DARASI NA 57
Me Za Ka Yi Idan Ka Yi Zunubi Mai Tsanani?
Ko da kana ƙaunar Jehobah sosai, kuma kana iya ƙoƙarinka don kar ka yi abin da zai ɓata masa rai, a wasu lokuta, za ka iya yin kuskure. Amma wasu kurakure suna da tsanani fiye da wasu. (1 Korintiyawa 6:9, 10) Idan ka yi zunubi mai tsanani, ka tuna cewa Jehobah yana ƙaunar ka har ila, yana shirye ya gafarta maka kuma ya taimaka maka.
1. Mene ne za mu yi don Jehobah ya gafarta mana?
Waɗanda suke ƙaunar Jehobah suna baƙin ciki sosai sa’ad da suka gane cewa sun yi zunubi mai tsanani. Amma Jehobah yana ƙarfafa su da alkawarin da ya yi wa bayinsa cewa: “Ko da kun yi ja wur da zunubi, za ku yi fari fat kamar auduga.” (Ishaya 1:18) Idan mun tuba da gaske, Jehobah zai gafarta mana. Yaya za mu nuna cewa mun tuba? Za mu yi nadama, mu daina yin abin da bai da kyau kuma mu roƙi Jehobah ya gafarta mana. Sai mu yi iya ƙoƙarinmu mu daina tunanin banza ko halayen da suka sa mu yi zunubi. Kuma mu yi ƙoƙari mu yi rayuwar da ta jitu da ƙa’idodin Jehobah.—Karanta Ishaya 55:6, 7.
2. Ta yaya Jehobah yake amfani da dattawa ya taimaka mana idan muka yi zunubi?
Idan mun yi zunubi mai tsanani, Jehobah ya gaya mana cewa mu faɗa wa “dattawan ikilisiya.” (Karanta Yakub 5:14, 15.) Dattawan nan suna ƙaunar Jehobah da kuma bayinsa. An koya musu yadda za su taimaka mana mu gyara dangantakarmu da Jehobah.—Galatiyawa 6:1.
Ta yaya dattawa suke taimaka mana idan muka yi zunubi mai tsanani? Dattawa biyu ko uku za su yi amfani da Littafi Mai Tsarki don su nuna mana cewa abin da muka yi ba daidai ba ne. Ban da haka, za su ba mu shawarwari kuma su ƙarfafa mu don su taimaka mana kar mu sake yin zunubin. Idan mutum ya yi zunubi mai tsanani kuma ya ƙi ya tuba, dattawa za su cire shi daga ikilisiya don kar ya ɓata sauran ’yan’uwa.
KA YI BINCIKE SOSAI
Za mu koyi yadda za mu nuna godiya ga Jehobah don yadda yake taimaka mana idan muka yi zunubi mai tsanani.
3. Furta zunubanmu zai sa mu gyara dangantakarmu da Allah
Duk zunubin da muka yi yakan ɓata wa Jehobah rai. Saboda haka, ya dace mu gaya masa abin da muka yi. Ku karanta Zabura 32:1-5, sai ku tattauna tambayar nan:
Me ya sa zai dace mu gaya wa Jehobah zunubin da muka yi maimakon mu ɓoye shi?
Bayan mun gaya wa Jehobah zunubanmu, za mu sami kwanciyar hankali idan muka nemi taimakon dattawa. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.
A bidiyon, ta yaya dattawa suka taimaka wa Canon ya komo ga Jehobah?
Wajibi ne mu gaya wa dattawa gaskiya don za su taimaka mana. Ku karanta Yakub 5:16, sai ku tattauna tambayar nan:
Me ya sa zai yi wa dattawa sauƙi su taimaka mana idan muka gaya musu gaskiya?
Ka faɗi zunubin da ka yi, ka gaya wa dattawa gaskiya, kuma ka amince da taimakon Jehobah
4. Jehobah yana yi wa masu zunubi jinƙai
Idan mutum ya yi zunubi mai tsanani kuma ya ƙi bin ƙa’idodin Jehobah, za a cire shi daga ikilisiya, kuma ba za mu yi tarayya da shi ba. Ku karanta 1 Korintiyawa 5:6, 11, sai ku tattauna tambayar nan:
Kamar yadda yisti yake sa fulawa ta kumbura, ta yaya yin tarayya da wanda ya yi zunubi kuma ya ƙi tuba zai shafi ikilisiya?
Kamar yadda Jehobah yake yi ma waɗanda suka yi zunubi jinƙai, haka ma dattawa sukan ɗauki matakai don su taimaka ma waɗanda aka cire daga ikilisiya. Mutane da yawa da aka cire daga ikilisiya sun sake dawowa. Me ya sa? Domin horon da aka yi musu ya taimaka musu su gane cewa abin da suka yi ba daidai ba ne.—Zabura 141:5.
Ta yaya yadda Jehobah yake bi da waɗanda suka yi zunubi yake nuna cewa shi mai ƙauna ne, mai jinƙai, kuma ya san abin da ya dace da mu?
5. Jehobah yana gafarta mana idan mun tuba
Yesu ya yi amfani da wani misali don mu fahimci yadda Jehobah yake ji idan wani ya tuba. Ku karanta Luka 15:1-7, sai ku tattauna tambayar nan:
Mene ne misalin nan ya koya maka game da Jehobah?
Ku karanta Ezekiyel 33:11, sai ku tattauna tambayar nan:
Wane abu mai muhimmanci ne za mu yi don mu nuna cewa mun tuba da gaske?
Kamar makiyayi, Jehobah ya damu da bayinsa
WASU SUN CE: “Ina tsoron gaya wa dattawa zunubin da na yi, don za su cire ni daga ikilisiya.”
Me za ka gaya wa mutumin da yake da irin wannan ra’ayin?
TAƘAITAWA
Idan muka yi zunubi mai tsanani, muka tuba kuma muka yanke shawara cewa za mu daina yin abu marar kyau, Jehobah zai gafarta mana.
Bita
Me ya sa yake da kyau mu gaya wa Jehobah zunubanmu?
Mene ne muke bukatar mu yi don Jehobah ya gafarta mana zunubanmu?
Idan mun yi zunubi mai tsanani, me ya sa muke bukatar mu nemi taimakon dattawa?
KA BINCIKA
Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda Jehobah ya nuna ma wani mutum irin jinƙai da aka kwatanta a Ishaya 1:18.
Ta yaya dattawa suke taimaka ma waɗanda suka yi zunubi mai tsanani?
“Yadda Za A Nuna wa Mai Zunubi Kauna da Jinkai” (Hasumiyar Tsaro, Agusta 2024)
Ku karanta talifin nan don ku ga yadda ake nuna ƙauna da jinƙai ga masu zunubi da suka ƙi tuba.
“Yadda Za A Taimaka wa Waɗanda Aka Cire Daga Ikilisiya” (Hasumiyar Tsaro, Agusta 2024)
Ku karanta labarin nan “Ina Bukatar Komawa ga Bauta wa Jehobah,” don ku ga dalilin da ya sa wani mutumin da ya daina bauta wa Jehobah, yake ganin cewa Jehobah ne ya dawo da shi.
“Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Afrilu, 2012)