domin albarkun nan!
Mu yi ɗokin kasance
“A cikin Aljanna!”
(Ka kuma duba Ayu. 33:25; Zab. 72:7; R. Yoh. 21:4.)